Sashe 12
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Saminu bama irin wannan wasan da kai! Don Allah ina abokinka? Ya min al awarin zai turo iyayensa domin su zo neman aurena yau. Gashi yanzu goma saura babu wanda yazo." "Ca ! Lallai Safiyanu anyi an iska na bugawa a jarida. To wallahi arya yake maki. Iyayansa ma ba an nan bane. Daga can auyen Katsina yake. Ni na ji yana cewa ko Dabai ko Inaaa..... Gaskiya na mance sunan auyen. Ko ma otanku da kike gani yana zama a gidan wallahi taimaka masa suke yi. Shi arya ne kawai! Almajiranci yake yi a nan in shekaru can da suka wuce. To ya ta a aiki a gidan suna an bashi abinci da ihisani shiyasa kika ga kamar ya zama an gida. Ganin sa kuma da kike yawan yi har kuka ulla soyayya; zuwa yayi domin su gaisa amma ko su mutan gidan basu san mahaifarsa ba." Hannu Zinatu ta aura a kai tare da rushewa da kuka ta shiga fa in, "Allah ya isa tsakanina da ku. Kuma sai Allah ya saka min. Da ha in bakinka aka yaudareni." Tana gama fa in haka ta wuce da gudu. Wani dogon tsaki ya ja tare da fa in, "Aikin banza aikin wofi! Kwa ayinki dai ya ja maki. Dama ai ance duk wanda ya hau motar Kwa ayi babu inda zata sauke sa sai a tashar wula anci. Kuma ai dama kwa ayi mabu in wahala ce! Sha-sha-sha sakarya." Da san a ta shigo gidan tana tafiya tana waige-waige. Fizgo hijjab inta taji anyi da arfi sannan akai ball da ita. "Daga gidan uban wa kike a cikin daren nan? Duk cikin ana kece fitinanniya wacce bata gudun zuciyata." Ya fa i hakane yana mai kai mata duka da zabgegiyar bulalan hannunsa. Ihu ta buga da arfi tana mai sosa bayanta tare da turo baki. "Ni zaki mayar mutumin banza? To bari kiji; Wallahi aure tsakanin ki da Mansur babu fashi, kuma sannan daga yau ko kwar gida ban yarda ki sake fita ba idan har nine mahaifinki. Dama ni na san babu wasu da zasu zo gidan nan neman aurenki. Kin ji na rantse da girman Allah idan kika sake kika bijiremin a karo na biyu, ko kuma kika watsa min asa a idanu ta hanyar auko min abun kunya, wallahi sai dai ki nemi wani gidan zaman ba nan ba. Mutuniyar banza mutuniyar hofi..." Ya mayar da kallonsa wajen mahaifiyarsu tare da fa in, "Ke kuma Atine, idan kin ga dama kar ki saka mata idanu. Ki barta ta cigaba da fita tana gantali ana zagina a titi." Yana gama fa in haka ya yar da bulalan ya wuce aki. Wawan harara uwar ta bita da shi tare da fa in, "Ke dai Zinah ba kiji da in rayuwarki ba wallahi! Ke yanzu baza kiyi koyi da an uwanki ba? Wallahi ki natsu ki kama kanki." Tun daga wannan rana Zina bata ara samun sararin fita ba. Kullum tana umshe a aki tana kuka. Gashi bikinsu sai da a matsowa yake yi. Kullum da wani irin mugun zazza i ta ke kwana. Ga wani irin miyau da ke taruwa a bakinta. Kasancewar mahaifiyarta fushi da ita take shiyasa ko bi ta kanta ba ta yi. arta Sa'adatu ce ta soma lura, sai dai ita ma bata fahimci ciki bane da anwar tata har sai da ta samu mahaifiyarsu ta fa a mata Zinatu fa bata da lafiya sosai sannan mahaifiyar ta nufi akinsu domin duba ta. Tana shiga akin lokacin Zinatu ta tashi zaune, Maryama kuma ta mi a mata ruwan da ta bu ata zata sha. Tana kai ruwan baki ta soma kelaye amai kamar zata amayar da hanjinta. Aman kuma kore shataf. Wani irin bugawa irjin mamar tasu ya dunga yi tana ta arin aryata abunta take zargi a zuciyarta. A hankali ta taka gaban Zinatu tare da bu e kwayar idanunta aya bayan aya sannan ta jeho mata tambayoyi kamar haka; "Zinah, abunda zaki mana kenan? Zina yaushe rabon da kiyi al'ada? Wani an iskan kika bawa mutuncinki? Kin cuce mu! Wannan ba ita ce tarbiyyar da mukai maki ba. Kin cuce mu kin cuci kanki. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Ta fa i tana mai rushewa da kuka. Zinah kuwa hankalinta ne yayi mugun tashi jin kalaman da mahaifiyarta ke yi. Cikinta ya bada sautin ulululuuuu. Don sai yanzu lissafin ya fa o mata; lokacin da ta fara bawa Safiyanu kanta, bata jima sosai da kammala al'adarta ba. Kuma tun daga wannan lokacin bata kuma yin wani ba. Kuma a alla yanzu ya kamata tayi jini uku ko biyu. "Na shiga uku ni, Zinatu. Safiyanu ya cuce ni ya gudu ya bar ni!" Wani wawan mari mahaifiyarsu ta auke ta dashi a baki sai da bakin ya fashe. "Don ubanki da baki kai masa kanki ba, har gida zai zo ya miki cikin? Kin cuce mu Zinatu." Wani irin juyawa suka yi duka su hu un suna kallon bakin ofa jikinsu na rawa jin furucin mahaifinsu. "Allah ya tsine maki albarka Zinatu. Allah ya hana ki jin da in duniya. Allah ya aura maki bala'i da tashin hankali a cikin duniyar nan. Allah ya ha a ki da masifa da bala'i. In Sha Allah baza ki ta a ganin haske a rayuwarki ba. Ki tashi ki fitar min a gidana. Na cire ki daga cikin sahun ana. Na yi maki rantsuwa da Allah duk na ara arba dake cikin gidana sai na kashe ki da hannuna. Kije duniya za ta koya maki hankali. Allah ya isa tsakanina da ke gwargwadon ciyar dake da nayi a cikin gidana tun kina tsumma. Abu mafi muhimmanci kuma; kar ki kuskura ki ara amfani da sunana matsayin mahaifinki. Ni ba ubanki bane. Abun kunya ne a gare ni idan har duniya ta san ni ne ubanki. Kije na yafewa duniya ke!" Wani irin kuka Maryama, Sa'adatu da mahaifiyarsu suka fashe dashi. Da gudu Maryam ta kama afar mahaifinsu tare da fa in, "Abbanmu don girman Allah ka yafe mata. Bakinka a gareta dafi ne." A fusace malam Ayuba ya ce, "Duk wacce ta ara bani ha uri a cikin ku ana in dai akan Zinatu ce, wallahi tallahi ban yafe mata ba. Ke kuma Atine, na ga bakinki rawa yake kina son nemawa arki yafiyata, to ko da wasa kika kuskura kika ro eni, wallahi a bakin aurenki. Kuma yanzu yarinyar nan ta fice min daga gidana." Luuuuuu mahaifiyarsu ta tafi asa ta sume. Maryama da Sa'adatu su kai kanta suna jijjiga. Zinah kuwa tunda ta ame waje aya bata ko motsawa ba sai maganganun mahaifinta da ke mata amsa kuwa a masarrafar jinta. Shuru-shuru mal Ayuba bai ga fitowar Zinah ba. A fusace ya fito daga aki zuciyarsa na masa tu in ba in ciki ya nufi wajen tsohuwar injin ruwa da da yake ni a kamun ya lalace ya finciko bulalan injin ya nufi akinsu Zinah. Zagaye ya gansu sun saka mahaifiyarsu a tsakiya wacce ta zama kamar mutum-mutumi suna kuka. Zinah kuma na daga gefe ta ha a kai da guiwa. Wani irin fa awa ciki yayi ya shiga zubaba mata bulalan ta ko'ina a jininta yana ha awa da shurin cikinta da ko'ina ya samu a jikinta. Tun Zinah na arin karewa har ta mi e ta fita da gudu zani a hannu daga ita sai pant ko underwear babu. Su Maryama da Sa'adatu biye da ita a baya suna kuka babu damar bawa mahaifin nasu ha uri. Har titi mal Ayuba ya bi Zinah yana duka yana zagi tare da tsine mata albarka. Jama'a sun taru sai kallonta ake gata ko zani babu a jikinta. Daga ita sai panta. Kanta babu ankwali. Mutane na jan mal Ayuba suna bashi ha uri tare da nuna masa illar abunda yake aikatawa amma sai idanunsa sun rufe ya i sauraran kowa. Wani irin tsanarsa tare da takaicin kasancewarta arta ya dira cikin zuciyarta. A hankali ta du a ta auki zaninta da Maryama dake kuka a kwar gida ta ba wani yaro ya cillo mata. Sai da ta aura zanin jikinta sannan ta taka ta isa har gaban malam Ayuba da wani abokinsa Malam Ussaini ya samu nasarar ri e sa ta ce, "Billahil lazhi la'ilaha'illahuwa sai na zame maka bala'i. Kuma wannan sunan naka da kake matu auna sai na yi yaga-yaga da su. Sai na zama wata tantiriyar a a duniyar nan kuma duk inda na je sai nuna kai ne wanda ya kwanta da mahaifiyata har ta samu cikina. Karuwanci kuma yanzu na fara, malam Ayuba. Mu zuba ni da kai!" Tana gama fa in haka ta juya ta soma tafiya ba tare da ta waiwayi baya ba. Zina daga nan bata zarce ko ina ba sai gidan karuwai da yayi aurin suna dake nan jihar Bauchi. Kai tsaye ta samu jagora har wajen magajiyar gidan. Tana isa gabanta ta zube tare da aura kanta a cinyar magajiyar ta dunga rera kuka. Magajiya bata ce mata komai ba kuma bata hana ta kukan ba. Sai da tayi mai isarta sannan magajiyar ta kama hannunta ta kai ta akinta ta zaunar da ita tare da gabatar mata da abinci da ruwa. Bayan ta gama ci ta bata ruwan wanka ta je tayi sannan ta dawo ta kwanta saboda zazza in da ya rufe ta. Cikin daren ranar Zinah ta soma wani azababben ciwon ciki mai tsanani wanda ya haifar mata da zubewar cikin dake jikinta. Sam ba haka Zinah taso ba. So tayi ta haife cikin sannan ta koma gida ta nunawa mahaifinta jikansa ko jikarta da ta haifa silar karuwanci. Magajiya haka ta cigaba da kula da Zinah ba tare da ta tambayeta abunda ya baro ta daga gida har ta zo nan ba, duk da tana ji a jikinta silar cikin da Zinah tayi arinsa ne dalili domin kaso casa'in na nuna cikin shege ne. Sai bayan sati uku, lokacin Zinah ta gama warwarewa gaba aya. Magajiya ta same ta har aki ta tambayeta labarinta. Zinah bata oye mata komai ba daga cikin labarinta. Sai ma arin bayani da tayi mata na cewar so take ta zama shahararriyar karuwa. Sunanta ya buga tambari a lungu da sa o na garin Bauchi.