← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 161

Sashe 29

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta gama magana ba wacce ta yi magana. Ita kan ta Iya yadda Maryam ke magana da ƙarfi sai da ta ɗan tsorata.

Daren ranan sai da Zaytoonah ta kwana da zazzaɓi saboda kuka da ta sha.

***

Exams yaran ke yi dan haka da wuri su ke dawowa gida. Yau ma sun jima da dawowa suna ta damunta da rigima ta tura su gidan su Fawaz. Shi kuwa Auwal ya je aski. Ba ta jin daɗi ya sa ta dawo daga office tun ƙarfe shaɗaya na safe. Laulayi ne ta ke wanda ba ta san tana ɗauke da cikin ba sai sati biyu da su ka wuce wanda ya kama satin T J shida da barin ƙasar.
Jin ana buga ƙofa ne ya sa ta tashi daga baccin da ta ɗan farayi.

"Zaytoonah? Salman?" Ta fara kiran sunan yaran amma shiru dan haka ta sa a ranta ba su ba ne.
Doguwar riga ce ajikin ta dan haka gyalensa kawai ta yafa ta fito.

Jin yana ta buga ƙofa ba a amsa ba ne ya sa shi buɗe ƙofan ai kuwa ya ji shi a buɗe. Ba tareda wani shayi ba ya kutsa kai cikin gidan.
Ko'ina tsab-tsab a falon sai ƙanshi ke tashi. Yai murmushi dan ya san Maryam ce da wannan gyaran.

Fitowan da za ta yi a ɗaki ta ga wani guntun mutum a tsakiyar falonta ya ƙurawa hoton su da ke jikin bango ido. Hoto ne da su ka yi duka gidan ranan birthday ɗin Salman na cika shekara huɗu a duniya.

"Malam lafiya za ka shigo min gida ba tareda izinin ma su g..." maganar ta kafe lokacin da mutumin ya juyo.

Shekaru shabiyar rabon da ta sashi a ido , ita tama manta da batun sa. Saɓanin wancan da ta sani da ya ke yaro ɗan ƙauye mai kusan shekaru ishirin, wannan ya ƙara girma da wayewa ga alamun hutu ya ratsa shi.

"MUNTARI!" Ta furta cike da mamaki

"No no no no. Its ALHAJI MUNTARI"

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*10-Zaytoonah*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Maryam renon cikinta ta ke yi hankali kwance, laulayin da ta ke ji ma a hankali ya zo ya tafi. Karatu su ke ba kama hannun yaro dan haka ba ta da lokacin raki. Indai ba so ta ke ta sake maimaita jarrabawarta ba. Ko so ɗaya ba ta yi gigin zuwa gida ba, da Azumi da sallah duk a Abuja ta yi. T J ma duk yadda ya ke so ya ganta kusa da shi haƙura yai dan ya san zaman Abuja ya fi ma ta kwanciyar hankali ga karatu ga renon ciki. Duk weekend yana zuwa ya ganta friday da yamma zuwa Sunday da yamma ya tafi.

Bayan sallar Azumi watarana ta shiga gaisuwa sashen su Landlord É—in ta wanda matar ta dawo daga Umurah.

"Maman biyu" Hajiya Fatima ta faÉ—a tana dariya

"Ni na É—auka zan zo na samu kin sauka"

"Hajiya idan na haihu ai bakwaini kenan"

Hajiya ta yi murmushi ta ce "Allah ya raba lafiya"

Bayan sun gaisa ne ta kawo mata tsaraba ta yi godiya ta tafi.
Cikin tsarabanta akwai gabaruwa da kuma 'ya'yan Zaytoon wanda ke cikin wani kwalba mai kyau.
Ta ji daɗin 'ya'yan Zaitoon ɗin nan dan zuwa washegari a school ta cinyeshi tas. Daga lokacin kuma kamar wacce ta zama addicted to it sai ga shi har komawa ta yi wajen Hajiya Fatima ko akwai ta ƙara ma ta. Unfortunately duk ta rabar amma ta ce ba za a rasa a manyan grocery stores ba.
Daga wannan lokacin ta zama regular customer a wani ƙaton store wanda ta samu suna sai da 'ya'yan zaitoon ɗin. Watarana da ta je siya babu ta haɗe rai sai wata mata a wajen ke cewa "ki ce mun kusa samum Baby Zaitoon ko Zaytoonah" Maryam ta yi dariya ta bar store ɗin da zimmar ta nemi wani wajen ko za ta samu...

Prior to Bar final exams ɗin su sai da ta yi rashin lafiya, karatu ne ba wasa indai tana son cin exams ɗinta ga cikinta da ya shiga wata takwas. Wani weekend da T J ya zo ya ganta ne ya tsorata da ramar da ta yi saboda stress. Saturday ya tafi Ringim ya ɗauko Asma'u wacce ta zama 'yan mata. Tana JSS two kuma alamu sun nuna za ta ƙarisa makaranta dan Goggo na son 'yar jikarta ta yi boko. Suna hutu dan haka ba wata matsala.

Ta ji daɗin zuwan Asma'u dan ko ba komai za ta rinƙa taimaka ma ta da wasu ayyukan sannan kaɗaici ma na daɗa ƙara ma ta damuwa.
Haka dai ta daure ta yi karatun da daÉ—i ba daÉ—i, da ikon Allah kuma da aka fara exams ba ta samu matsala ba dan har ta gama ba ta yi ciwo ba.

Washe garin da ta ƙarisa exams sai ga T J ya zo ɗaukan ta. Ta ce ba inda za ta je ba za ta haihu a Zaria ba, ANC ɗin ta duk a Abuja ta yi dan haka a nan za ta haihu. Duk yadda T J yai da ita ƙi ta yi ta ce ba za ta tafi ba. Shi tsoron barinta ita ɗaya ya ke yi a wajen ga shi Asma'u ta koma makaranta. Ita kuma zama da Iya ne ba ta so musamman at this condition da ta ke ciki.
Ganin ta ƙi yarda ne ya sa dole ya haƙura ya bi son ranta amma ya ce da ta ji wani ciwo ta aikawa su Hajiya Fatima ta amsa ma sa da za ta yi hakan.

Washe garin ranan da ya tafi da ta kama Monday ta tashi da naƙuda ta daure ta shiga cikin gida ta sanar da Hajiya Fatima.
Hajiya ta shirya ta sa Dreba ya wuce da su Asibitin da Maryam É—in ke awu.
Haihuwa zai zo ba zai zo ba tun ƙarfe shaɗaya na safe har bayan Isha, kusan ƙarfe tara da minti shida na dare tukunna ta sauka, ƙatuwar Baby Girl ta fito duniya.

Ba ƙaramin galabaita Maryam ta yi ba kafin ta haihu, saboda baby ɗin ma da girmanta sai da aka ɗan farka ta kafin kan baby ya fito. Maryam ta ga Bone kam, ashe haihuwa ba sauƙi.

Zuwa goman dare an shirya baby an gyara uwarta. Hajiya Fatima ce ta tsayawa Maryam, daga gidan ta aka kawo mu su komai. Duk da babu wata matsala amma ance gara Maryam ta kwana ta huta tukunna kafin a sallame su dan haka a Asibitin su ka kwana. Hajiya ta yiwa Maryam kawaici dan ko da mai aikinta ta zo akan ta bari ta kwana da Maryam ɗin ƙi ta yi ta ce ta je ba matsala.
Washe gari da safe ƙarfe tara da rabi na safe aka sallamesu su ka wuce gida. Baby kam tana cikin ƙoshin lafiya sai bacci da cin abinci da kuma kuka.

Da su ka dawo ne Maryam ta yi amfani da wayan landline ɗin Hajiya ta kira office ɗin su T J baya ma Office ɗin colleage ɗin shi ne ya ɗauka. Ta bar mi shi saƙo akan a sanar da shi ta sauka lafiya.

T J na dawowa da aka sanar da shi ya kama tsallen murna haka ya tattare ya koma gida. Cike da farin ciki ya sanar da Iya cewa Maryam ta haihu.
Buɗan bakin Iya sai ta ce "an dai ɓata mana zuriya"
T J ya cizi leɓensa na ƙasa yana jin zafin kalaman Iya.

Da yamma ya isa gidan inda Maryam ta koma sashin su Hajiya saboda Hajiyan da ta nemi ta dawo wajen ta.
Ya É—au Baby wacce ke baccinta hankali kwance.

"Wakey-Wakey Princess, Daddy is here"

Yana maganar yana shafa fiskarta da babban yatsar sa.

Maryam ta ƙura ma sa ido tana murmushi.

Ya É—ago ido ya kalli Maryam ya ce "Dama na gaya mi ki Princess ce"

"Sannu Daddyn Princess"

"Allah ya raya mana ita da Imani"

Maryam ta amsa da Amin.

Ya rankwafo ya kissing goshin Maryam ya ce " na gode da wannan kyauta"

Ta tunkuÉ—e shi ta ce "dole ka ce ka gode tunda kana chan kana hutawa ka barni da wahala"

"Sorry My Queen kin san da akwai yadda za ayi na maida ciwon jikina da zanyi. Tunda ki ka yi nauyi Dear ban taɓa samun kwanciyar hankali ba sai yau. Ke ma kin sani"

"A hakan the last time da ka zo sai da ka yi..."

"Sai da na yi me?"

Ta É—an ja kumatunsa yai dariya ya ce " Maryam kin san idan kina kusa da ni tamkar magnet na ke komawa, idan ban ji ki a jikina ba na jin daÉ—i"

"Sorry Mr Magnet ni da kai sai bayan shekara biyu idan na yaye Adaeze"

"Adaeze?"

"Princess" Maryam ta amsa ma sa

"Wani suna ya kamata mu sawa Adaeze, the last time da mu ka yi maganan kince na bari ki haihu lafiya tukunna"

"You decide"

"No we decide"

"Duk abinda ka sa ma ta ni dai zan kirata da ZAYTOONAH"

"Zan ba ta labarin yadda ki ka yi ta yawon neman 'ya'yan zaitoon kwararokwararo-lungu lungu"

Sun tsaida magana akan za a yiwa Iya takwara amma za su dinga kiranta da Zaytoonah. Duk yadda ta so ta kauce zuwa Zaria a ranan bai yiwu ba dan shatan mota ya É—auko su ka wuce Zaria bayan sun yi wa su Hajiya Fatima sallama.

Takwas na dare ta É—an wuce kaÉ—an su ka isa gida, su na shiga kaman yadda ya saba ganin su hakan ce ta faru domin kallo su ke yi dukkan su biyu ga falon nan kaca-kaca, sun ci abinci amma ba su tattare kwanukan ba.

Maryam ta daure ta ce "Barka da dare"
Chapter 29 · 0% Book details