← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 161

Sashe 127

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ya fito ɗaure da babban towel a ƙugun sa zama yai bakin gado yana nishi ya ce "duba min fridge a falo akwai goran Zuma ki haɗomin da ruwa mai ɗumi a kofi"

"To gani nan zuwa" ta fice da sauri.

Gidan na su ya yi tsit dan duk sun yi bacci. Atika ma da za ta buɗe mu su ƙofa da su ka iso ta yi bacci dan sai Ghazalar ce ma ta yi amfani da key ɗinta ta buɗe ƙofar.

Tsabar kiɗima falon ƙasa ta je duba Zumar amma babu ta leƙa kitchen kafin ta sake haurawa sama ta duba fridge ɗin falon sa ta ɗauka ta kawo ma sa. Allah Sarki Bawan Allah sanda ta koma ɗakin yana cikin banɗaki yana fama.

Bayan ya fito ta haɗa ma sa ruwan ɗumi da Zuma kamar yadda ya umurta ya ɗauka yana kurɓa a hankali.

"Abu Razz ko Asibiti za mu je ne. Ko na kira Likita?"

"Barin sha wannan É—in idan bai lafa ba sai mu ga mi za a yi"...

Kamar yadda ta saba tashi yau ma É—in hakan ta tashi, bayan ta yi alwala ta zo ta gabatar da raka'atanil fajr ta É—an yi azkar kafin ta wuce É—akin 'yan biyu dan ta tashe su, tunda tare su ke fita sallar Asuba da Galadima.
Sai da ta tabbatar sun yi alwala kafin ta saka mu su jallabiya kafin su ka wuce na ta É—akin dan nan Galadima zai biyo mu su su wuce. Sai dai har aka fara kiran sallah ta biyu har ma aka shiga sallar ba ta ji É—uriyan sa ba, kuma ta san halin sa da wuri ya ke tashi.
Tunani ɗaya ta yi ko dai ba su dawo ba ne daga inda su ka je. Ƙarshe kawai ta ce mu su yau a gida za su yi sallah ,Daddy baya nan...

Wajen ƙarfe bakwai saura Zaytoonah ta fito daga ɗakinta, ta so komawa bacci amma tunawa da ta yi su Galadima ba sa gida ya sa ta ke son ta haɗa abin karyawa da wuri, dan akwai Zoom meeting da za ta yi ƙarfe takwas da wasu ma'aikata.

Isowanta kitchen ta ga Ghazala na faman É—aura tukunya. Tsabar jiya ba ta samu daman bacci ba kayan jikinta na jiyan ne dai ba ta cire ba.
Zaytoonah ta tsaya kasaƙe tana kallon ta. Kenan dai sun kwana a gidan. Kishi ne ya sa ta jin haushin Galadima, shi birthday daɗi ko sallan Asuba bai fita ba.

Bayan ina kwana da ta ce ba ta ƙara cewa uffan ba ta fice a kitchen ɗin. Dama a tsarin su sai Ghazala ta yi breakfast kafin ta karɓi girkin.

Takwas da kwata Hadid ya shigo da gudu yana faÉ—in "Mom Daddy ba shi da lafiya"

"Hadid ina meeting"

Ta faÉ—a lokacin da ta cire earpiece É—aya.

"Mom Doctor zai ma sa allura yanzu"

Tsorata ta yi jin kalaman Hadid ɗin. Ta yi saurin sallama da Ma'aimatan tareda cewa an ɗaga meeting zuwa ƙarfe biyar na yamma agogon Nigeria.

Room slippers ta saka ta fita da sauri. A falo ta tarar da Ghazala da Likita suna magana. Sama-sama ta amsa gaisuwar Likitan ta wuce É—akin Galadima.

Dukka Yaran sun zagayeshi sun yi jugum. Ruwa aka É—aura ma sa Hadid ke cewa allura.

'Amma Ghazala baƙar munafuka ce, shine ba ta gaya min bashida lafiya ba ɗazu' ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta tambayeshi da sauƙi. Abu da gudawa tuni ya wani faɗa idonsa ya shige ciki, saboda ruwan jikinsa da ya tsotse. Jiya da dare da likitan ya zo kusan karfe shabiyu da minti arba'in ya ma sa allura ya kuma sa ma sa ruwa, ya nunawa Ghazala yadda za ta cire idan ya ƙare. Da ake akwai ƙarin leda ɗaya da za a ƙara saka ma sa shine ya zo da safe ya saka ma sa.

Haka dai kwana biyun Zaytoonah ta yi shi cikin jinyar Galadima. Duk da taji tausayin mijin na ta amma hakan bai hanata yin dariyan abinda ya faru ba bayan Galadiman ya samu lafiya. Har tsokanar sa ta yi da cewa hakkinta ne ya kamashi tunda yana da gida ya wuce cin abincin hotel.

***

Ƙoƙarin shirya closet ɗinta ta ke ta ji maganar sa a bayanta "Zaytoon wani irin shirme ne wannan" ya faɗa yana nuna ma ta wayar sa.
Karɓar wayar ta yi tana kallon screen ɗim wajen status ne dai amma ya riga ya goce ba ta san wanne bane ya ke nuna ma ta.

"Sayyidi minene?" ta faɗa tana kallon sa cikin rashin fahimta dan ɓacin rai ƙarara ta kalla akan fiskarsa koma minene ya faru gaskiya ran sa ya ɓaci sosai.

"Ki duba status ɗin ki" da ƙarfi

Yau da safe ta tsokali Ghazala ta tura ma ta video clips na wajen da ta yi rawa ranan birthday É—in Galadima clips ne guda uku ciki harda wajen da ta ke rawa a jikin sa.
Da ke hidimar rashin lafiyar Galadima bai sa ta waiwayi video da aka yi ba sai jiya da dare ta sauke su akan laptop É—inta ta yi editting sannan ta tura a wayanta.
Bayan ta gama turawa Ghazala video ɗin ne ta ɗaura clip na wajen da 'yanbiyu da su Suhailah ke rawa da ɗaya kuma wanda 'yanbiyu ne kaɗai su ka yi rawan tun a ɗaki kafin su sauko ƙasa. Iya video biyun nan kawai ta ɗaura amma ga mamakinta sai ga video na uku na second tara wanda ta ke rawa ita ɗaya. Ba ita ta ɗaura wannan ba infact ɗin time ɗin da aka ɗaura da na farkon akwai tazara wancan da safe ta ɗaura su wannan kuma bai fi awa ɗaya da ɗaurawa ba tana tunanin fitan da ta yi ɗazu ta je ta duba jikin Bahijje shine koma wanene ya samu damar amfani da wayarta har ya ɗaura status ɗin.

"Maza nawa ke da contacts É—in ki? Ba wannan ba, wani mutunci ne a cikin É—aura irin wannan a matsayin status ko da kuwa Mata zalla ne za su gani?"

"Ka yi haƙuri dan Allah amma Wallahi Sayyidi ba ni na ɗaura wannan ba" Zaytoonah ta faɗa kamar za ta yi kuka.

Bai ce komai ba ya juya ya fice daga É—akin.

Da ke girkinta ne da dare maimakon ya ci abincin da ta zuba mu su a falon sa sai ya sauko ƙasa tareda Yaran ya ce Raziya ta zuba ma sa abinci. Ghazala na ganin haka ta sa murmushi.

Lokacin da ta shiga ɗakin sa haƙuri ta shiga ba shi amma bai waiwayeta ba balle ya nuna ya ji mi ta ce.

Tana durƙushe dai-dai ƙafarsa ta sake jarraba ba shi haƙurin.

"Ranka shi daɗe ba ni na ɗaura wannan video ɗin ba. Idan kana so na rantse da Ƙur'ani zan yi, ban san wa ya saka ba"

"Kina nufin Hadid ne ya É—aura ko kuma dai Hashir?. Su ne su ka rubuta *see Galadima's property* really Zaytoon"

Tabbas abinda aka rubuta a ƙasan video ɗin kenan.

Abu biyu ne ya sa shi wannan fushin. Na farko kishi ne na biyu kuma abinda ya sa a ransa shine Zaytoonah ta sa video É—in ne saboda Ghazala.

"Ka yarda da ni Allah Wallahi ba ni ba ne"

"Matsamin zan kwanta"

Ajiyar zuciya ta sauke tareda miƙewa ta bar wajen. Tunda ta kira ma sa Allah bai yarda ba shikenan ya yarda da abinda ya ga dama, Allah ya san ba ita ba ne kuma zai tona asirin munafuki.

Tunda ta san darajar turakar Galadima yau ne rana ta farko da su ka kwanta kowa na fuskantar gefe, dukkan su biyu a gefe gefen gadon su ka kwanta sai ya zama tsakiyar da fili.

Washegari ma sammakal su ka tashi dan Galadima bai sauko ba. Da safiyar kuma sai ga kiran Iya. Ba ta da numbarta ma sai da ta amsa ta gane muryan. Iya ce ta roƙeta akan ta zo gida yau zuwa gobe saboda jibi za a fita da Muntari kuma tana son su gana kafin su tafi. Ce ma ta tayi za ta tambayi Galadima idan ya barta za ta zo.

A take a lokacin ta tura ma sa text amma bai yi reply ba. Sai kusan biyar da rabi kafin reply É—in sa ya shigo *Allah ya kiyaye hanya* kawai ya rubuta.
Ta girgiza kai kawai ta ajiye wayar ta cigaba da abinda ta ke a kitchen.

Da dare ma bai ci abinci tareda ita ba amma wannan karan ita ta serving na shi lokacin da ya ce Raziya ta zuba mishi abinci ita ta yi saurin miƙewa ta fara zubawa.
Da za su kwanta ta sake tuna ma sa maganar tafiya Zaria.

"Na ce Allah ya kiyaye hanya mi kuma kike so?"

"Na gode" ta faÉ—a a hankali.

Tare ta tafi da yaranta da ba za ta iya barwa Ghazala su ba duk da kwana É—aya kawai za ta yi.

A chan Zaria kuwa tun ranan da Auwal ya faɗawa Iya cewa an gama yi mu su Visa tafiyar su ta kama ranan Alhamis ta je ta samu Mommy har gida ta ma ta godiya tareda roƙonta gafara. Mommy ta ce ma ta ta jima da yafe ma ta.

"Maryam na san akwai ciwo amma Dan Allah ki taimaka ki yafewa Muntari, wallahi kullum cikin damuwa ya ke, ki yafe ma sa saboda ya samu ya gama da duniya lafiya" ta ƙarisa maganar tana sheshsheƙar kuka.

"Na riga na yafe ma sa sai dai idan ba Tijjani na gani ba ba zan taɓa iya zuwa inda ya ke ba"

"Da yardar Ubangiji Shehu zai dawo gidan nan da ƙafafuwansa. Na gode da kika yafe ma sa"

Bayan tafiyar Iya Mommy ta jima tana ƙara jinjina lamarin Ubangiji. After all this years sai ga shi Maryam Nkiru Inyamura ita ce Iya ke neman yafiyar ta...

Awa biyu da zuwan su Zaytoonah Iya da Humairah su ka zo gidan.

Abinci ma Zaytoonah ke ci lokacin da su ka shigo. Zaytoonah ta mu su tayin abinci su ka ce a ƙoshe su ke. Bayan ta gama cin abinci ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen ta dawo.
Chapter 127 · 0% Book details