Sashe 5
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ya shigo Iya ke ta masifa. Ta je za ta shiga banÉ—aki ne ta haÉ—u da Nkiru ta fito daga banÉ—akin shine ta fasa shiga ta shiga É—ayan.
"Wai ni kam wacece wannan ne da ta sa Iya ta cikin damuwa haka?"
"Karuwar da Hamma ya kawo mana, ni inaga mayya ce ma dan tun randa ta zo na ke fama da ciwon kai"
Muntari yai dariya ya ce "ikon Allah Hamma Tijjani ne ya kawo karuwa har gida"
Iya ta shiga bashi labarin ƙarya da gaskiya gameda Nkiru, gaba ɗaya sai ya matsu da ya ga wannan yarinyar da ake ta magana.
"Barin je na gaida Goggo" ya faɗa tareda miƙewa tun kafin Iya ta cigaba da ƙorafi...
Wanka ta yi ta saka kaya amma ta kasa motsawa jini ne ya zo mata ta rasa ya zata yi, ba kowa a ɗakin gashi ƙila T J sai dare zai dawo. Tana zaune a ƙasa inda ta shimfiɗa wani zani kar jinin ya ɓata ƙasan duk da ta san zai jima kafin ya ratsa doguwar rigan da ta sa tunda da kaɗan-kaɗan ya ke zuwa ranan farko.
"Salamma Alaikum, Goggojiya ina baƙin na ku" ya faɗi yana kutsa kai cikin ɗakin
"Goggo i..." maganar ya maƙale lokacin da ya hango ta zauna tana yamutsa fiska. Ya buɗe ido baki hanci duk yana kallonta. Fara ce sosai dan zai iya cewa ta fishi fari nesa ba kusa ba. Kai Murjanatu da Talatun Inna Adama ake ganin farin su har yayi yawa amma wannan ta ninka su. Shi ba dan ance ma sa Inyamura ba ce da Baturiya zai kirata. Ga ta ɗan 'yar duma-duma irin matan da ya ke so ba kamar matan su na nan da su ke a bushe ba. Kitson da aka ma ta lokacin da za su yi festival a ƙauye shine a kanta, ya fara tsufa amma bai hanashi ƙasa haskaka fiskan ba. Beads ɗin da aka yi kitson da shi har lokacin suna kan ta.
"Hallo Bentiful woman. Am Muntari, small brother of Tijjani" ya faÉ—a tareda tsugunnawa a gabanta.
Murmushi ta yi saboda jin turancin sa, accent ɗin bahaushe ne ke bakin T J nan ma ba sosai ba amma ya iya turanci, suna full conversation ba wani gargada. Amma wannan kam ba vocabulary ba grammar ba komai, kuma yadda ya dage yana maƙe murya ka ce turanci mai kyau ya ke faɗi.
Murmushin da ta yi ya ƙara fito da dimple ɗin ta wanda hakan ya sake birkita Muntari.
"What is ya name?"
"Mary" ta amsa a taƙaice tunda T J ya ce sunan ta Mary ne Nkiru zai mu su wuyar faɗi. Shi kaɗai ke kiranta da Inkiru.
"Bentiful, me i come for Kano. Small Sister is to marriage tomorrow"
Ta gyaÉ—a ma sa kai tana murmushi, ya sa hannu ya shafa fiskarta yana danna wajen dimple É—in
"Kan bala'i! wannan taushi haka"
"Muntari!" Ya ji an daka ma sa tsawa.
Ita kanta Nkiru sai da ta tsorata.
A fusace ya ƙariso yana huci kamar mayunwacin zaki.
"A wani dalilin za ka taɓa ma ta fiska"
"Hamma kawai"
"Ka shiga taitayinka Mukhtari. Dan ba ta sallah ba shine zai sa ka dinga taɓata yadda ka ke so ba, ba muharramanka ba ce ka kiyaye" ya faɗa kaman zai make Muntari
"Mi ya ke faruwa?" Goggo da ta shigo ta ke tambaya.
"Ba fa abinda na yi Goggo, na ga baƙuwa a ɗakin ne na ke gaisawa da ita"
"Fita a ɗakin nan" ya faɗa da ƙarfi. Muntari ya fice yana tsaki.
Ganin ba shi da niyyar magana ne ya sa Goggo cewa "Allah ya baku haƙuri"
Daga tsaye ya fara yiwa Nkiru faɗa akan ka da ta yarda ta bari wani namiji ya taɓata babu wani ƙwaƙwƙwaran dalili ko da kuwa shi ne. Bai jira mi za ta ce ba ya fice a ɗakin.
Yana shiga ɗakin sa ya kasa zaune ya kasa tsaye, hannun Muntari kawai ya ke gani a fiskar Nkiru. Zuciyarsa tana wani ƙuna. Yarinyar kam akwai ta da wauta ko dan saboda ita ce 'yar fari, amma bai ɗauka wautan ta ya kai har ta tsaya Muntari ya dinga shafa ma ta fiska ba tare da ta buge hannun ba. Wata zuciyar ta ce ma sa " ka ma ta uzuri, addinin ku ba ɗaya ba haka yaren ku ba ɗaya ba ne" sai dai duk da ya tuna da hakan zuciyar sa ba ta yi sanyi ba. Buga ƙofar sa da ake yi ne ya sa shi dai na sintirin da ya ke a ɗakin.
Asma'u ce ta gaya ma sa saƙon Goggo nan da nan ya fice da sauri...
Kuka sosai ta ke yi lokacin da ya shigo.
Tsugunnawa yai a gabanta yana jin wani abu na zungurar shi a zuciya.
"I'm sorry Inkiru" ya faÉ—i da tausashashshiyar murya. Shi kan sa bai san dalilin yi ma ta wannan faÉ—an ba.
Rarrashinta yai ta yi har ta yi shiru. Ganin ta dena kuka ne ya sa shi tashi zai tafi sai ya ji ta kira shi a hankali "Teejay"
Ya kalli idonta wanda ke birkitashi tun haÉ—uwar su.
"I'm i'm" sai ta rasa bakin magana, yadda ya tsareta da ido ya sa ta ji kunyar gaya ma sa abinda ta yi niyya.
"What?" Ya É—aga ma ta gira
"My p p period" ta faÉ—a tareda rufe fiskarta da tafukan hannun ta.
Murmushi yai ya ce bari ya kawo ma ta takarda sai ta rubuta ma sa abinda ta ke buƙata..
*har yanzu fa sharan fage ake a labarin*
*Ga Hamma Tijjani ga kuma Muntari duk idon su ya ƙyasa da Mary-Nkiru*
*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... ......ZAYTOONAH*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat
*Free page*
*2- Igbo girl (Inyamura)*
Bismillahir Rahmanir Rahim
A inda ta ke zaune ta fara gyangyaɗi sai dai buɗe ƙofar ɗakin da aka yi ya fargar da ita ta buɗe ido tana kallon ƙofa cike da tsoro. Wata mata ce ta shigo ɗauke da lantern irin na da wanda ake sawa kerosene. Sai da ta matso kusa da ita kafin Nkiru ta gane waye. Anty Nonye ce wacce ta maida sunan ta Elizabeth, ƙanwar Patrick. Tunda mijinta ya mutu shekaru uku bayan auren su ta dawo gida da zama, kusan shekaru sha shida kenan ba ta sake wani auren ba. Ta maida kan ta wata ƙaramar pastor dan ta maida rayuwarta kwacokam wajen yiwa church ɗin su hidima.
Elizabeth ta sa hannu a bakinta tareda faÉ—in "shshshsh"
Kunce ma ta É—aurin da aka yi ta yi sannan ta ce a hankali "ki biyoni a hankali"
Siɗak-siɗak su ka fito daga ɗakin Elizabeth na riƙe da hannunta su ka fice daga gidan, kasancewar ɗakin yana chan ta baya ne sannan kuma tsakar dare ne kowa yayi bacci dan ana maganar ƙarfe uku na dare.
Sosai su ka yi tafiya kafin su ka kai bakin church ɗin ƙauyen inda wani mutumi ke tsaye a bakin keke yana jiran su.
Elizabeth ta kama hannun Nkiru guda biyu tana faɗin " kin ga iyayen ki da su ka mutu ina da yaƙinin Uncle ɗin ki Udodiri ne ya kashe su kuma ke ma sharri ya miki dan a kashe ki. Dukiyar mahaifin ki ya ke son ƙwacewa, ki bi Antony zai kai ki garin Obowo akwai gidan wani elder na church ɗin mu sai ki zauna a chan idan kin huta zai sa ki a mota ki wuce Calabar, ban san gidan Kakannin ki na chan ba amma na san tunda Patrick ya ce iyayen Caroline ma su kuɗi ne ba za su yi wuyar samu ba. Sai ki tambayi gidan Chief James Asibong" Nkiru ta gyaɗa kai tana hawaye. Ko ba ta faɗa ma ta ba ta san sunan Kakan na ta, tunda maiden name ɗin Mommy shine Caroline Asibong. Ta kuma san Mommy ce 'yar fari a wajen mahaifinta kuma tana da ƙanne biyu maza 'yan biyu.
Elizabeth sai da ta ga sunyi nisa kafin ta bar bakin church É—in tana addu'an Jesus ya sa Nkiru da Anthony su isa garin Obowo lafiya...
Sun fita daga ƙauyen lafiya amma ba su yi wani nisa ba keken Anthony ta yi faci dan haka a ƙafa su ka ci gaba da tafiya Anthony na tura keken ita kuma Nkiru na binshi a gefe. Nkiru tana tafiya ne tana hawaye, yunwa da ishirwa sun ma ta kamun talala amma ba wannan ne damuwarta ba damuwarta shine abinda Uncle Udodiri ya yi.
Kafin su iso garin gaba É—aya ta jigata amma a haka ta dage tana tafiya ba tareda ta nuna gajiyawarta ba.
Ko da su ka je gidan Elder ɗin safiya ta yi sosai sai dai rashin sa'a matar sa ta ce mu su baya gari. Antony ya gayawa matar saƙon Elizabeth akan Nkiru za ta zauna da su na wani lokaci dan haka duk da Elder baya nan zai bar Nkiru a wajenta idan ya dawo sai ta sanar da shi. Matar Elder ta washe baki ta ce ma sa ba komai.
Anthony ya fita dan ya je yai facin tayar keken sa sannan ya wuce ƙauyen su.
Bai fi minti takwas da tafiyar Antony ba matar ta kalli Nkiru da ke zaune tana zazzare idanu ta ce da yaren Igbo " ba zan amince da zaman ki a gidan nan ba saboda na san halin mijina, the last time da aka kawo mace gidan nan ban ji da daÉ—i ba dan haka ki tashi ki kama gaban ki, idan dai Calabar za ki je ga hanya daga nan ba nisa zuwa park za ki samu mota"
Nkiru da ta É—auko kofin silver na ruwa da matar ta kawo mu su za ta kai baki sai ta kafe a wajen hannunta ya fara rawa.