Sashe 121
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
18, Zubair 16/17 don babu nisa tsakaninsu, Aliyu kuma 14. Duk sun girma, matan ma sun isa aure. "Ina mama, mama tana ina?" Zeenah ta fa i gabanta na fa uwa. Da hannu Adda Maryam ta nuna mata aki da hannu. Da gudu Zeenah ta kwasa ta yi akin da mama Hafsat ke ciki. Tsaye ta same ta jikinta na rawa tana kuka. Wani irin kuka Zeenah ta arke da shi tare da furta, "Maamaaaa!" sai ta fa a jikinta ta rungume daidai lokacin da Baffa aleri ya shigo akin shi da an uwansa da su Adda Maryam. Kuka sosai suke yi ita da mama Halima. Su Adda Maryam ma suna ganinsu suma suka saki na su kukan suka arisa suka rungume su. Baffa alerin ma hawaye kawai ya ke yi, hata baffa Bel o don ba aramin tausayi suka ba shi ba. awa asa Zeenah ta yi bayan sakin mahaifiyarta ta kama afafunta tare da fa in, "Ki yafe min ba in cikin da na unsa miki na tsayin wannan shekarun don girman Allah. Mama ashe haka kika ji lokacin da na bar gida na shiga duniya? Ashe haka haka uwa ke jin una a zuciyarta idan 'yarta ba ta a kusa da ita kuma bata san halin da take ciki ba. Na cutar da zuciyarku iyayena, ku yafe min ko zan samu salama a cikin zuciyata!" tana maganar tana wani irin tamkar numfashinta zai bar jikinta. Hannu Mama Hafsat ta kai ta dafa iyarta da lalube don kukan da take yi ya saka idanunta sun rufe kuma dama ta auki shekaru tana jinyar arin jikinta da ya nemi shanyewa sabida damuwa da hawan jini, ga kuma ciwon zuciya da ke addabarta. Har yanzu idan ta yi tari jini ke zuba mata ko kuma idan amai ya yun uro mata. "Na yafe miki Zeenah tun kamun ma ki du a ki nemi yafiya ta. Tun lokacin da kika saka afa kika bar gina na riga ya yafe miki. Sai dai kin tafi kin bar ni da kewarki, kin bar ni da tunanin a wani hali kike ciki, mai kike aikatawa kuma a wani hannu kika ata. Kullum na kai goshina asa sai na ro i Allah ya sassauto da zuciyar mahaifinki ke kuma ya kuyo da hankalinki zuwa gida. Tun bayan tafiyarki ba bu wanda ya kuma samun farinciki a gidan. Maryama da Sa'adatu duk sun rasa igiyoyin aurensu sabida ke. Sa'adatu da tsohon ciki aka koro ta gida bayan duka a hannun miji da kuma tsangwamat uwar miji. Ita kuma Maryamu kishiyoyi da gorin miji da na danginsa ya kore ta daga gidan miji. Har yanzu an i bata anta tilo da ta haifa a can. Sa'adatu cikin da ta zo dashi sabida damuwa da rashin abinci da take fama dashi ya sa an bai fito da rai ba. Ga annanki nan su Sajida duk sun isa aure amma ba mai zuwa neman su da aure. Mahaifinki kullum cikin damuwa ya ke amma imarsa da yake ta ama da,shi da kuma zafin zuciya game da kafiya,sun hana shi saduda ya amshi addararsa da hannu biyu. Kin yi mummunar kuskure Zeenatu, amma mahaifinki ya fiki kuskure domin hannunka bai ru ewa ka yanke ka rai. Sannan kuma arna bata ta a gyara arna. Yanzu gashi sai nadama yake wacce ya riga ya yi ta a urarren lokaci domin komai ya riga da ya lalace!" gaba aya cikin kuka ta yi maganar. Juyawa Zeenah ta yi ta kalli mahaifinta da ya sunkuyar da kai yana kuka. Sai ta rarrafa ta kama afafunsa tare da fashewa da kuka ta shiga fa in, "Ni na sani ka yi iyakaci bakin arinka wajen bamu tarbiya ni da su Adda Maryam. Kana ari wajen sauke duk wasu nauye-nauyenmu da ke kanka, amma sai Allah ya jarabceka da fan ararriyar 'ya wacce bata gudun acin ranka. Na ata maka suna a duniya. Na shafawa, zuri'arka ba in fentin da har abadan ba zai gogu ba sai dai idan har abunda ya wuce zai dawo in gyara kuskuren da na yi wadda hakan ba zai ta a yuwuwa ba. Yau na gasgata maganar da kake yawan fa a mana cewar mutunci madara ne idan ya zuba ba zai ta a kwasuwa ba. Abbanmu ka yafe min abubuwan da na aikata maka. Ba kai ba, ni kaina ina dana sanin haihuwataa da kuka yi, domin da ba a haifeni ba da ban zame maku wannan bala'in ba. I'm shameful to this noble family!" wannan karar tsabar kuka har kyarma jikinta ke yi. agowa Baffa aleri ya yi tare da zaunar da ita a kan kujera sannan ya uka a gabanta ya furta, "Zeenatu ba laifinki bane ke aya. Kamar yadda mahaifiyarki ta fa i ina da kaso mafi rinjaye wajen lalacewarki. Domin da ban kore ki na tozartaki ba a titi da hakan bata kasance ba, kamata ya yi na zaunar da ke na miki fa a tare da nuna miki haramcin abunda kika aikata ta hanyar nasiha sa ayoyin da hadisan ubangiji. Amma sai zuciya ta kwashe ni na aikata aikin dana sani. Abun ya min ciwo ainun. Gani nake kamar ni bai kamata ace a cikin 'ya'yana a samu fasi a ba mai kaucewa hanyar Allah, na mance ko a cikin Annabawan ubangiji masu darajaa akwai wa a aka jarabce su da 'ya'yansu. Na mance ni in ba kowan kowa bane. Na auki girman kai da zafin rai na aurawa kaina. Ke ma kanki Zeenatu idan baki yafe min ba Allah sai ya mana hisabi domin ba ta hakan ya ce in tarbiyantar da amanar da ya bani ba. Gaba ayanku baku san mai ake kira da da in mahaifi ba, na kasance tamkar wani boss a cikin gidana babu wani nisha i bare sha uwa a, tsakaninmu balle har na ja ku a jiki mu yi jira na fahimci damuwarku. Don Allah 'ya'yana ku yafe min." ya arisa maganar tare da ha e hannayansa biyu yana neman gafara. Gaba aya sai suka taso suka rungume shi suna kuka. Da sauri baffa Bel o ya juya ya bar gidan gaba aya yana hawaye domin bawa mahaifi da 'ya'yansa waje su nuna wa juna aunar da ba a yi ba shekaru da dama. Daren ranar babu wanda ya rintsa tsakanunsu. Bajewa su kai a falo suna hirar da basu ta a yi ba. Sun yi kuma har sai da hawayensu ya afe lokacin da Zeenah ke basu labarin irin rayuwar da ta yi a gidan magajiya da kuma Lagos. Mama Hafsat sai da ta faki ido ta shiga bayi ta ri a kwarara aman jini saboda tashin hankalin da ta shiga jin irin rayuwar wula ancin da 'yar tata ta yi a garin Lagos. Ta ci kuka a bayin nan har numfashinta na barazanar aukewa. Baffa eleri shima zare jikinsa ya yi ya nufi akin da matarsa ta shiga ya tura bayin. Zaune ya ganta da as a asa tana kuka ga jinin da ya gani a bakinta da kuma asa. Sai hankalinsa ya yi mugun tashi ya nufe ta ya agota tare da soma jero mata tambayoyi akan yaushe ta fara aman jini. Hannunsa ta ri e ta sakar masa murmushi tare da fa in, "Ko yanzu na fa i na mutu Allah ya cika min burina. Abu aya kawai ya rage min wanda bai wuce ganin duka 'ya'yana mata a akin mazajensu ba cikin aminci." "Muje asibiti Hafsat, babu abunda zai same ki. Ba za ki mutu yanzu ba. Idan kin mutu ni kuma na yi yaya da tawa rayuwar?" "Ka saurare ni don girman Allah. Ban so 'ya'yana su san halin da nake ciki, ban so su ara shiga damuwa a cikin wanda suke kai yanzu. Don Allah ka ri e min wannan sirrin!" Kallonta ya ri a yi babu blinking kamun ya ha ata da jikinsa ya shiga zubar da hawayen tashin hankali kamun ya furta, "Duk da hakan zan kai ki asibiti a duba min ke. Zan kai ki a oye kuma na cikin estate innan ba." Jinjina kai Mama Hafsat ta yi alamar gamsuwa. Sai ya ara ameta cikin jikinsa. Abdul-Hameed dai ranar hankalinsa ba a kwance ya ke ba tun da Zeenah suka fice tare da mahaifinsa. Gashi lokacin da ya dawo bai ce masa komai ba sai ma korasa gida ya yi bayan ya kankara masa warning akan kar ya kuskura ya je gidan baffa elerin. A ranar dai ko queen Elizabeth ta kasa gane kansa, ta yi turanci har ta gaji ta ha ura ta koma nata akin ta kwanta. Shi kuwa yadda ya ga rana haka ya ga dare. Da sassafe ko takwas ba tai ba ya shiga mota ya tafi gidan baffa eleri don a can ma ya karya don ko da ya fito Hajiya Asma'u uwar 'yan boko bata farka daga barci ba don a'idarta ita ba a tashinta daga bacci har sai idan ita ta tashi da kanta. Sosai farinciki ya dabaibaye shi ganin Zeenah insa cikin farinciki. Don ko da ya isa duk da ba su yi bacci ba jiyan dukkansu a falo ya gansu bisa dinning suna karyawa. Sai da ya du a ya gaida Baffan da Mama Hafsat sannan ya ja kujeran dinning aya ya zauna. Ga a suka ha a baki suka gaida shi. Amsawa ya yi yana kallon Zeenarsa da gaba aya ta canza ta koma wata silent. Gyaran murya baffa aleri ya yi tare da fa in, "Ina ka baro matar da kake arin karyawa a nan? Ni fa ban son rashin adalci!" an susa eya ya yi tare da fa in, "Tana gida bata tashi ba, ba a tashinta idan tana bacci ni kuma yunwa nake ji kuma ina son ganin Zee-meed don jiya ko runtsawa ba yi ba ina ta tunanin kar ka dakar min ita." hankalinsa kwance ya yi maganaa kuma har wannan lokacin bai bar kallon Zeenah ba. Su Adda Maryam kuwa baki sake suke kallonsa jin abunda ya furta da ya basu kunya shi kuwa ko a jikinsa don bai ga wani abun damuwa ba cikin maganarsa. Mama Hafsat kuwa ko agowa bata yi ba sai yi ma ta yi tamkar bata ji abunda Abdul-Hameed in ya ce ba. Baffa aleri bai