← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 143

Sashe 58

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ASSOCIATION* ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*) ```Takenmu shine unkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.` Page 34 *Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!* ```Dukkan godiya su tabbata ga Ubangijinmu, mahaliccinmu mai kowa mai komai da ya sa muka ga zuwan wannan wata da ta wuce (Ramadan) lafiya. Allah don girmanka da zatinka ka sa muna daga cikin antattun bayinka. Ubangijin al'arshi, kai muke ro o domin kai ka ai ne muke wa laifi, muyi mu kuma arawa, amma hakan bai hana idan mun aga hannu mun ro eka ka amsa mana. Kai ka ai ne _LAM-YALID WALAM YULAD, WALAM YAKUL LAHU KUFWAN AHAD_! Albarkacin fiyayyan halitta (Muhammad Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama) ka saka tausayi a zukatan shuwagabanninmu domin su tausaya mana a wannan rayuwa da muke ciki. Allah don Rahmarka, don zatinka, don udirarka, ka yafe mana zunubanmu domin mun san duk abunda ke faruwa damu zunubanmu da in bin dokokinka ne suka jawo mana komai. Allah ka shirya duk wanda bai kan hanyar da kake so mu bi, idan kuma ba masu shiryuwa bane, Allah kai ka san yanda za kai dasu. Allah duk musulman da suka koma gareka a cikin wannan watan mai albarka da ma wa anda suka kwanta dama tun daga zamanin Annabi Adama har izuwa yau ka gafarta masu daga cikin gafararka, ameen!``` *BARKA DA SALLAH MUTANAN ARZIKI, DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA! ALLAH YA MAIMAITA MANA* *For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* https://chat.whatsapp.com/BmPYHeDVxgO3mMelztOhjK *_Don girman Allah zan sake fa i, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin addarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* "Dama ai ni na jima ina fa a maka Sabo da Kaza amfani kawai ya ke da kai domin cimma manufarsa. To idan ba haka ba, yaushe zai baka damar aukar fansarka? Kawai Yasaar ka yi abunda zai fissheka kawai don Sabo da Kaza yana gama amfani da kai zai yar da kwallon mangwaro ya huta da uda ne wallahi!" Abokin Yasaar da suke waya ya fa i hakan cike da zuga. Numfashi Yasaar ya fesar tare da fa in, "Shekara goma sha ina wa tsinannan aiki amma babu wani abunda ya tsinana min a rayuwa in banda Prison da ya jefa ni tare da bada an uwana rabin jikina a ka kashe matsayin ni. Dole ne ma na ci amanar wannan an iskan wallahi!" "Kai ba ka ji sunansa ba, Sabo da Kaza fa! Ai hakan na nufin duk yanda kuke da shi hakan ba zai hana ya yi maka kafurci ba, wata ila ma ya zama ajalinka! To wallahi kamun ya farga ka tarwatsa shi kai," abokin Yasaar ya fa i yana ara kunna shi. "Bari, zan kira ka zuwa anjima da yamma!" Ya fa i hakan tare da yanke wayar yana wani dogon nazarin ta yanda zai yi da rayuwar Laushi da na arta Meema. _Abuja_ Wani irin wankan fitar hayyaci Mardiya ta ke yi a cikin bayi da shower gel in da ta gani ciki. Sai da ta kusa zuba kwatar goran a jikinta, bata samu natsuwa ba har sai da ta ji jikinta ya koma babu abunda ya ke sai amshin shower gel in nan sannan ta ha ura ta fito daga bayin. Jakar da Aunty Ladi ta shigo mata da shi ta bu e tare da fiddo audugar mata kasancewar tana fashin sallah ta saka sannan ta mayar da kaya a jikinta. angaren Mama Halima kuwa, ta daina kuka sai tagumin da ta zabga tana kallon anta mata da suka fita shiga tashin hankali da auren da Babiyo ya yiwa Baffansu. Baffa Gi o kuwa ya shige akinsa ya turo ofa har da saka key saboda bai son zuwa wajen amarya. Abun ya zamewa mama Halima goma da ashirin don idan har bai tafi ba, wani matsalar ce za ta sake ullowa idan Mamiyo ta shigo gobe da safe domin duba ratayayyar warya. Don da kanta ta ke zuwa dubawa ba aike ta ke yi ba. Mama Halima ta yi bugun ofar har ta gaji, amma Baffa Gi o bai bu ewa. Ganin zaman parlourn ba zai fissheta ba ga a sun saka ta gaba da kuka, sai ta mi e ta nufi aki tare da rufo ofa ta auki waya tare da turawa Baffa Gi o sa o kamar haka; _Baffan Habib, idan har ba so kake ka saka a kore mu kamar yanda aka kori Hamma Bel o da Hamma aleri ba, ka yi ha uri ka fito ka wuce akin amaryarka. Idan kuma so kake Babiyo ya yanke hukunci a kai na, fine! Don na tabbata baka manta kashedinsa a gare ni ba. Kuma idan har baka kwana akin amaryarka ba a yau, hakan na nufin ni ce na hana ka a idanun Babiyo da Mamiyo da sauran da ke goya masu baya!_ Bayan kamar mintuna bakwai da tura masa sa on, sai ta ji maganarsa a parlourn shi da ansa. Rintse idanu ta yi tana hamdala cikin zuciya. Hawaye ne suka sillo mata lokacin da ta ji fitarsa daga akin, dama ta riga ta san ba zai shigo ba saboda gudun acin ranta. A daren dai barci arawo ne ya kwashe ta. _Mamiyo_ Mahaukatan maruka Mamiyo ta ri auke Baffa Jibrila da shi cikin zafin rai da acin zuciya. Shi kuwa Baffa Jibrila sai wani irin huci ya ke idanunsa sun ada sun yi jazur tsabar yanda zuciyarsa ke tafasa. "Wannan ai hauka ne da neman tona mana asiri a cikin Ar o Barkin o! Ka yi hauka ne, Jibrila? Dukkan mu nan da kake gani kowa a tafashe ya ke! Mai yasa sam wani lokacin ba ka iya sarrafa kan ka ne? Ka san mai ka aikata kuwa? Allah ka sa wannan yaron bai mutu ba!" Baffa Mahmud wan Baffa Jibrila ya fa Mamiyo kuwa bayan ta gama kakkafta masa maruka sai ta shiga zagaye akin hankalinta a matu ar tashe don har zufa igo mata ya ke duk da sanyin Ac akin. "Wannan yaron wani lokacin ji na ke kamar ba jinina bane! Da i kawai ya na neman tona mana asiri. Wa ya fa a maka kashe Abdul Hameed shine zai warware mana komai? Waye ya baka damar bin bayansa har ka aikata wannan anyan aiki, Jibrila? Ka fini son ya mutu ne? Ko kuwa ka fini dabara, basira da kuma walwa ne?" Mamiyo ta fa i a hassale. "Ki min aikin gafara Mamiyo, na auka abunda na yi zai sanya ki cikin farin ciki, ban auka shirme na aikata ba!" Baffa Jibrila ya fa i kansa a asa. "Sha-sha-sha!" Mamiyo ta fa i bayan ta jefa masa wata uwar harara tare da aukar wayarta a bakin makeken gadonta ta shiga lalubo Number in Hafizu. "Akwai matsala babba, Hafiz! Kana ina ne?" Mamiyo ta fa i bayan Hafiz ya aga wayar. Hafiz da ke du e gaban Babiyo da ya yi kiransa suna tattauna wata magana ya furta, "A'a ban yi nisa ba ina wajen Babiyo, yanzu ya kira ni. Ku ci baccinku kawai idan na dawo zan ci nawa," ya arisa maganar kamar da matarsa ya ke magana a kan wayar. Mamiyo kuwa da jin haka ta katse wayar don bata da bu atar fashin ba i kasancewar ta fahimci ba zai iya wata magana da ita ba saboda suna tare da Babiyon. "Yanzu haka Hafiz yana tare da Babiyo, amma na tabbata zai sake kirana nan ba jimawa. Zan saka shi ya yi clearing wannan matsalar da ke shirin kunno mana," Mamiyo ta fa i tana mai saka mazaunanta a kan kujera. "Ka tashi ka tafi wajan iyalanka, gobe idan Allah ya kai mu ma arisa maganar," Babiyo ya fa i yana kallon Hafiz da ke ta an kame-kame. Murmushin ya e ya yi tare da fa in, "A'a ba ayi haka ba, Babiyo. Ba wani abu bane fa, ta ji shiru ne shine ta ke tambayata ina ina ne in dawo in ci abinci," da kame-kame irin na marasa gaskiya ya fa i hakan. Shi ma Babiyon murmushi ya yi tare da fa in, "Uhm! Jeka kawai wajen matarka, Hafizu. Ai hakan ake son mace wajen kula da mijinta. Je ka ci abinci tare da iyalanka." an sunkuyar da kai ya yi alamar girmamawa tare da fa in, "Godiya na ke Babiyo, Allah ya ara girma." Kai kawai Babiyo ya gya a, shi kuma Hafiz ya mi e da sauri ya fice daga parlourn. Mota ya bu e ya shiga tare da tadawa ya bar Ar o Barkin o Street. Sai da ya yi nisa da gidan sannan ya yi parking tare da dannawa Mamiyo kira. Mamiyo na ganin kiran Hafiz ta yi murmushi tare da aga kiran ta kara a kunne. "Uwar akina kin kira ina kusa da wannan tsohon, amma dabarata ta yi aiki don yanzu haka gani na fito daga gidan," Hafiz ya fa Kai tsaye Mamiyo ta tafi ga kan batunta, "Jibrila na neman ata mana aiki Hafizu, don ya bi bayan Abdul Hameed zuwa ke an gidansa ya bigesa da rodi a kai saboda rashin hankali." "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ya a kai ya yi wannan aika-aikar haka? Wayyo Allah ni kai na! Hajiya yanzu ya za muyi?" Hafiz ya fa i a rikice. "Abunda nake so da kai yanzu, maza-maza ka fita ka nufi gidan ka auke sa ka kai shi Ar o Barkin o specialist hospital, bayan ka kai shi sai ka kira Babiyo ka fa a masa kana kan hanyan komawa gidanka sai ka ga motar Abdul Hameed in wani na binsa a baya sai kai ma ka rufa masu bayan, sai ka ara da ce masa kana shiga ka gan shi kwance cikin jini kuma baka ga wanda ke bin sa in ba," Mamiyo ta fa "Hakan za ayi, bari na tada mota, sai kin ji daga gare ni," yana gama fa in haka ya katse wayar tare da tada motar ya figeta da sauri. Kai tsaye
Chapter 58 · 0% Book details