Sashe 98
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan alƙawurra da Udodiri yai ta yi na cewa zai kaita birni sannan ya kai 'ya'yanta karatu ƙasar waje sun bi ruwa hakan ya sa Uloma ta fara nadama tun lokacin, ta ba da rayuwar ta wa Christ tana neman yafiyar sa. Jiya kuwa da Pastor Emmanuel ya mu su wani wa'azi hakan ya ƙara tsoratata har ta yanke hukuncin sanar da Mommy komai. Lokacin da Aka fara case ɗin Udodiri ya zo ya ba ta dubu ɗari akan ka da ta kuskura ta faɗi abinda ta sani ko kuma hakan yai sanadiyyar kashe 'ya'yan ta. Amma tana son shiga heaven gara kawai ta tona asirin komai saboda Jesus ya yafe ma ta gaba ɗaya, kuma ta yadda Jesus zai cececi 'ya'yan ta daga tuggun Udodiri.
Sai da ta mu su alƙawarin za ta zo a matsayin shaida kafin su ka bar gidan.
Suna shiga Mota Zaytoonah ta turawa Justice recording ɗin da ta yi. Lokacin da su ke hanya ne ta ga text ɗin Justice ya shigo wayar ta, tana buɗewa taga umurni ne ya ke ma ta akan ta recording hiran su da Aunty Uloma. Cikin zuciyarta ta dinga jinjina ƙasaita irin ta Justice, wato maganar ta ma sa nauyi sai dai yai text.
Har su ka koma Mommy ba ta yi magana ba, jikin ta yayi sanyi da abubuwan da ta ji. Ta daɗe da sanin cewa Udodiri ne ya kashe Iyayen ta amma yau da aka kuma tabbatar da komai da kuma yadda abun ya faru ta girgiza sosai. Ace akan dukiya ƙani zai hallaka yayan sa, duniya kenan.
Washegari Monday Justice ya shirya ya koma Abuja bayan sun sake tattaunawa akan yadda suke ƙara samun evidences akan case ɗin.
***
"Ikon Allah, yanzu Abu Razz kuma yare zai É—auko, Hajiya kuma kuka zuba ido"
Hajia Ghazala ta yi maganar cike da damuwan jin bayanan Hajia Abu.
"To ya za mu yi tunda shi dai ba yaro ba ne ya san abinda ya kamata amma ya biyewa shirirtar Ni'ima"
"Ni fa yaran nan na ke tausayawa idan ba haka ba da bazan damu da ko waye zai aura ba. Gashi yarinyar ba wani kamun kai gareta ba, yadda kika san ba musulma ba haka take ta shiga cikin maza a office É—in su"
"Maganar fa ta kai wajen Mai Martaba, shi kuma har ya É—au mataki akai maganar da ake ma yanzu an bashi yarinyar. Ina ga ma dalilin da ya sa ya tafi chan garin su kenan dan su sasanta"
Duk wani bayani da ya biyo baya Hajia Ghazala sama-sama ta ke jin sa. Maganar an bawa Justice Mata ya riga ya birkita tunanin ta, amma da ya ke ita É—in gwana ce wajen iya shanye damuwarta shiyasa Hajia Abu ba ta fahimci komai gameda tasirin da maganar yayi a jikin ta ba dan Hajia Ghazala harda yiwa Justice addu'an alkhairi.
Tana barin gidan Hajia Abu numbar Justice ta kira bai ɗauka ba dan haka ta duba lokaci, ƙila yana sallah ta faɗi a ranta tana ƙara alhinin wannan al'amari. Wai Justice zai auri yarinyar da ta gani a office ɗin su ranan. Ta ina ta dace da Justice?. Ta ya za ayi ta rasa Justice a karo na biyu?.
Ƙaddara dai ta riga fata amma da yanzu fa ita ce Matar sa tun asali, Ƙuruciya dangin hauka, ƙuruciya ya sa ta yi wauta da har yau ta ke nadama...
Uba ɗaya su ke da marigayiya Maryam kuma mahaifin su ƙani ya ke a wajen Mai Martaba. Da ke Justice a ƙasar waje yai karatun sa ba ta san shi sosai ba, rabon da ta gan shi ma tun wani hawa da aka yi su ka je kallo lokacin ba za ta wuce shekara shaɗaya zuwa shabiyu ba.
Tana shekara shatakwas yayinda Maryam ke shatara Mahaifiyarta ta ma ta maganar haɗin da Abban su ke son yi da ita da Yunus ɗan Sarki. Kai tsaye ta ƙi saboda soyayyan Alhaji Bashir da ya rufe ma ta ido. Alhaji Bashir yana ɗaya daga cikin ma su Arziƙi da su ke tashe a lokacin, matar sa ɗaya a lokacin da 'ya'ya biyu.
Tunanin Yunus ma irin halin Yayan sa ya ɗauko na neman Mata da shan giya ya ƙara sawa ta yi fatali da zancen auren Yunus. Maryam an yi ma ta baiko da wani ɗan uwanta ta wajen Uwa amma ya rasu sakamakon haɗarin Mota, hakan ya sa ta ce karatu za ta cigaba ba za ta yi aure a kusa ba.
Da Abba yai wa Ghazala maganar sai ta yi biris ta nuna indai aka takura ma ta za ta kira Mai Martaba ta ce ba ta son auren kuma ta san ba zai ma ta dole ba. Abban su ya ji haushi sosai amma ya ƙyaleta da zaɓin ta inda aka juya maganar zuwa wajen Maryam. Dama saboda Ghazalar ce ke kula samari ya sa yai niyyar haɗasu da Yunus tunda Mai Martaba ya ma sa maganar a nema ma sa mata kafin ya koma ƙaro karatun da ya ce zai yi.
Ranan da Yunus ya zo gidan dan su sasanta da Maryam ne Ghazala ta je ganin Yunus É—in dan ta yi gulma kasancewa ba wani jituwa su ke da Maryam É—in ba sosai.
Kuka sosai Ghazala ta yi da ta shiga É—aki bayan ta ga Yunus. Kyakyawan saurayi mai kwarjini da kamala. Ashe shine Yarima Zannoon da ake ta labari cewa yana da kamun kai nitsuwa ga uwa uba Ilimi.
Lokacin da ta yi wa Umma maganar akan ta amince za ta auri Yunus Umma faɗa ta yi ma ta dan tun kafin a karɓi kuɗin Aurenta a wajen Alhaji Bashir aka ma ta maganar Yunus amma ta ce ba ta so.
A lokacin duk wani soyayyar da ta ke ganin tana yiwa Alhaji Bashir sai ta nemeshi ta rasa, soyayyar Yunus ne ya mata mugun kamu ya mamaye ilahirin zuciyar ta.
Tun tana dana sani a fakaice hatta zo tana bayyana Hassadar ta a fili. Da labari ya kai wajen Abba ne ya sa ya matso da bikin ta kusa. Maimakon wata biyu da aka saka da sai aka dawo da shi sati uku.
Bikin dai kamar ba za ayi ba haka dai aka samu aka yi auren Ghazala da angonta Alhaji Bashir. Bayan wata biyar ma tukunna aka yi auren Maryam da Yunus...
***
Su Mommy na komawa Calabar da kwana biyu aka kira su akan Anty Uloma ta mutu. Ba mamaki ba ne kasancewa bayan tafiyar na sun Anty Uloma ta bugo akan Udodiri ya zo yana ƙara ma ta kashedi akan ta yi shiru da bakin ta ko kuma jikin ta ya gaya ma ta.
Æarayi ne su ka shiga gidan ta su ka kasheta bayan sun yi sata amma ga mai hankali ya san akwai lauje acikin naÉ—i.
Thank God suna da recording ba dan haka ba da sun rasa vital evidence, duk da testifying da za ta yi zai wadatar fiye da audio É—in amma duk da haka audio É—in ma shaida ce...
Sati ɗaya da tafiyar Justice suma su ka dawo Zaria. A ranan da su ka dawo ne su ka samu saƙo daga Ringim wai Mommy ta je idan ta samu lokaci.
Mommy ta tambayi Auwal da ya ba da saƙon ko ya san dalilin neman ta da ake yi amma ya ce bai sani ba. Yanayin da ya ke yi tun dawowar su ya sa ta lura akwai wata matsala a ƙasa.
Waya ta ke yi da Justice tana bashi update akan maganar appeal da su ka yi wanda za a fara sauraron ƙaran nan da sati uku a Nigerian court of appeal da ke Abuja. Auwal ne ya shigo da sallama ya samu waje ya zauna yana satar kallon Zaytoonah da ke faman waya fiskarta ɗauke da murmushi. Yanayin maganar da ta ke yi ne ya sa ya fahimci da wanda ta ke magana.
Yau Mommy ta tafi Ringim kuma ya san idan ta je chan za ta ji koma minene aka shiryawa Zaytoonan ba tareda sanin ta ba.
Ba zai iya haƙura da Zaytoonah ba a karo na biyu, indai ta amince da soyayyar sa to dai dole Justice ya haƙura duk da kasancewar ya riga ya turo magabatan sa.
Kusan minti shida kafin ta gama wayar ta ajiye wayar gefe tana faÉ—in. "Ya Auwal idon ka kenan, tunda mu ka dawo fa sau É—aya na gan ka"
"Idan kina son ganina kirana za ki yi ai sai na zo"
"Ba wani ai da da ƙafar ka kake zuwa ka neme ni" ta yi maganar tana haɗe rai
"Ban samu amsar tambayata ba har yanzu Zaytoonah. Ko kuma dai zaɓin da su Baffah su ka miki shine dai-dai a wajen ki?"
Zaro ido ta yi jin kalaman Auwal. Itafa ranan da su ke chatting ya ma ta wannan tambayar ta É—auka wasa ya ke yi shiyasa ta manta da maganar ma.
*"ina so ki bani dama na zamo Uba a wajen Hashir da Hadid. Ina so ki bani dama na kasance tareda ku har iya ƙarshen rayuwa ta, Ina so ki bani dama na nuna miki soyayya da kulawa"*
Saƙon da ya tura ma ta kenan ranan da su ke chatting ta ke tambayar sa gameda rigimar 'yan biyun ta.
Emoji É—in dariya ta tura ma sa sannan ta sauka, daga baya kuwa da ta hau ko da ya kawo zancen sai ta ce ba ta son irin wannan wasan.
"Ina son ki Zaytoonah" maganar sa ta dawo da ita daga tunanin da ta ke yi.
" tun ban san minene so ba, na rasa ki a karo na farko ba na fatan rasa ki a wannan lokaci"
"Ya Auwal please..."
"Ba zan tursasa miki ba, amma dan Allah ki saurari abinda zuciyar ki ke so "
"Ya Auwal akwai abubuwa dayawa akai na kuma..."
"Please Zaytoonah" yanayin maganar na sa ya ba ta tausayi. A matsayin Yaya ta ɗauke shi tun da kuma har yanzun nan hakan ta ke. Auwal Yayan ta ne, duk da akwai aure tsakanin su amma ba ta taɓa sawa a ran ta maganar soyayya za ta shiga tsakanin ta da shi ba balle aure.