Sashe 51
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a iya wannan irin azababben ciwon kan nan a Paris har saboda da kaza ya kai ta aka mata hoton kai. Sai dai bai fa a mata result in hoton ba idan banda ce mata da yayi stress ne da damuwa ya jawo mata ciwo, sai kuma pills in da ya bata ta sha, kuma tun da ta sha bata kuma jin irin ciwon ba har suka je Dubai suka gama kwanakin su suka dawo Nigeria. Irin wannan azabtacciyar ciwon kan da taji ko ma iyinta ba ta masa fatan ya ana. "Mummyna, don Allah kar ki tafi ko ina ki barni. I can't live without you, mommah!" Meema ta fa i tana ara ame uwar. Bayanta kawai ta ke bubbugawa ba tare da ta ce mata komai ba. Mafarkin da ta yi ne ya tuno mata karshe da mahaifiyarsu ta yi mata; _Zinatu, ni mahaifiya ce a gare ki kuma mai aunarki, wacce take son cigabanki. Duk duniya babu wata mace ko a namiji har da mahaifinku ban cire ba da zai gwada min ya fini son ku. Ina aunar ki Zinatu. Sosai ba ka an ba, amma halinki ne ya ke sani jin haushinki da zuba miki idanu idan kina wasu abubuwan. Zinatu kowa rai ya yiwa da i barin mai shi ne. Yanzu fisabilillahi, Maryama da Sa'adatu basu burge ki? Sun natsu waje aya babu ruwan su da shashancin ko kuma yin abunda Abie inku zai hantare su. Kullum orafinki shine ba a aunarki cikin gidan nan. Kina ganin mutum zai haifi a ya ce bai so? Ko bambamci da kika ga babanku yana nuna tsakanin sauran an uwanki da ke, saboda halinki ne. Zan iya irga sau nawa babanku ya saka hannunsa a jikin Maryama da Sa'adatu. Amma ke ban ga ranar da za ta hudo har ta fa i ba a jibgeki a cikin gidan nan ba. Zinatu kina da shegen kwa ayi da hangen na sama da ke wanda hakan ba aramin illa bane a rayuwarki. Shi kansa mahaifin na ki da kika ganin kamar shi ya yankarwa kansa talauci, rayuwa ce ta mayar dashi haka. Amma da gatansa. Kawai yau da gobe ce, ku kun san haka don baku rasa ci, sha ko sutura ba. Yana iyakacin bakin arin sa a kan ku. Amma ke aya kawai kina son caza mana walwa. Shin kin san irin ashin arzikin da Allah ya yiwa shi mijin da ya za ar miki? Don girman Allah Zeenah ki daure ki yiwa mahaifinki biyayya ki auren nan kamar yanda sauran an uwanki suka amince. Kin ganni nan, na auri mahaifinku ne saboda biyayyar iyaye because I belongs to the family where good daughters never say no to their parents. My father wanted me to get married, and all a said is, if that will make you happy I'll say yes. And you all know it was never a happy marriage. Mahaifinku mutun ne mafa aci kuma mai zuciya tsiya. Yana da mugun taurin kai kuma ba aramin abu ke saka zuciyarsa ta yi laushi ba. Don girman Allah ina ro onki da ki kiyaye fushi da zuciyar mahaifinku, Zinatu. Zeenatu duk lokacin da na juya na kalle ku ku mata uku reras a gabana, sai na ji zuciyata ta tsinke. Bani da burin da ya wuce na ga na aurar da ku na mi a ku gidan mazajan ku cikin mutunci. Ki taimaka min Zinatu, wallahi ke ka ai ce ciwon kaina. Ban jin Maryama da Sa'adatu domin su in masu tausaya min tare da jin maganata ne ni da mahaifinku._ Hannu Laushi ta kai ta share hawayen da suka ziraro a idanunta bayan ta gama tuno kalaman mahaifiyar tata a kunnanta kamar yanzu take mata magana. "It been 10years now without you Mamana! Ba mutuwa kika yi ba amma ban da ikon zuwa inda kike saboda abunda na aikata! Wallahi tallahi ba intentionally na yi ba. Self-defense ne. Allah ka san komai kuma kana ganin komai." Laushi ta fa i cikin zuciya tana hawaye. "Ashe hake kike ji Mama? Ashe haka duk wata uwa take ji a kan anta? Ban san mai yasa ba kwanakin nan duk na kalle ki ata sai inji gabana yana mugun fa uwa. Na haifeki ba tare da aure ba, na ata miki record. Ban ta a tunanin wannan tabon da na miki zai dame ni ba. Ban ta a tunanin akwai ranar da za ta zo in soma nadamar abubuwan da na aikata ba. Ban ta a zaman mintuna biyar na yi fashin ba i a kan kalamanki ba ummi na. Ashe gaskiya kike fa a mini." Wannan karan hawayenta har sauka suke a wuyan Meema da ke rungume da ita. A hankali Meema ta ago tare da kai hannu tana share hawanyen Laushin tare da fa "Stop crying mom, everything will be alright. You will get better soon, In Sha Allah!" a kai Laushin ta yi tare da fa in, "In Sha Allah, daughter." Daidai nan Salmanu an daudu ya shigo hannunsa ri e da plate in sakwara miyan egusi da ya ji stockfish da nama don Salma nice ba daga nan ba wajen girma ko wata macen albarka. "Uwar Meema kin tashi? Ya jikin na ki? To ga abinci nan da zafinsa ki samu ki ci." "Nagode, Salma. Kawo Meema ta ci don na san she must be hungry." "Uwar Meema, ai ha uri da wannan sunan don Allah. Kira ni da Salmanu ya fi da in ji wallahi," Salmanu an daudu ya fa Laushi bata kula shi ba don she's not in the mood da za ta biye shi a yanzu kam. "Je ki wanke hannunki ki zo muci abinci," Laushi ta fa i tana mai mi ar da ita tsaye. Sauka daga kan gadon ta yi tare da shiga bayi ta wanko hannu sannan ta dawo lokacin Salmanu ya bar akin. A asa ta samu Laushi ri e da goshi saboda nauyi da kanta da kuma idanunta suka mata. "Mummy, kan ne?" Meema ta fa i muryanta na cracking. Girgiza mata kai ta yi tare da fa in, "No, am ok. Kawai idanuna ne suka min nauyi." "Can I feed you, mum?" Meema ta fa i bayan ta zauna kusa da ita. a kai Laushi ta yi hawaye na arin zubowa amma sai ta yi saurin shanye su. Hannu Meema ta saka cikin kwanon ta gutsiro sakwaran sannan ta dangwala miya ta kai bakin Laushi. Bu e baki ta yi ita kuma ta saka mata. Laushi can't hold it bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba wanda lokaci guda jijiyoyin kanta ya harba. Hannu ta saka ta ri e kan da arfi tana kuka. Da gudu Meeman ta fita daga akin ta kira Ladi Katifa suka dawo akin tare. "Zeenah, kan ne? Bari na auko miki magungunar ki." Ta arisa maganar tare da fita da sauri. Meema kuma zama ta yi gafenta tare da sauke hannunta aya ta ri e gam a hannunta. Jim ka an Ladi ta shigo da magungunan da kuma bottle water. Sai d ta are tukun ta mi awa Laushi ita kuma ta kar a ta watsa a baki tare da binsa da ruwan goran. Zuwa can ta jinginar da kanta jikin gado. Abincin da bata iya cinsa kenan ba, haka Meema don ita ma kasa cin sakwarar ta yi sanida Laushi bata ci ba. Da kyar dai ta sha custard in da Ladi ta ha a mata shima cokali biyar kawai ta yi. Sati aya kawai Laushi ta yi wani irin zabgewa. asusuwa sun mata sar a a wuya. Ta yi bye-bye da farin ciki da natsuwa. Cuta da tashin hankali ya yi mata knocking kuma ba tare da shiri ba ta bu ofa. akun rana ne Laushi ba ta azababben ciwon kan nan, bata ta a samun natsuwa har sai ta sha pills in da Sabo da Kaza ya bada a ri a bata. Meema ma duk ta zabge saboda rashin lafiyar mummynta. Sabo da Kaza kuwa ko a waya bai waiwaye su ba har sai da kwana bakwai ta cika sannan ya turo Yahuza ya auki Meema a mota wata ranar Litinin da sassafe. Wani makaranta suka nufa a an cikin garin Lagos mai matu ar kyau da tsaruwa kamar ba a asar Nigeria ba. A nan aka sake enrolling inta a primary 5. Kuma kullum Yahuza ke zuwa ya kai ta sannan ya dawo da ita. Da farin ciki Meema ke fa awa Laushi irin makarantar da aka kai ta, ita dai Laushi murmushi kawai take yi ganin Meema cikin walwalar da tun da ta fara ciwo bata yi shi ba. Haka Meema ta kwashi sati biyu tana zuwa makaranta, sai dai ita bayan an tashi, Yahuza yana kai ta wata makaranta da ake koya mata yaren da bata ta a jin irinsa ba a rayuwarta. Tun bata aunar yaren kuma yana mata wahala har ta saba da shi don wata rana idan ta tashi da safe za ta gaida su Laushin da yaren ta ke gaida su. Makamai kuwa ba a daina jibge su ba. Sai dai bayan kwana biyu ko uku, amintaccen Sabo da Kaza, wato Yahuza yana kawo wasu su kwashe bayan sun gama ciniki sun bada ku *_Abuja_* Daga Kaita har Habib babu wanda ke samun cikakken lokacin kansa don Babiyo ya matsa masu namba. Musamman ma Habib da ko ofar gate in Ar o Barkin o bai isa ya je ba. Bikinsu saura kwana hu u rak. Idan kuka ga Habibu sai ya ba ku tausai don ko ta ina zafi ne a wajansa. Ta angaren iyayansa, Baffa Gi o ko ka an bai raga masa kamar yanda Babiyo ya tsauwala masa. Ta wajen mama Halima da ta an sauko ne kawai ya ke an samun sau i. Mamiyo kuwa har ba en magana take fa a masa idan ya je gaishe ta. Kai tsaye take zagin mahaifinsa tana aibata shi da mugayan suna. Jawaad kuwa, Mahaifiyarsa ce da kanta ta za a masa Khairat a matsayin matar da zai aura, kuma sosai Babiyo ya ji da in za en don Khairat tana aya daga cikin jikokinsa da yake ji da su. Ana idar da sallar magrib a babban masallacin