← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 161

Sashe 44

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe ma dai sai da T J ya tambayi Maryam amma babu ita. Dan haka ya ce Auwal ya kira ma sa Yayan sa a kai wa Goggo zai yi magana da ita.

Auwal ya kira Mahaifin sa ya sanar da shi T J ke son magana da Goggo. Ba a jima ba aka kai wa Goggo wayan. Auwal ya sawa T J a kunne su ka fara magana...

Duk da Goggo na fama da ciwon ƙafa hakan bai hana Goggo zuwa Zaria a ranan ba. Maganganun T J ya tada ma ta hankali musamman ma da ta ji cewa a Asibiti ya ke.

*"Goggo Dan Allah ki faÉ—a min gaskiya, kin san da cewa Mukhtari na son Maryam kafin auren mu?"*

*"Barkindo a ina ka ji wannan maganan?"*

*"Ki faɗa min gaskiya Goggo dan gaskiyar ce za ta ƙwaci Mukhtari a hannuna. Ba zan taɓa yafe ma sa ƙoƙarin ketawa matata haddi da yai ba"*

*"Ya subhanallahi! Barkindo wannan ba maganar waya ba ce. Zan shirya na taho yau yau É—in nan"*...

Kusan ƙarfe uku Goggo ta iso Asibitin wanda Auwal ne ya je ya taho da ita daga park, tare su ka taho da wani jikan ta mai suna Al'amin ɗan Zahra ƙanwar T J.

Ganin T J kwance a gadon Asibiti ya sa jikin Goggo yai sanyi. Ta so ta ƙi faɗa ma sa gaskiya akan sai ya warke za ta faɗa mi shi komai amma ya dage shi a lokacin ya ke son sanin komai dan hankalin sa ba zai taɓa kwanciya ba.

Labarin komai ta bashi tun daga Lokacin da Muntari ya fara yiwa Baffah maganar yana son auren Maryam tun tana Mary Nkirun ta har zuwa rikicin da aka yi har ta kai ga aka É—aura auren Tijjani da Maryam a cikin Fadan Ringim. Ta haÉ—a da cewa tana zargin auren na su da aka yi ne ya sa Muntari barin gida har shekara shabiyar kafin ya dawo.

T J ya sunkuyar da kai yana hawaye yana maimaita Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun saboda ya samu sassauci a zuciyar sa dan har lokacin bai dena jin zafi a zuciyar sa ba.

"Ka yi haƙuri ka da ka ɗaga hankalin ka Dan Allah, zan samu Maryam na ba ta haƙuri"

Ashe dalilin da ya sa Muntari yai wa Maryam kyautar mota lokacin saukanta kenan, saboda bai haƙura da ita ba.
Wani irin so ne wannan ace mace ta auri Yayan ka shekara ishirin da ɗaya amma ka kasa haƙura da ita. Anya kuwa Muntari na da cikakken hankali ?

"Itama Aishatun da ta ke ɗaurewa Muntari gindi zan je na sameta. Har yaushe za ta yi hankali ta yadda da ƙaddara ta bi duniya a sannu?" Muryan Goggo ya katse shi daga tunanin da ya ke yi.

"Goggo dan Allah ki tayani roƙon Maryam, ki roƙeta ko da minti biyu ne ta zo ta duba ni dan na nemi yafiyar ta"

Da wannan maganar su ka rabu da Goggo. Auwal ya raka ta gidan Muntari dan ba ta san gidan ba yayinda Al'amin ya zauna da T J.

Hanne ce ta nunawa Goggo É—akin Iya wacce tunda ta dawo daga Asibiti ta shige É—aki ko abincin rana ba ta ci ba. Da safe da ta shiga duba T J kalma É—aya bai ma ta ba lokacin da ta ke ma sa ya jiki sai hawaye da ya ke yi.
Sai dai ta ƙi gaskiya amma duk cikin 'ya'yan ta Tijjani ke ma ta biyayya ɗari bisa ɗari kuma ba ƙaramin darajata ya ke yi ba. Duk yadda ta ke ja baya da shi baya fushi.

Sai da Goggo ta zauna a kujeran da ke ɗakin sannan ta kalli Iya da ke zaune bakin gado ta ce " a matsayina na 'yar uwar ki zan ba ki shawara Aishatu. Kin san dai Baffah ya rasu ba maganar shekara ɗaya ko biyu ba, kuma duk inda ya ke ina da yaƙinin yana cikin rahamar Ubangiji saboda kyawawan halayen sa da ya rayu da su har mutuwar sa. Aishatu ina miki tuni da cewa inda Baffah ya je ko ba daɗe ko ba juma za mu je muma. Yadda ya ke kwance ƙarƙashin ƙasa muma haka za a rufe mu da ƙasa mu je mu amshi sakamakon ayyukan mu na duniya. Ki shuka alkhairi Aishatu, ki shuka Alkhairi, duniya ba matabbata ba ce. Kuma ina so ki sani yadda Allah ya ce 'ya'yan da mu ka haifa su mana biyayya haka muma ya ce mana 'ya'yan mu amana ne a garemu. Aishatu Allah zai tambayeki amanar 'ya'yan ki, banbanta Muntari da Tijjani da ki ke yi shi ya kawo su ga wannan hali yanzu. Tun farko kin riga kin dasawa Muntari hassadar ɗan uwan sa kuma har yanzu shi ke bibiyar sa. Ki kula da amanar Tijjani da ke hannun ki, dan Allah zai tambayeki, tun yana yaro kike tsangwamar sa saboda ni yanzu kuma ya girma ma ba ki bar shi ba. Ni da Maryam ba mu muka haifi Tijjani ba ke ce kika haifi kayan ki, dan haka duk abinda ya sameshi dalilin mugun halinki ki kuka da kan ki. Zan ƙara jaddada mi ki,Tijjani amana ne a gareki kuma Allah zai tambayeki game da shi. Ita kuma Maryam duk abinda ki ka yi ma ta Allah zai saka ma ta, ina ba ki shawaran ki nemi yafiyar ta ko kuma ku haɗu a gaban Sarkin da ba ya zalinci"

Da wannan ta miƙe ta fita daga ɗakin ta bar Iya zaune jiki yayi laƙwas. Maganganun Goggo sun shigeta sosai...

Lokacin da Auwal ya kira Maryam ya ci sa'a wayan ta a kunne, ba ta É—auka a kiran farko ba sai a na biyu tana sallama kuwa Goggo ta amsa.

"Maryam ki zo gidan ki ina jiran ki"

"Goggo ki yi haƙuri bazan tashi daga office da wuri ba"

"Ba na son musu Maryam, ki zo gida kawai"

Ba yadda ta iya dole ta amince za ta zo É—in. Goggo uwa ce a gareta, ita ce matar da ta ke gani ta manta cewa uwar da ta haifeta ba ta raye.

Kusan ƙarfe biyar sai ga ta a gidan. Su Zaytoonah da Salman na tareda Goggo dan Auwal ya koma Asibiti.
Zaytoonah da Salman ba su san Daddyn su ba lafiya ba dan Auwal ce mu su yai da Daddy da Mommy sun yi tafiya.
Shi ba yaro ba ne, ya fahimci kafin rashin lafiyar T J sun samu matsala da Maryam, ga kuma conversation É—in Goggo da Tijjani da ya saurara É—azu da safe.

Da sallama ta shigo yaran su ka yi kanta da gudu suna ma ta oyoyo. Har da tambayarta ina tsaraban su.
A É—akin Maryam su ka yada zango saboda su samu damar tattaunawa da kyau.

"Maryam Dan Allah ki yi haƙuri. Shehu ya gaya min komai kuma na sani ba a miki adalci ba. Amma Maryam bai kai kiyi watsi da mijinki a lokacin da ya fi buƙatar ki ba."

"Goggo na haƙura da shi, na gaji da matsalar mahaifiyar sa, kowa yai hanyar sa kawai" ta faɗa tana goge hawaye

"Tun da Shehu ya kawo ki wajena ya damƙa mini amanar ki na ɗauke ki a matsayin ɗiyar da na haifa. A matsayina na uwa ina ba ki haƙuri bisa laifuffukan da aka miki tun auren ki da Tijjani har yau. Ba sai na gaya miki Tijjani na son ki ba kema kin fini sanin hakan. Ina so ki san wani abu guda, rabuwar ki da Tijjani babu alkhairi a ciki. Ba za ki samu kwanciyar hankaliba kazalika shima ba zai samu ba. Kin dai san yana da hawan jini kuma na san kin san yanzu ma yana kwance a asibiti, saboda ke ne Maryam saboda ke"

"Goggo..." ta faÉ—a cikin muryan kuka

"Ka da ki sa baƙin ciki ya kashe Tijjani, ki koma gareshi ku cigaba da rufawa kan ku asiri. Shekaru ɗaiɗaiɗai har ishirin ba wasa ba ne, ta ina za ki ma fara raba kan 'ya'yan ki? Wa ki ke da shi da ya fi Tijjani? Waye zai so ki fiye da Tijjani?. Kiyi haƙuri ki cigaba da haƙuri. Ilimi da kyakykyawar zuciya da Tijjani ke da shi shiyasa ya ke takatsantsan da maganar mahaifiyar sa. Ki godewa Allah da ya ba ki miji irin sa, ki cigaba da haƙuri da shi har su rabu da mahaifiyar sa lafiya"

Goggo na magana Maryam na kuka. Duk abinda ta faɗa gaskiya ne. Ba ta da wanda ya fi Tijjani amma Iya Iya Iya. Anya za ta iya cigaba da haƙuri da baƙin cikin Iya?

Haka dai Goggo ta cigaba da yi ma ta nasiha har ta haƙura da zancen rabuwa da za su yi.
BanÉ—aki ta shiga ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga shadda kalar blue wanda ya sha aiki. Ta yafa farin gyale wanda ya ke da duwatsu blue a jiki. Ta É—an yiwa fiskarta kwalliya kaÉ—an har da sa janbaki pink wanda ya amsheta sosai saboda ita fara ce. Yaran ta É—auka su ka wuce Asibiti Goggo ba ta bi su ba.

A hanya ta faɗa mu su Daddy za su je su gaisar ba shi da lafiya. Zaytoonah har da sha alwashin za ta yiwa Auwal rashin mutunci da ya mu su ƙarya.

Sun zo shiga Asibitin su ka hango Hajjo da Auwal suna fitowa da alama Auwal É—in ke son tare ma ta abin hawa.
Bayan sun fito daga mota su ka jira har Auwal ya zo ya same su sannan ya mu su jagora zuwa ɗakin da aka kwantar da T J, suna tafiya Zaytoonah ta ɗira ma sa dundu a baya tana faɗin ladan ƙaryan da ya mu su, za ta ma ƙara ma sa wani dundun Maryam ta hana ta.
Chapter 44 · 0% Book details