← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 161

Sashe 68

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A darare Maman Abdul ta gaida Maryam sannan ta tambayeta labarin Zaytoonah. Maryam ta ce tana lafiya.

Maman Abdul ta yi shiru tana tunani kafin daga baya ta ce " wani hoto aka turo a wani group kuma sai na ke ganin kamar hoton Zaytoonah na gani amma zan turo miki sai ki duba"

Maryam ta ce " ikon Allah".

Hoton da ta turo ma ta ne ya sa numfashin Maryam sarƙewa. Ta dafa ƙirjinta tana maimaita Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. A lokacin mantawa ta yi da cewa sun yi waya da Zaytoonah shekaranjiya har ta ke ce ma ta sun chanja gida.
Da ƙyar ta lallaɓa ta saurari voicenote ɗin tana ji tana girgiza kai saboda rashin yarda da abinda ake faɗa a ciki.
Numbar Zaytoonah ta lalubo da sauri ta shiga kira sai dai ba a É—auka ba nan hankalinta ya sake tashi. Ta kira yafi sau biyar amma ba a É—auka ba jikinta na rawa ta shiga neman numbar Zuhayr sai dai shima É—in shiru ba a É—auka ba.

Hijabi ta É—auka da Key É—in mota tayi hanyar waje dan gidan Alhaji Iliyasu ta ke da niyyar zuwa. Sai Allah ya sa Zaytoonah ta kira ta.

"Hello Mommy"

Jin muryar 'yar ta ta ya sa ta ji wani sanyi ya shigeta. "Adaeze akwai abinda ke faruwa ne da ban sani ba?"

"Kamar me Mommy?"

"Yanzu dai mu yi video call ina son ganin ki"

Daga haka Mommy ta samu waje ta zauna a falo ta buÉ—e data É—inta.

Ganin Zaytoonah sanye da bathrobe ya sa ta sami kwanciyar hankali. Ta shiga gaya ma ta labarin hoton da aka turo da kuma abunda ake faÉ—i.
Ba amfanin ɓoyewa tunda komai ya warware dan haka ta fara ba ta labarin abinda ya faru. Mommy sai gashi tana hawaye.

"Yanzu Zaytoonah irin wannan abun ya faru da ke amma ba za ki sanar da ni ba"

"Mommy shiyasa Zuhayr ya ce kar mu gaya miki gashi yanzu har kin fara yin kuka"

Mommy ta goge hawayen da ke fiskanta ta ce "ina Zuhayr É—in?"

"Yana ƙasa idan ya shigo zan kiraki"

Mommy ta ce ta barshi gobe da safe za ta kira shi. Sun jima suna hira gameda abinda ya faru sannan su ka katse wayar.

Zaytoonah tunda Ben ya shigo ta haura sama ba ta sauko ba. Ita dai ta ka sa gaskata abinda Zuhayr ke faɗi wai Ben ya karɓi musulunci.

Tunda su ka dawo gidan tare su ke kwana duk da kuwa babu abinda ke shiga tsakanin su. Bayan sun gama waya da Mommy ta jirashi a ƙalla kusan awa ɗaya da rabi amma bai shigo ba hakan ya sa ta tura littafin da ta ke karantawa gefe ta shige cikin bargo tana tunane-tunane har bacci ya ɗauketa.

Zuhayr kam taɗi su ke da Ben kamar wanda sun jima ba su haɗu ba. Zuhayr was so excited shi kuma Ben wani farinciki ne ya mamayeshi saboda rabon da su zauna su na hira tsakanin su irin haka tun farko-farkon zuwan Zaytoonah. Ƙarshe da Zuhayr ya duba ya ga dare yayi sai ya ce ya kwana a gidan kawai...

Shigowanta kitchen É—in ta samu Chef Green yana haÉ—a mu su breakfast. Ta gaida shi tareda tsayawa gefe dan ta taimaka ma sa da wani abun.
Sai da komai ya kammala ta koma ciki dan ta duba ko Zuhayr ya dawo amma ba ya nan. Lokacin da ta farka baya ɗakin, da ke duk safiya yana fita gudu shiyasa ba ta damu ba ta cigaba da abinda za ta yi. Ta gama shirin makaranta tsaf kafin ta sauko ƙasa dan ta karya hakan yai dai-dai da shigowar Zuhayr da Ben gidan.

"Good morning Sister Inlaw" Ben ya faÉ—a yana murmushi.

Ta yi seƙeƙe tana kallon sa. Wato dai wannan mutumin ba zai dena bibiyar su ba. Ba ta amsa ma sa ba sai ma wajen dining da ta wuce.
Tana zama akan kujera Zuhayr ya ƙariso wajenta.

"Zaytoon ba ki ji Zubayr na gaishe ki ba ne? Yanzu fa É—an uwan ki ne musulmi, treat him nicely please"

"Ba zan iya ba dan ban yarda da shi ba, kuma ba zan taɓa yarda da shi ba"

"Zaytoon..."

"Kuma ka karya Alkawari tunda ka ce min ba zai sake zuwa inda na ke ba amma sai gashi kai da kan ka ka kawoshi gidan nan, har da kwana mana a gida bayan yana da na sa gidan"

"Zaytoon idan akwai lokacin da Zubayr ya fi buƙatana to yanzu ne. Dole ne na taimaka ma sa ta yadda zai saba da yin sallah da wasu abubuwan, musulmi ɗan uwan musulmi ne ko ba haka ba?"

"Hakane" ta faÉ—a tana kau da kan ta gefe ta fara cin abinci. Shima bai kuma cewa komai ba sai ya juya ya tafi.

Cikin zuciyarta ta ce "Allah ka yafeni amma gaskiya ban yarda da musuluncin Ben ba. Ya Allah ka kareni daga sharrin sa"

Da wannan ta samu ta cigaba da cin abinci hankalinta kwance...

Ganin Zaytoonah ba ta son zuwan Ben ne ya sa shi Zuhayr É—in ya koma zuwa wajen Ben. A dole shi yana so ya sabar ma sa da ibada ya kuma nuna ma sa yadda ake basic abubuwa na musulunci. Idan Zuhayr ya fita da safe ba ya dawowa sai chan dare sosai. Daga office za su je masallaci da Ben daga nan su je gidan Sheikh Hassan É—aukan karatu sai su koma gidan Ben inda Zuhayr ke ma sa bitar abinda aka koya ma sa. Ya kan kira Zaytoonah akai-akai ya ji lafiyarta amma yanzu kam haÉ—uwar su sai dare kawai daren ma wani lokaci zai zo ya samu ta yi bacci.

Sau É—aya da Zaytoonah ta yiwa Zuhayr magana akan Ben ya jawo ma ta hadisin musulmi É—an uwan musulmi ne sai ta ja bakinta ta yi shiru tunda dai Ben ya dena zuwa mu su gida matsalarta ta ragu. Sai dai kuma tana missing Zuhayr sosai, É—an wasa da dariya da su ke yi tsakanin su babu shi yanzu. Swimming da ya ce zai koya ma ta ma ya janye, ina ma ta ga idon sa balle ta tuna ma sa da maganar koyon swimming É—in...

Tana fitowa da akwatin ta daga ɗaki ta yi kiciɓis da shi.
"Ina za ki je?" Ya tambaya da mamaki

Ba ta yi zaton zai zo gidan ba tunda bai saba dawowa da yamma haka ba. Ta kauda kai gefe ta ce "gidan su Farha"

"Why"

"Zan fi yin karatu a chan kuma ya fi kusa da school"

"Farha ki ke aure?, Farha ne guardian É—in ki ko..."

"Eh ɗin ita na ke aure tunda kai ma Ben ka ke aure ai. Ka je ka riƙe shi nima zan riƙe kaina. Ai dama ba sona ka ke ba yanzun ma dan ka ga ina da cikine shine ka ke lallaɓani na ƙarya. To zuwa zanyi a cire cikin idan ya so ka ɗauka ka sawa Ben ya haifa ma ka shi"

Ta ƙarisa maganar tana hawaye.

Dafa kafaɗarta yai zai yi magana amma ya rasa mi zai ce ma ta. Chan ya daure ya ce "Ben ɗan uwa na ne Zaytoon. Ko babu musulunci shi ɗan uwa ne a gareni. Idan akwai abinda ya taɓa yi miki please ki yafe ma sa, yanzu shi musulmi ne, kulawar mu ya ke so ba ƙiyayyar mu ba"
Yai shiru yana sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "na yadda na aikata miki babban laifi amma Dan Allah Zaytoon kar ki cire cikin nan. Ina son ganin Baby na, please"

Yadda yai maganar sai jikinta yai sanyi ya ba ta tausayi dan idon sa har wani ja ya koma. Ta faÉ—a ne kawai amma ba abinda zai sa ta cire ciki.

"Please ki min Alƙawarin ba za ki cire ba kin ji?" Ya faɗa yana haɗa hannu biyu alamar magiya.

"Na ji" ta faÉ—a ba tareda ta kalleshi ba.

***

Yau Alhamis daga school ta wuce Asibiti saboda kwana biyun nan ta rasa gane kanta sai ta dinga jin yunwa da wuri kuma ba ta iya cin abincin da yawa. Likitan da ta gani ya ma ta bayanin cewa ba wani abin ta da hankali ba ne duk yana daga cikin signs na early pregnancy amma ya rubuta ma ta magani guda É—aya da za ta sha.
Tareda Farha su ka zo dan haka sai da aka kai Farha gida kafin aka wuce da ita.

A gajiye ta ke dan haka ɗaki ta shiga bayan ta shigo gidan sai dai kuma yadda ɗakin ya chanja ma ta ne ya sa ta buɗe baki. Roses ne akan gado ga kuma candles nan a kunne a ƙurya da ƙuryan ɗakin, wajen ya zama so romantic.

Ta É—au doguwar rigan da ke kan gadon haÉ—eda karanta takardar da ya ke gefen sa.
*Dinner at the sea, 5pm*

Murmushi ta yi tana tunanin wannan salo na yau, ko da ya ke tun maganar da su ka yi shekaranjiya ta ga yanayin sa ya chanja.

Ta shiga banÉ—aki ta yi wanka sannan ta fito ta shafa mai da É—an powder sai kwalli, dama kwalliyarta kenan. Ranan da ta ji karambani shine za ka ga ta É—an goga lipstick shima ba mai yawa ba.

Farar gown ce irin beach gown ɗin nan, Hannun shimi gareshi sannan ta sama ya matse ta amma daga ƙugu zuwa ƙafa a buɗe yake sosai. Cikin kayanta ta ɗauko beach hat ta saka kalar baby pink sannan ta ɗau wani shawl cream color ta rufe kafaɗunta da shi dan idan ta fita haka sanyi za ta ji sosai, gashi saman rigan bai rufe ma ta nonuwa sosai ba.

Wajen da aka kafa bukka inda su ke yawan zama su yi hira nan ta nufa. Ba kowa a wajen amma an shirya kayan abinci a kan table ɗin wajen, ga flowers da candles shima a wajen an ƙawata shi sosai.
Ta duba ta duba ba ta ga kowa ba sai kawai ta zauna ta cigaba da baza ido. Minti biyu ta yi a haka ta ji lallausan hannun sa a idonta.
"Kin makara, minti takwas kika ƙara"

"Tun É—azu na zo ban..." ta tsaya lokacin da ta ji saukar lips É—in sa a wuyanta
Chapter 68 · 0% Book details