Sashe 34
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata ga zuwansa ba sai maganarsa. Ba tare da ta ce masa uffan ba ta nufi direction in da ya fa a mata don ta san Sabo da kazan ne zai ce ya jira ta a waje. Mur a handle ofar ta yi sannan ta shiga kasancewar a bu e ya ke. Zaune ta same shi a tsakiyar gado daga shi sai short yana amsa waya. Alama ya mata da ta taho garesa. Babu musu ta nufe sa sai dai bata fahimtar abu aya da yake fa i saboda wani yare ya ke yi wanda ita bata ta a jinsa ba. Kamar ta wanka masa mari a fuska haka ta ji lokacin da ya jawo ta sosai zuwa jikinsa yana shinshinar wuyanta duk da waya ce a kunnansa. Magana ce da ta auke sa kusan rabin awa sannan ya gama tare da ajiye wayar yana kallonta. "Zeenah, what's wrong na ga duk kin koma wata tsohuwa duk wanann kwalliyar babu shi?" Kamar tana jira ta rushe da wani irin kuka sosai tana fa in, "Na shiga uku ya auke min farin cikina!" Zaune sosai ya tashi tare da kai hannu ya shafa irjinta duka biyun don shi a tunaninsa ko masu kwashe mamuka da asiri ne suka tafi mata da su, amma da yaji duk suna nan sai cewa ya yi, "Ban gane ba? Gabanki aka shafe ko mai?" Girgiza kai Laushi ta yi tare da fa in, "Yasaar ne!" Wani irin ura mata idanu ya yi yana wani tunani cikin zuciyarsa. Can ya ce, "Ban gane Yasaar ba! Mai Yasaar in ya yi? Shi da ya ke cikin Prison." "Meema ya sace. Tana wajensa yanzu haka. Kuma ya ce idan na saki na fa awa an sanda sai ya yi gunduwa-gunduwa da ita ya turo min da part-part in jikinta." Wannan karon saukowa ya yi daga kan gadon tare da fa in, "Wannan shirmen banza da wofi ne! Ta yaya mutumin da ke kulle a prison zai iya yin hakan?" Laushi ita ma mi ewa ta yi tare da fa in, "Wallahi, tallahi shine! Don mun yi waya da shi. Kuma Yasaar yana da manya sosai a garin nan. Ko su za su iya taimaka masa. Na san wasu daga cikin sirrikun Yasaar sosai. Idan na fa a maka sunan manyan mutanan da yake wa aiki a garin nan, za ka sha mamaki. Abunda ya sa ban ta a cewa komai ba ko kuma in fallasa asirinsu, saboda babu ruwana don ba da su ne ke fa a ma, da Yasaar na ke yi. Shi in ma wula antanin da ya yi ne ya saka na rama gwargwadon abunda ya min. Amma ni ba ruwana da tonawa iyayan gidansa asiri." "Wannan dalilin ya sa kike raye har yanzu!" Fa in Sabo da kaza cikin zuciya sai dai maganar zuciyar ta fito fili don da sauri Laushi ta ce, "Mai ka ce? Ban gane ba". Ta fa i hakane tana kallonsa. "Eh mana! Shuru da bakin da kika yi ne ya saka ubannin gidansa ba su au mataki a kanki ba. Da kin sake kin kira sunansu ko arin tona masu asiri, to yanzu haka zancen wata ake ba ke ba. Tuni za su saka a kashe ki kuma a cikin na kusa da ke zai aikata hakan. Ai ba sa wasa da sirrinsu ko ka an," fa in Sabo da kaza. "To ni mai zai kai ni wannan aikin. Ni dai don girman Allah na san kana da hanyoyin da za ka taimaka wajen ku utomin da ata kwalli aya. Ka taimaka min don girma Allah." "Tun yaushe Yasaar ya soma kiran ki?" Ya jefa mata tamabaya. Nan ta bashi labarin komai har zuwa yaron da ya turo da hotuna da kuma kiran da ya mata last. Masifa ya hau ta dashi sosai a kan mai yasa tun lokacin da Yasaar in ya kira ta ranar farko bata fa a masa. "Da tun lokacin kika fa a min, wallahi da ba zai sake yun urin kiranki na biyu ba balle ya yi wannan anyen aikin. Amma yanzu ba bata aci ba, zai ci ubansa. Ban hotunan da ya aiko da su." Ya fa i rai a ace. Da sauri ta auki hotunan da ta aje a kan gadon ta mi a masa. Sai da ya gama arewa hotunan kallo sannan ya ajiye a kan gadon bayan ya yi kwafa tare da saka kaya sannan a auki hotunan ya saka cikin aljihun shaddar jikinsa sannan ya kalli Laushi tare da fa in, "Muje na sauke ki a gida, Meema yau a gida za ta kwana ki kwantar da hankalinki." A take ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi sai ta mi e ta bi bayansa. A baya duk suka zauna ita da shi a cikin mota. Fuskan nan na shi a matu aure har suka isa ofar gate in gidan Laushi. "Ki je ki kwantar da hankalinki. Na tabbatar miki Meema gida za ta kwana. Kuma ina fatan babu Saurayinki cikin gidan don a nan zan kwana duk dare," ya fa i yana kallonta. a masa kai ta yi tare da bu e murfin motar ta fita, Yahuza ya ja motar. "M.S.P.K (Maximum Security Prison, KiriKiri, Lagos State.)" Abunda sabo da kaza ya fa i kenan yana danna wayarsa. Shi kuma Yahuza na jin haka ya dau i hanyar Prison in. 54mimutes ya kawo su Prison in. "Ka jira ni a mota!" Fa in Sabo da kaza tare da bu e murfin motar ya fita ya doshi Prison in. A ofar gate suka ha u da wani jami'in gidan mai babban mu ami sannan suka shiga ciki a tare. Tafiya suke yi suna shiga lungu-lungu kamun suka iso wani waje kamar kogo amma a bakin kogon gate ne mai atuwar kwa una a jiki. ewa jami'in ya yi da key in da ke hannunsa sannan ya shiga, Sabo da kaza biye da shi a baya. Su takwas ne zaune, ko wanne sanye da riga kalar sararin samaniya, ko wanne da Number insa a jiki. Kati suke bugawa. Sai dai tun lokacin da suka ka fahimci ana arin bu ewa suka dakata tare da zubawa wajen idanu. Yasaar na arba da Sabo da kaza, ya mi e da sauri jikinsa na ari. A fusace Sabo da kaza ya arisa ya dunga auke fuskansa da maruka hagu da dama. Sai da ya masa maruka shida sannan ya nuna sa da yatsa tare da fa "Ban ta a sanin da ancin naka ya kai har haka ba sai yau! Ko ka san kuwa saboda ni har yanzu ka kasance da rai a jikinta? Da naga dama da tun lokacin da aka kama ka a airport zan saka a auke min kanka da alburushi. Wato ka raina dabarata da wayau na shiyasa kake aukar matakin da zai kai ka ya baro ko? Mai kake ci na baka ke zuba?" A fusace Sabo da kaza ke maganar. irjin Yasaar in ya bubbuga tare da fa in, "Saura iris, Zeenah ta zo hannunka. Daga wannan lokacin babu wanda ya isa ya dakatar da kai akan fansanka. Ni nan Junaidu inkiya Sabo da kaza, na tsaya maka. Kar kai arin ata rawarka da tsalle. Bar ni na yi amfani da ita na wannan lokacin kamun na ka turn in ya zo. Kar ka kuma aikata irin wannan sakarcin. Ka saka a mayar da yarinyar!" Yana gama fa in haka ya juya ya kalli jami'in da suka shigo tare ya ce, "Daga yau kar a sake bashi waya har sai idan ni na bu aci hakan," yana gama fa in haka ya fice jami'in ya bishi a baya. Sai da ya kulle ofar sannan ya bi bayan Sabo da kaza. Sai da ya rako shi har mota sannan ya le a ta window tare da fa in, "Yalla ai ya za ayi da wannan budurwar ta gida da ka ce a ajiye maka?" Wani kallo sabo da kaza ya yiwa jami'in tare da yin murmushi sannan ya ce, "Sabo da kaza......." Dariya jami'in ya yi tare da fa in, "Bai hana a yanka ta! An gama yalla ai. Yau sai dai uwarta ta haifi wani tunda ka gama cin moriyarta." "Shiyasa na ke son aiki da kai, Labaran. Sa a zai biyo ka har gida." Fa in Sabo da kaza. Sara masa jami'in ya yi tare da aga masa hannu yana murmushi har motarsu ta bar wajen. _Bayan awa biyu_ Wayar Laushi ce ta yi ara alamar shigowar sa o. Da sauri ta kai hannu kuma dama jigum suka yi su ukun suna jiran ta inda Meema za ta shigo. o ne daga oyayyiyar Number kuma na san Yasaar ne. Wallahi tsoron bu ewa na ke yi." Laushi ta fa Ladi Katifa ce ta amshi wayar don hannun Laushi sai rawa ya ke. _Tsiyarki na ofar gida a ajiye, amma ki sani wallahi Yasaar ba zai ta a kyale ki ba sai ya mayar dake abun kwatance_ "Meema na ofar gida!" Ladi ta fa i tare da yin hanyar waje da sauri, Laushi da Salma nice suka rufa mata baya. Curko-curko suka yi ganin atuwar akwati a ajiye a ofar gate ta cikin gida. Dukkansu babu wanda irjinsa bai dukan tara-tara. Laushi jikinta babu inda bai rawa sai kallon akwatin take. Ladi Katifa ce ta yi arfin halin tsugunawa ta soma zage zip in har ta bu e gaba aya. Wani irin ja baya ta yi ganin Meema tsirara cikin jini kuma babu numfashi. Daga tsayen nan Laushi ta kife kif a asa sumamma. (Jama'a ashe sabo da kaza munafiki ne! #Sabo da Kaza #Yasaar #Laushi #Meema #Jami'i Labaran #M.S.P.K #My Destiny #Matar Sayyadee 08128755583 [2/20, 9:56 PM] Rahamanatu: *_MY DESTINY_* ( ~ addarata~) *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION* ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*) Takenmu shine unkasa cigaban adabi! _We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them._ Page 23 *For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* https://chat.whatsapp.com/J1oXseCghhuB6mMFTnFRn7 *_Don girman Allah zan sake fa i, masu