Sashe 116
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma sun yi luhu-luhu da su alamar an kwana kuma an yini ana kuka. Da dasasshiyar muryanta ta gaida shi shi kuma ya amsa yana mai bata girman na kasancewarta matar babban wansu duk da ya girme mata. "Adda Saudatu!" ya yi kiran sunanta kuma sai ya yi shuru yanaa kallonta don har ga Allah ya fahimci irin abunda take ji a zuciya. Ko kamun ya ara cewa wani abu, sai ga sallamar Abdul-Hameed bayan ya turo ofar. Turus ya tsaya yana kallon mahaifiyar tasa da ta masa kallo aya ta sunkuyar sa kai. Gaba aya sai ya ji jikinsa na masa rawa kuma afafuwansa sun gaza aguwa sabida yadda ya ga kamannin mahaifiyar tasa ta canza. "Taho Abdul-Hameedu zo nan zauna." Baffa ya fa i yana nuna masa asa kusa da afafun Nennen. yar ya iya aga afafunsa ya tako ya zauna a inda Baffan ya nuna masa. Daidai nan Ramadan shima ya fito daga nasa akin sai shima baffan ya nuna masa wajen zama. "Adda Saudatu, don girman Allah ina so ki an bani hankalinki domin yi maki wani bayani." Baffa ya fa i sai ta ago ta kallesa. "Na san kina cikin tsananin ba in ciki da acin rai bisa abubuwan da suka faru shekaran jiya. Na san kowacce uwa za ta ji zafi sosai ace anta ya aikata abunda ya yi shekaran jiya. Kamun in tsunduma kan batun da nake tafe dashi, ina so ki kwantar da hankalinki anki mai auke da cuta mai karya garkuwar jiki domin Jawaad arya yake yi. Tun a ranar na tafi na same shi kuma ya fa a min gaskiya har da hujjoji don sai da ya bani rahoton lafiyar Baffa alerin. Bata auke da HIV kawai ya fa i hakane domin kishi don shima yana sonta ne. Tare suka tafi can asar da Babiyo ya tura shi, tana tare da shi kusan tsayin watanni hu u zuwa biyar." Da mugun ma aukakin mamaki Nenne ke kallon Baffa Modibbo kamun ta furta, " iyar Hamma aleri kuma? Magana fa ake akan karuwar da ke neman raba kawunan 'ya'yan gidannan tare da arin kashe min aurena." Girgiza kai Baffa ya yi tare da fa in, "Ba ita ke neman kashe miki aure ba, Marwa ce. Kuma tabbas yarinyar iyar aleri ce, jaririyar da Hafsatu ta haifa. Lokacin da Babiyo ya kore su daga gidan nan ita ce jarirai do ko arba'in ba su bai a gidan nan aka fitar da ita babu kaya, kin tuna?" Jinjina kai Nenne kawai ke yi hawaye na kwarara a idanunta. Da yar ta iya bu e baki ta ce, "Hamma Modibbo how comes?" Gyara zama ya yi tare da warware mata labarin da Baffa alerin ya bashi wanda ya yi sanadiyar da ya saka ya kori Zeenah daga gidansa har ta fa a karuwanci. Gaba aya tun dagaa kan Nenne, Ramadan da Abdul-Hameed kuwa suke yi. "Wannan wani irin banza hali da akar zuciya ce ke bibiyar ahalin gidan nan na korar a idan ya aikata kuskure! Inna lillahi wa'inna ilaihir rajun " Nenne ta maimaita sau uku tana mai rufe fuska da tafin hannunta bayan fashewa da kuka. akin ya yi shuru na wasu lokaci kamun Abdul-Hameed ya bu e baki tiryan-tiryan ya soma ba su labarin ha uwarsa da Zeenah har zuwa kusantarta da ya yi wanda daga shi har ita basu san mai ya jasu zuwa ga hakan ba. Ya kuma ara masu da bayanin d tunda wannan abun ya faru ya mance da ita a rayuwarsa tamkar an shafe masa walwa, sai kwanannan komai ya dawo masa tamkar dai aikin aljanu. Bai rage komai ba har cikin da ya yi mata da haihuwar da ta yi da kuma sace 'yar da aka yi. Sosai kukan Nenne ya aru har jikinta wani irin rawa yake yi tamkar mazari. Hatta Modibbo ya tsorata da yadda yaga Nennen na kuka. Sai ya shiga bata ha uri tare da fa a mata maganganu masu kwantar da hankali da kuma fa in ubangiji game da tawakkali. "Don Allah ku je ku kawo min Zeenatu nan gidan na ganta. Ku auko min ita don girman Allah. Ashe 'yata ce! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah ka sassauta mata. Allah ka sa muci wannan jarabawar." Abdul-Hameed tun da ya ji Nenne ta ce ya auko mata Zeenah ya tashi da sauri ya fice daga akin, gaban rigarsa duk ya ji e da hawaye. Ko kallon Isma'il da ke masa magana hankali tashe bai yi na ya shiga mota ya tada ya bar gidan. Ganin haka sai Isma'il ya yi saurin nufa cikin gidan don sanin abunda Abdul-Hameed in ke wa kuka. Bayan kamar mintuna goma sai ga shi ya dawo shi da Zeenah da idanunta ke a soye alamar ita ma kwana dai ta yi tana kukan. Shi ya mur a handle ofar ta bu e sannan ya nuna mata hanya ta shiga. Kanta na asa ta shiga ciki, sai ta samu waje ta ra e ta zauna jikinta na rawa. Da sauri Nenne ta taso tana mai toshe bakinta sabida kukan da ya ara yun uro mata. Ita kuwa Zeenah ganin Nenne ta nufo ta gadan-gadan sai ame jikinta tare da rintse idanu tana jiran saukar duka. Zaro idanu ta yi jin an agota an rungume tare da sakin kula, kawai sai ta samu kanta itama da fashewa da matsanaicin kuka. Hannunta Nennen ta kama ta zaunar a kan kujera tare da zama asa tana kallonta. Sai yanzu ta ke hango tsantsan kamanninta da aleri da kuma Babiyo. Don idan kaga eleri ka ga Babiyo, haka idan ka ga Zeenah ka ga aleri tamkar ya yi kaki. Ba tare da sun tambayeta ba ta shiga basu labarin komai tun daga farko abunda ya saka baffanta ya koreta da irin wula antata da ya yi a titi, alwashin da ta auka, zuwan gidan magajiya, ha uwarta da Ladi katifa, zun en da akai ta yi wa mahaifin har ya kai an daina binsa salla, ha uwarta da Abdul-Hameed da yanda ya canza mata rayuwa har ta yi nadamar abunda ta aikata da kuma udurinsu na yin aure bayaan ta gama istibura'i, tsautsayin da ya afka masu na yin Zina har ta samu ciki da kuma shafewar tunaninta, zuwanta gida domin auko sar ar zinari, rigimar da suka yi da mahaifinta har ta caka masa wu a bisa rashin sani, guduwanta Lagos da kuma rayuwarta da ta yi, ha uwarta da Salma nice da kuma Yasaar,fa ansu da Marwanatu, ha uwarsu da Habib da Jawaad, komawarta gidan Sabo da kaza da zama da, abubuwan da ake aikatawa a can, ciwon da ya same ta na raunanniyar jijiyar jinin walwa da kuma dalilin zamanta a Denmark tare da Jawaad. Da hannu bibbiyu Nenne ta ri a kaiwa Zeenah duka tana kuka a lokaci guda tare da fa in, "Kin yi kuskure babba, kin aikata kuskure Zeenatu. Abunda kika yi bai dace ba sam. Idan bawa ya shiga wani musiba wajen Allah yake komawa ba fa awa halaka irin wacce kika yi ba. Yanzu menene ribar abunda kika aikata. Kinsan illar da kika yi wa kanki kuwa? Kin cuce mu kuma kin cuci kanki har da zuri'ar da za ki yi nan gaba don wannan tabon da kika yafawa kanki zai ta bibiyarki ne har sai kin ji tamkar ki birne kanki da ki huta da ba in cikin duniya. Mai yasa? Mai yasa kika aikata hakan? Why Zeenah?" ta arisa da arfi tana mai jawowa jikinta ta rungume. "Babban mai laifin shine Hamma aleri. Babu inda addini ya ce ka kori 'yarka mace don ta aikata kuskure. Da a lokacin da tai cikin farko bai kore ta ba, ya jata jikinsa ya nuna mata illar abunda ta aikata tare da azabar da Allah zai yi wa mazinaci da duk hakan bai faru ba. Maimakon hakan sai ya turata tura ta duniyar bayan aikata mata da tsinuwa da bala'i kala-kala da ya ke jifanta da shi. Wallahi idan Zeenah na da laifi hamma shi ke da kaso saba'in bisa ari. Haba! Wannan ba ar zuciya da mai ya yi kama? Kuma abunda zai baki mamaki Adda Sauda, wallahi har yanzu babu nadama a idanunsa. Ba ki ga irin dukan da ya yi mata a asibiti ba yana ikirarin kashe ta. Wallahi zafin zuciyar Hamma tsoro ya ke bani. Ya fi Babiyo nesa ba kusa ba!" baffa Modibbo ya fa "Idan shi bai sonta ni ina so ya bar min. Hannunka na ru ewa ka yar da shi ne? Ko so ya ke ta kuma fa awa wani halakar? To ni ma ina bayan Babiyo In sha Allah sai Abdul-Hameed ya aureta. Allah dai ya bashi lafiya ya dawo da su cikin aminci." ta arisa maganar da kuka. Abdul-Hameed kuwa ji ya yi tamkar ya zuba ruwa a asa ya sha don da in abunda mahaifiyarsa ta furta. "To yanzu mu dawo batun ita 'yar da Zeenah in ta haifa. Ta yaya za mu samu nasarar cafke shi an iskan har ya fito mana da jikarmu. Ohh! Allah sarki yarinya baki ji ba kuma baki gani ba." Baffa Modibbo ya fa i yana mai zabga tagumi. Sai a lokacin Abdul-Hameed ya bu e baki tare da fa in, "In sha Allah sai inda arfina ya are wajen dawo da Meema cikin ahalinta. Gobe da kaina zan tafi Lagos in domin soma bincike akan shi Sabo da kazan da kuma tsinannen Yasaar in, In sha Allah za ta bayyana cikin gaggawa." Girgiza kai Baffa Modibbo ya yi tare da fa in, "No, babu inda za ka for now sabida abunda ke gabanka yanzu. Ni da kaina zan koma Lagos na yi bincike sosai. Don idan ban mance ba kamar akwai wanda naji ance an kama shi da miyagun wayoyo har da bama-bamai da yake ajewa a gidan budurwansa, kuma babban mutum ne shi." Da sauri Zeenah ta kalle shi tare da fa in, "Ina kyautata zaton shi inne. Don ban manta ba lokacin da mu kai magana da Ladi Katifa a waya lokacin ina masaukin da wanda Jawaad ya saka ya auko, ta fa a min an sanda sun zagaye gidan da na ke ciki." Jinjina kai Baffa ya yi tare da fa