Sashe 114
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Suhailah zo mu je na cire mi ki kaya" ta faɗa tana riƙo hannun Suhailan.
"Anty barin je na cire uniform kin ji"
Zaytoonah ta gyaɗa ma ta kai. Sai da su ka kai bakin ƙofa ta ji Raziya ta ce "wa ya ga Anty Buskuɗa" sai kuma ta kwashe da dariya.
*BuskuÉ—a* Zaytoonah ta maimaita sunan a fili.
Tabbas za ta sha fama da yaran nan...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 57
Bismillahir Rahmanir Rahim
*confession*
A ƙaramin table da ke gaban sa ta ajiye ma sa plate ɗin da ta yanka ma sa Kankana da Apple.
"Barka da yammaci"
Ba tareda ya É—ago ba ya ce ma ta "sannu da aiki"
"Daddyn Raziya idan ba matsala inada magana" ta faÉ—a bayan ta zauna.
Ya rufe littafin hannun sa ya kalleta yana faÉ—in "Bismillah"
Sai da ta sauke dogon numfashi kafin ta ce "yau da safe aka kirani, Mrs Haddish ba ta da lafiya, she's seriously ill"
Ta yi shiru tana nazarin yadda za ta faÉ—a ma sa da ba zai ji haushi ba.
"Erm, ta buƙaci ganin 'yan biyu kafin mutuwarta and i was thinking ko za ka bani dama ni da yaran mu tafi Las Vegas cikin satin nan. I Promised Sati ɗaya kawai za mu yi mu dawo tunda yaran na Makaranta"
Ta ƙarisa maganar a hankali. Hutun second biyar ta ɗauka kafin ta cigaba.
"Mrs Haddish Kakar Marigayi ne and..."
Ta yi shiru ganin irin kallon da ya ke ma ta.
Ya É—au fork ya É—ebi Kankana ya kai bakin sa yana taunawa a hankali, bai ce komai ba har sai da ya kusan cinye plate É—in Kankanar kafin ya ajiye fork ya tura plate É—in gefe.
"A duk lokacin da ta buƙaci ganin yaran, za ku iya yin video call, zai wadatar"
"Amma..."
"Idan Allah ya kaimu zuwa lokacin da 'yan biyu su ka samu hutun Makaranta, sai ku je ku gaisheta. Ina ma ta addu'ar samun lafiya"
Wani abu ta ji ya toshe ma ta maƙoshi ya sa ta kasa koda haɗiyar yawu.
Rabonta da Mrs Haddish tun ranan da za ta taho Nigeria bayan ta gama karatunta.
Ko alif ba ta furta ba ta miƙe ta bar ma sa falon. Yayinda shi kuma ya bi bayanta da kallo.
Yinin ranan kamar za ta fashe saboda yadda ta cika ta yi fam da haushin Justice. Daga baya ma kiran Mommy ta yi, ta roƙeta akan ta yiwa Justice magana ya barta ta yi tafiyar. Mommy ta ce ta haƙura kawai ta bi umurnin mijin ta...
***
Zoom meeting su ke da wasu ma'aikata. Ta saka airpiece tana sauraron bayanan Mr Silas da ke bayani.
Falaq ta shigo ɗakin na ta da gudu. Riƙe hannunta ta yi tana faɗin "Anty come"
Zaytoonah ta cire airpiece É—in tana faÉ—in " Miya far..." ba ta ida ba ta jiyo kukan 'ya'yan ta. Da sauri ta tashi ta fita daga É—akin da gudu, Falaq ta bi bayanta.
ÆŠakin 'yan biyu ta shiga dan daga nan ta ke jiyo kukan Yaran.
"Innalillahi! Ghazalah lafiya?"
Ta faɗa da ƙarfi tareda jawo Hashir da ke kuka jikin ta.
"A wani dalilin za ki samin yara a gaba da duka, who gave you the audacity to beat my kids?"
"Ina da hurumin dukan su dan ba za su zo su ɓatawa 'ya'yana tarbiyya ba. Yara ƙanana ba abinda su ka iya sai iskanci"
"Ta nan kuma ki ka ɓullo. To Wallahi aniyarki ta bi ki dan 'ya'yana ba 'yan iska ba ne"
"Eh Lallai! Shiyasa na ga sun cirewa Suhailah wando suna shirin afka ma ta"
"Kar ki ƙara Ghazala. 'Ya'yana ba Jakunan ki ba ne, ko me za su yi a gidan kar ƙi ƙara, dan Wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare a kan ki"
"Ki dai gyara tarbiyyan Yaran ki tunda tun ƙuruciya sun zama kwartaye"
Lafiyayyen mari Zaytoonah ta shararawa Ghazala.
Ghazala ta fusata ta ɗago hannu za ta rama Zaytoonah ta riƙe hannun.
"Kin yi kaÉ—an Wallahi, kin yi kaÉ—an" ta faÉ—a tana zare ido.
Ta yafce ma ta hannun gefe.
Zaytoonah na ƙoƙarin kamo hannun Hadid da ta gani kwance a ƙasa ta ji saukar dundu a tsakiyar bayanta. A fusace ta juyo ta shaƙo wuyan Ghazala da ba ta shiryawa hakan ba. Yadda ta shaƙeta da ƙarfi sai da idon Ghazala ya firfito, sai faman cire hannun Zaytoonah ta ke amma ta kasa, ta ji damƙar manya.
"Hasbunallah! Zaytoon!"
Justice ya faɗa da ƙarfi lokacin da ya shigo ɗakin. Shima ɗin da ƙyar ya samu ya raba Zaytoonah da Ghazala. Ghazala ta yi ƙasa da sauri tana neman numfashi da gaggawa.
"Wani rashin hankali ne wannan?"
"Ka gaya ma ta duk ranan da ta sake taɓa min yara sai na kasheta"
Daga haka ta É—auki Hadid da ke kwance ta ja hannun Hashir su ka bar É—akin.
Sai da ta fita ne ma ya ankara da cewa a gaban duka yaran sa ake wannan katoɓarar. Raziya da Falaq sun yi ido zuru-zuru ita kuma Suhailah kuka kawai ta ke yi.
"Mi ya faru?" Yai tambayar yana kallon Ghazala da har yanzu ba ta gama dawowa hayyacinta ba.
"Ki sameni a ɗaki" ya faɗa tareda ficewa daga ɗakin cikin ɓacin rai.
"Baby are you OK" ta faɗa idonta cike da hawaye. Gashi nan dai idon sa a buɗe amma ya ƙi cewa komai sai numfashi da ya ke fitar wa da sauri-sauri.
"Hadid my love say something. Ahmad please say something" ta faÉ—a tana jijjiga shi
"Mom i want to go to Zaria" ya faÉ—a bayan kusan minti biyu.
"Zaria ko, we'll go to Zaria ka ji. Yau É—in nan ba gobe ba"...
***
"FaÉ—a a cikin gidana Ghazala. Mi ya kawo haka?"
"Ranka shi daɗe ka gafarce ni. Mummunan abinda na gani ne ya sa na ɗau mataki cikin gaggawa,to hakan kuma sai ya ɓatawa Zaytoonah rai har ta kamani da faɗa tana shirin hallakani.
"Muna ƙasa ni da Raziya da Falaq sai na duba banga Suhailah ba sai su ka ce min tana wasa tareda 'yan biyu a ɗaki. Na share zancen mu ka ci gaba da kallo, to da na hau sama zan shiga banɗaki sai na ce barin leƙa dan ban ji ɗuriyar su ba. Abu Razz ka san yadda duniya ta lalace, yara ƙanana sai ka ga suna aikata abubuwan al'ajabi da ban mamaki.
"Ɗaya daga cikin yaran na gani a kan Suhailah, sun ɗage ma ta skirt ɗinta sun cire ma ta wando, dan pant ɗin ma na yashe a ƙasa. Hankalina ya tashi matuƙa shine na ɗau belt ɗin yaran na zane su dukan su biyu. ita kuma daga zuwa ba ta bi bahasi ba sai ta mareni ta kamani da faɗa.
"Ranka shi daɗe Suhailah 'ya ta ce, dole ne hankalina ya tashi idan na ga abinda zai cuce ta. Dan Allah ka yi haƙuri na yanke hukunci cikin gaggawa ba tareda na bari ka zo ba"
Bai ce komai ba ya wuce ya barta a É—akin tana share hawayen munafurci.
ÆŠakin Yaran sa ya shiga dan Raziya ta kaÉ—a kan su sun dawo na su É—akin.
Suhailah na kwance akan gado kan ta na cinyar Raziya da ke lallashinta.
Zuwa yai gadon ya jawo Suhailah jikin sa yana faɗin "my baby wa ya taɓa min ke?, wa ye nan ya isa ya taɓa min pretty Princess ɗina"
Ta lafe jikin sa tana kuka a hankali.
Ganin ba ta ce komai ba ya sa shi barin maganar zuwa lokacin da ta huce. Bai bar É—akin ba sai da ya tabbatar ta dena kuka har ma bacci ya saceta...
Duk wasu kaya ma su mahimmanci na ta ta ke ta kan haÉ—awa. Abu ne ya faru a lokacin da ta ke tsakiyar jin haushin zamanta a gidan, kasancewar Mai gidan ya hanata tafiya Las Vegas, ga kuma wannan tsohuwar Matar ta san ta sa gidan gaba É—aya ya fice ma ta kai.
A bakin ƙofar ɗakin ya ci karo da akwatuna guda biyu Babba da ƙarami.
"Hashir Love ka gama kashin ne?"
"No" ya amsa ma ta daga banÉ—akin.
Hadid na kwance akan gado yayinda ta ke ƙoƙarin saka Laptop ɗinta cikin jaka
"Ina za ki je?" ta ji muryan shi a tsakiyar É—akin.
Ba ta kula shi ba ta cigaba da abinda ta ke yi.
"Adaeze" ya faɗa da ƙarfi.
Ta É—ago ido ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba.
"Magana na ke miki"
"Gidan mu zan je"
Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya ƙarisa wajen da Hadid ya ke kwance.
Ya saka hannu a goshin sa ya ji zafi, da alama akwai zazzaɓi tattare da shi.
ÆŠaukan sa yai cak zai fita da shi daga É—akin Zaytoonah ta tare gaban shi "ba inda za ka kai min shi, tafiya za mu yi"
"Matsa min na wuce" yai maganar fiskarsa É—aure.
Ta É—an ji tsoro amma ta dake ta ce " ba inda zan je sai ka ajiye min É—ana"
"Matsa na ce!" Ba shiri ta matsa ma sa ya fita daga É—akin. ÆŠakin sa ya kai yaron sannan ya É—auko first aid box ya buÉ—e ya fito da paracetamol na ruwa ya ba shi. Sai da ya sha tukunna ya kwantar da shi da kyau jikin sa yana bubbuga bayan sa a hankali.
Shima Hashir da ya fito ya ga babu É—an uwan sa sai ya fice daga É—akin. Zaytoonah na kiran sa amma ko waiwayan ta bai yi ba. Kai tsaye É—akin Justice ya je dan ya ji maganar su lokacin yana banÉ—aki.
Da ya shigo É—akin shima wajen Justice ya je ya kwanta. A hankali ya ke lallashin yaran sai ga shi sun sake jiki sun manta da dukan da Ghazala ta mu su. A fakaice ya tambayi mi ya faru wanda Hashir ya bashi labarin komai.