← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 143

Sashe 126

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi ba, za ki iya samun waje a zuciyarki ki yafe mata." Banza da shi ta yi tamkar bata ji abunda ya ce ba. Sai ma ture plate in abinci ta yi tare da goge bakinta da tissue ta mi e. Shima mi ewar ya yi tare da mi awa waiter ku insa sannan ya nufo hanyar fita tana biye da shi a baya. Shi da kansa ya kuma bu e mata ofa ta shiga sannan ya rufe ya zaga ya shiga ayan angaren ya tada mota. Kai tsaye wani rantsattsan hotel ya nufa ya kama akuna biyu. Boxes insu kawai suka ajiye sannan suka kuma fita. Wannan karan Prison direct ya wuce da ita domin nuna mata wani abu. Har inda Yasaar ya ke a kulle babu afa da hannu ya kaita tare da rakiyar jama'an. Abunda ya bata mamaki shine irin girmamawar da aka ri a bashi tun daga bakim gate har ciki. "Ko kin gane wannan?" ya fa i yana mai nuna mata Yasaar da ya koma tamkar tsumma sai jan ciki ya ke. Ashe akwai cutar sida a jikinsa wacce sai da ta gama cinye jikin ta bayyana. Ya rame ya lalace ya koma tamkar warangwal. Ga kuma uwa uba cutar haukar da ke damun walwarsa. Girgiza kai Meemah ta yi tare da fa in, "Ban ta a ganinsa ba!" "Wannan shine Yasaar in da ya sayar da ke a wajen Adelberto, sai dai bai ci ko wandala daga ku in ba ya samu wannan lalurar. Kamar yadda ya ci amanar ubangidansa haka abokinsa ya ci amanarsa. arya Esmeralda take maki da ta nuna maki hoton mamanki. Shi ya basu hoton mamanki ya ce su yi maki barazana dashi idan kin yi arin yi masu taurin kai. Mamanki na can cikin tashin hankali da ciwo a zuciya tun ranar da kika bar asar nan har zuwa yanzu. Ta jima tana bege da mararin ganinki!" Wani kallon banza Meema ta masa tare da juyawa ta fice daga akin ta nufi hanyar fita. Ajiyar zuciya Aizaad ya sauke kamun ya bi bayanta don ya fahimci akwai taurin kai a tare da. Kamun fahimtar da ita zai sha wuya sosai. "Ka kai ni wajen ita wacce kake kiranta da mamana idan har da gaske taimakona za ka yi!" Meema ta fa i daidai lokacin da suka arisa wajen mota. Bai ce mata komai ba sai bu e mata mota da ya yi ta shiga, sai shima ya bu e mazauninsa ya zauna tare da tada motar ya koma hotel in da ya kama. Sai da ya rakata har akinta sannan ya tsaya a bakin ofa tare da fa in, "Gobe da safe za mu bar Lagos zuwa Abuja inda iyayanki suke." Kallonsa ta yi bayan ta shiga akin tare sa fa in, "Abunda na sani shine a nan Lagos na bar mamana, kuma bata da kowa a garin Abuja. Idan baza ka taimaka min ba ni zan iya da kaina." Shigowa ya yi tare da jawo ofar ya rufe sannan ya har e hannunsa a irji ya furta, "Idan kika ha u da mamanki mai za ki mata?" "Kashe ta zan yi!" ta bashi amsa kai tsaye ba tare da tsoro ko shakka ba. Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce, "Baza ki iya ba! Kuma ina da tabbacin haka." "We shall see!" ta fa i tana mai kwantar da box inta a kan gado tare da bu e ta fiddo wata doguwar riga alar yellow ta aje sannan ta mayar da murfin box in ta rufe. "Can I?" ya fa i yana mai nuna mata gefen gado. "Sure!" ta fa i bayan ta kallesa sau aya ta kawas da kai. Zama ya yi sannan ya mai da hankalinsa gaba aya a kanta tare da furta, "Mahaifiya ta wuce duk inda kike tunani Meemah. Tashin hankalin da a yanzu iyayanki suke ciki kawai ya ishe su ba sai kin ara masu da iyayyarki ba. Look, ba zan yi forcing inki ki fasa udurinki ba, amma ina so ki sani duk wani abu da za ki aikata saboda idanunki sun rufe, wallahi tallahi ololuwar nadama zai saka ki ko da kuwa a iya maganar banza ya tsaya. Na san kin san hanyoyin kisa da dama sabida da irin rainon aka girmar dake. Kuma na san ko a cikin Villa za ki iya aiwatar da nufinki, sai dai ina garga inki sa kakkausar murya akan ki janye udurinki!" "Shawara ce ko uwani?" ta fa i tana kallonsa a tsiwace. "Duka biyun!" ya fa i tare da mi ewa. Sosai ya ke da damar da ileta akan duk wani burinta, sai dai bai son haka ya fi son ta fahimci illar abunda ta ke arin yi tun kamun ta isa ga iyayanta. Tun lokacin da ya fara ganinta a Colombia haka kawai ya ji sam bata cancanci abunda ta ke aikatawa ba. Hakanne ya saka ya yi ta bibiyarta har ya yi nasarar cafketa a Mexico ta fa a masa ko ita wacece. Shi senior officer a hukumar DSS, wani muhimmin aiki ne ya kai shi Colombia na tsayin shekaru hu u. Kuma da in da awa mahaifinsa sanannan mutum ne a Ar o Barkin o don yana da hannun jari a companynsu. Sannan suna da kyakkyawar ala a da Baffa aleri don makaranta aya suka yi kuma class mate insa ne shi. Har ya kai ofar akin sai kuma ya dawo kusa da ita tare da ajiye mata wayarsa sannan ya fice daga akin ya jawo ofa. Kamar baza ta ta a wayar ba, sai kuma ta kai hannu tare jawo wayar ta shiga kallon screen in babu kyafta idanu. Kallon fuskan wanda a asa hotonsa ta ga an rubuta da manyan ba i _HIS EXCELLENCY ABDUL-HAMEED ABDUL-AZEEZ_. Zoomin hotonsa ta,yi sosai tana ganin photo copynta a jiki. Don tabbas ko makaho ya shafa hoton ya kuma shafa nata fuskar zai tabbatar akwai ala a na jini tsakaninsu. Ba ta fahimci rubutun hausar da aka yi ba don ya mata tsauri sosai. Tana kaiwa kan hoton Zeenah ta tsayar da idanunta cak a kai. Wani irin abu ta ri a ji mai kama da kewa na yun uroma har bata san hawaye na zubo mata ba. Sai kawai ta samu kanta da kai hannu tana shafa screen in wayar. Ta kasa gaba ta kasa baya, sai kallon fuskan uwar take yi. Da kyar da ita yin gaba, nan ta shiga arba da hotunan kala-kalaa tun tana arama. Wasu ita ka ai, wasu kuma ita da aunty Ladi katifa da aunty Salma nice. Can kuma ta ara ganin hoton mamanta da wanda jikinta ya gama bata shine mahaifinta, sun yi matu ar kowannen su auke da murmushi a fuska, can gefe daga sama sai aka kawo hotonta tana karama, asan hoton kuma hoton Zeenah ce taba ri e a hannunta tana busawa. A asan hoton kuma aka yi rubutu kamar haka; _ oyeyyen sirrin shugaban asar Nigeria ya bayyana! Shugaban asan Nigeria mai ci a yanzu wanda aka fi sani da *DODONSU* ko kuma *Baban matasa* yana da iyar da ya haifa da amaryarsa kamun auren su. Amaryar tasa dai shahararriyar karuwa ce da ta yi aurin suna a garin Lagos tun daga shekarar dubu biyu. Amaryar dai ba ta tsaya iya karuwanci ba, kamar yadda kuka ga hotonta na baya, ita in 'yar waya ce kuma mai shafarar miyagun wayoyi. A wani majiya mai arfi ma ance bata tuba dagaa harkan shaye-shaye ba, kuma tana da hannu a duk wani shugawar da ake da kayan maye a asar musamman hodar iblis. Shin jama'a wani raddi za ku yi wa shugabar asar namu na sabon hukuncin da ya fitar cewar duk wa da aka kama da miyagun kwayoyi a harbesa? Ni dai na ce hukunci daga gida ake farawa!_ Duk da Meema ba ta fahimci hausar ba, amma ta tabbata ba magana mai da i akai a wajen ba. Kashe hasken wayar ta yi ta aje a kan gadon jikinta a mugun sanyaye. a kai ta yi da gwiwa sai ta samu kanta da fashe da kuka daidai lokacin da Aizaad ya turo ofar ya shigo. Har inda ta ke ya ariso, bai hana ta kukan ba don tabbas tana bu atarsa. Sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shuru tana shasshe a, shi kuma a wannan lokacin ne ya soma magama cikin kwantar da murya. "Muhimmancin Hakkokin Iyaye Tun ranar farko da Allah madaukaki ya halicci mutum ya sanya jagorancin 'ya'ya a hannun iyaye wanda yake shi ne uba na farko Annabi Adam (a.s). Wadannan hakkokin an yi bayaninsu a wasu ayoyin na Kur'ani mai girma, aka kuma hada tauhidi da biyayya ga iyaye domin nuni zuwa ga girman wadannan hakkoki a fadinsa madaukaki; "Kuma yayin da muka riki alkawarin Banu Isra'ila da cewa; kada ku bauta wa kowa sai Allah kuma ku kyautata wa iyaye" . Sannan har ilayau aka sake nuna matsayi babba da Annabi Yahaya ya kai saboda biyayya ga iyaye ana yabonsa da cewa: "Ya kasance mai biyayya ga iyayensa bai kasance shakiyyi ba ". Kamar yadda Annabi Isa (a.s) yake fada da dukkan alfahari cewa: "Kuma mai biyayya ga mahaifiyata kuma bai sanya ni shakiyyi ba" . Musulunci ya himmantu da nuni zuwa ga wannan matsayi na hakkin iyaye yayin da manzon rahama (s.a.w) yake shelanta cewa: "Aljanna tana karkashin tafin iyaye mata ne" . a wata ruwayar ya zo cewa; "Karkashin tafin iyaye mata, dausayi ne daga dausayin aljanna" . Imam Ali Sajjad (a.s) yana siffanta irin wannan hakkokin da fadinsa: Ka sani hakkin babarka cewa; ta dauki cikinka wasu watanni tana ba ka abinci daga 'ya'yan itaciya da nononta, kuma ta bayar da gaba dayan rayuwarta domin kare ka, kuma ba ta yi sanyi ba tana mai yarda da kwana da yunwa amma kai ka koshi, ta zama da kishirwa kai ka koshi, ta kasance babu kyakkyawan tufafi kai kuma kana da tufafi, ta shiga rana kai kana inuwa, saboda ba ka nono tana rasa bacci ta jure wa rashin bacci, ta kare ka daga zafin lokacin zafi da kuma tsananin lokacin sanyi. Kuma ta jurewa dukkan wata wahala domin kai, ka sani ba zaka iya gode wa ni'imar uwa ba,
Chapter 126 · 0% Book details