← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 143

Sashe 38

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ku ka je kuna iskancinku tare da shaye-shaye ko! To ya yi kyau. Kin kyauta Laushi." "Wani irin maganar banza ce wannan, Katifa? Ni da ke wa ya fi son Meema? Kar ki manta ta jikina ta ratso ta fito a gaban idanunki. Duk duniya akwai wacce ko wanda zai nuna wa Meema soyayya ce da tafi tawa? Ya zan fa a miki abunda ya faru amma ki i yarda da magana ta! Wallahi, tallahi idan na kwanta da wani a namiji yau in nan, Allah ya auki raina yanzun nan ko kuma gobe mota ta yi kwatsa-kwatsa da kwanyata!" Ta arisa maganar cike da wani irin zafin rai da unar zuciya. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke don yanzu kam ta yarda da awarta. Hatta Salma nice da bai furta ko ala ba, shi ma ya yarda da abinda Laushin ta fa "To amma ina kika je haka kika kai dare? Gaba aya hankalinmu ya tashi wallahi. Duk mun auka kina tare da Sabo da kaza a hotel shiyasa ranmu ya aci," Ladi ta fa i da sanyin murya. "Muna tare da shi, amma wallahi babu abunda ya ha a ni da shi. Asalima ban san lokacin da ya fitar dani daga asibitin nan ba. Last abunda zan iya tunawa shine; zayyano min halin da Meema take ciki da ya yi. To tun daga wannan lokacin ban kuma sanin inda kaina yake ba," fa in Laushi bayan ta zauna gefen Ladi. "Mai suka ce ya faru da Meeman? Ba dai fya en ya yi mata ba ko?" Ladi da Salma nice suka ha a baki suka fa Sai da Laushi ta sharce hawayen da suka gangaro mata sannan ta basu labarin abunda Sabo da kaza ya fa a mata akan halin da Meeman ke ciki. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! In Sha Allah babu abunda zai samu kwakwalwar Meema. Meema za ta warke! Ai likita ba Allah bane," fa in Ladi tana kuka sosai. Salmanu an daudu kuwa mutuwar zaune ya yi bayan sauraron duk abunda Laushin ta fa i. Can ya aura hannu a kai ya kwan ama wani ihu tare da fa "Wayyoo ni kaina! Wayyo Allahna! Wayyo ni Salmanu jikan iya!" (Finally! Yau dai Salmanu ya kira kansa da namiji. Haka su kai ta kuka babu mai lallashin wani. Can dai Ladi Katifa ta ce, "Gaskiya Laushi, tunda ke ce uwar yarinyar nan ki zo ki zauna cikin daren nan ni da Salma nice mu tsefe miki kanki tasss ki wanka musulunci sannan ki alwala ki du ufa nemawa yarinyar sau in ubangiji, muma kuma za mu taya ki. Sannan kuma idan so samu ne, tunda gobe Litinin ki tashi da azumi. A cikin watannan gaba aya ki kiyaye sa on Allah domin samun damar Allah ya amshi addu'arki don ance addu'a da tsinuwar uwa tamkar yankan wu a haka yake ci." "Wallahi maganari gaskiya ce. Gobe-goben nan zan fita na yanko mata yadikan hijjabai kala biyar, kuma ba zan shigo nan da su ba sai a ike. Idan komai ya daidaita sai ki cigaba da sharholiyarki," fa in Salmanu an daudu. Ita dai Laushi bata ce komai ba. Duk yanda suka yi da ita a cikin daren nan haka take bi. Bayan sun an ta a abinci, sai suka hau tsefe kanta wanda ya auke su har biyun dare don Ghana weaving ne kuma anana. A haka ma don su biyu ne kuma suna da saurin tsifa. "Yauwa to Alhamdulillah! Yanzu sai ki shiga daga cikin bayi ki wankan tsarki sosai, sannan ki auro alwala ki fara sannan da wannan gyalen na Ladi na ga yafi naki an girma kamun dai zuwa goben," Salma nice ya fa i yana aga fashminan Ladi Katifa. Shiga bayin laushi ta yi tare da yin wankan tsarkin sannan ta fito aure da towel gashinta na igan ruwa. "Ni da zan baki shawara ki auka da cewa zan yi ki ha ura da wannan kitson arin da kike yi tunda tubarakallah kina da suma sosai. Gashi kitson nan da kike yi duk ya cinye miki gaban gashi," Ladi Katifa ta fa Ita dai Laushi ko ala bata ce ba. Ta koma kamar wata salaha mai tsoran Allah. "Ki ce Ash Hadu Allah Ilaha Illallahu Wa Ash......." "Kai dallah rufewa mutane baki! Ridda ta yi da kake arin bata kalmar shahada kamar wata tubabbiya?" Ladi Katifa ta katse Salma nice. "Haba ke kuwa Ladi! Irin wannan arna da a ka yi shekara da shekaru ana yi, ai har sai a fita daga musuluncin ma ba a sani ba," Salma nice ya fa "Oh Allaaah! To Allah kyau. Ai sai ki kar i kalmar shahadar ki koma cikin musulunci," fa in Ladi Katifa. Laushi bata saurare su ba ta saka rigar da ta kira tare da rolling fashminar Ladin ta tada sallah bayan ta shimfi a gyalenta a asa. Gaba aya duk sai ta jita wata kala don baza ta ta a iya tuna when last ta saka goshinta a asa ba da sunan gaishe da Allah. Sai ta ji wani irin kunya da nauyi ya kamata kamar Allah na gabanta tana kallonsa. Babu abunda ta manta game da karatun sallah don sun samu horo sosai a wannan fannin a wajen abban na su wato, malam Ayuba. Tun su Ladi na kallonta suna irga raka'a bibbiyu da take yi har barcin ya kwashe su. Laushi kuwa ko runtsawa bata yi ba har a kai kiran asuba wanda ta manta yanda ake jin kiran sallar a kunnanta. Addu'a ta yiwa Meema sosai bayan ta gama maimaita kiran sallah kamar yanda addini ya umarta. Sai da gari ya yi sanke taar sannan Laushi ta tashi ta nanna e gyalenta tare da fita daga akin ta nufi akin da aka kwantar da Meeman, luckily sai ta gansa a bu e sai ta yi saurin shiga har tana cin tuntu Meeman dai na nan kamar jiya, banda zuciyar babu abunda ke motsi a jikinta. "Allah don girman zatinka, ka tashi kafa un yarinyar nan ba don halina ba. Ya Allah kar ka dubi girman laifina a gare ka, na san ni mai zunubi ce. Allah don girman ka, don aunarka ga fiyayyan halitta, don tsarkakakkun sunayanka guda casa'in da tara, don zatinka, don tausayinka, don alfarmarka ya ubangiji ka tashi kafa un wannan yarinyar da bata san komai ba," ta arisa maganar tana mai ha e hannayenta guda biyu sannan ta kai goshinta asa ta yi sujada tare da fashewa da raunataccen kuka mai ta a zuciyar mai sauraro. Ta jima da kanta a asa bata ago ba kuma bata bar kuka ba har sai da Nurse in da ke kula da Meeman ta shigo ta ago ta. "Ki yi ha uri, za ta tashi in Sha Allah!" Nurse in ta fa i bayan ta dafa kafa unta. a kai kawai Laushi ta yi tare da kama karfen gadon tana kallon Meema wacce idanunta ke arufe. "Ku min ha uri in zauna kusa da ata don Allah," ta fa i bayan ta kalli Nurse "Babu matsala in dai baza ki hayaniya ba!" Nurse in ta fa "Ba zan yi ba in Sha Allah!" Laushi ta fa i tana jin da in sabon damar zama a akin don ta ri a kallon arta. Karfe tara Sabo da kaza ya kawo masu breakfast sannan ya yi sallama da Laushi a kan zai je Togo, tafiyar gaggawa ta same shi, sai dai ba zai wuce kwana uku zuwa hu u ba. Sannan ya bata kwarin guiwa a kan in Sha Allah Meemah za ta tashi. Nan da sati guda idan kuma bata farfa o daga doguwar suman da doctor ya ce ta yi ba, to zai masu visa su tafi India a duba ta kawai. Abun dai kamar wasa Meema ta kwashi sati guda bata farfa o ba a wannan asibitin. Ko anyatsanta bai motsi. Laushi ta yi wani irin ramewa. Kuma a cikin sati ayan nan ta koma kamar sabuwar halitta domin sallah bai wuce ta, haka azumi don azumin Annabi Dawood ta koma yi idan ta yi yau gobe baza ta yi ba sai jibi. Dama tun a rana ta biyar Sabo da kaza ya dawo daga Togo, kuma tun a can in da ya samu labarin jikin Meema bai improving, sai kawai ya shiga arin yi masu passport. Ranar da ya diro ranar passport insu ya diro, private jet suka bi suka tafi India, Meema, Laushi da kuma Sabo da kaza. Suna isa doctor hu u suka rufa mata, tasa-tasai kuwa anyi mata sun fi goma, anyi hoton walwa guda uku. Kuma Alhamdulillah bayan kwana biyu result ya fito. Don tun kamun result ya fito Meema ta farfa o daga dogon suman da ta fa a, sai dai ko da ta farfa o da ihu da kuma fizge-fizge ta farfa o har sai da aka mata allurar bacci. Doctor ya kira Sabo da kaza da Laushi office ya masu bayanin cewar Meema bata samu matsalar komai a kanta ba ban da buguwa, doguwar suma ta fa a sakamakon gana mata azabar da aka yi da kuma allurar da aka mata da ta fi arfin walwarta. Don ma dai ka an ne aka mata, amma da ya wuce hakan da tabbas walwarta sai ya ta u. Kuma wannan fizge-fizgen da take yi tsorata ta yi da kuma firgici shiyasa. Amma nan da wasu an kwanaki duk za ta bari idan har aka kwantar mata da hankali aka nuna mata soyayya da kulawa har ta manta wancen abun da ya faru. Wani irin sanyin rahama da da i Laushi ta ji jin babu wani mummunar cuta da ta samu arta. Satin Meema aya a India ta warware, sai dai basu dawo Nigeria ba sai da suka biya asashe biyu, wato Paris da Dubai. Meema ta samu farin ciki da mahaifiyarta da bata ta a samu ba a rayuwarta ba. Domin ta ririta kamar kwai. Sun auki hotuna babu adadi. Irin kulawar da Sabo da kaza ya basu ita da arta ya saka gaba aya ta sakankance da shi har ta mance da ibadar da ta soma, duk da dai sallar ana yinta, amma wani lokacin a urarran lokaci, amma kuma karuwanci an koma ruwa tsundum da shaye-shaye. Idan
Chapter 38 · 0% Book details