← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 161

Sashe 51

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Subbuhun Quddusun Rabbil Mala'ikati War Rooh. Rabirhamhuma kama Rabbayani Sagira. Ya Mujibussalihina, Ya Malakul Mulk" haka tai ta ɓuruntun addu'o'i kala-kala har sai da jirgi ya dai-dai ta a sararin samaniya tukunna ta yi ajiyar zuciya ta buɗe ido, juyawar da za ta yi ta sauke su kan na Mutumin da ke gefenta. Shi ba ma'abocin dariya ba ne sai murmushi, amma da ya yi dariyar kalar addu'o'in da ta yi ta yi, yadda bakinta ke motsi ma kaɗai abin dariya ne.

"What?" Ta faÉ—a tana É—aga gira bai ce komai ba ya juya yana kallon window.

Da aka zo za a serving na su lunch Zaytoonah har da na jaraba ta zaɓa. Yana gani yadda ta zage tana cin abincin da ya ke tunanin wannan cin kaɗai ya isa ya sa ta ƙiba. Duk abinda aka kawo sai da ta cinye shi tas.

Shi ba ma'abocin surutu ba ne da ya tambayeta ko da sunan ta ne dan yarinyar ta burgeshi, she's funny.

Da tafiya ta yi nisa TV da ke gabanta ta fara kallo ta sa headphone a kunnenta tana sauraro amma hakan bai hana bacci É—aukan ta ba.

Lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalleta zuciyar sa cike da tunani kala-kala akan ta.
Ƙila ɗaliba ce za ta koma makaranta.
Ƙila kuma hutu za ta je. Ko kuma ma dai gidan Iyayen ta za ta koma ta zo Nigeria hutu ne. Dan da ka ganta ka san ita ɗin 'yar manyan mutane ce. Kayan jikinta da yanayin fatar jikinta kaɗai ka kalla ka san 'yar hutu ce.

Da su ka zo sauka ne ya mustering courage ya ce "are you a student?"

"Kutmelesi. Ashe kana magana? Shine tun tasowar mu ka yi shiru. Ikon Allah" ta faɗi da Hausa. Ganin ya ƙura ma ta ido ya sa ta tabbatar bai ji abinda ta ce ba.

Ta wani turo baki ta ce "Yes, i'm a student"

Ta yi gaba ta bar shi. A wannan lokaci he wished shi ma'abocin magana ne da ya nuna ma ta cewa ya ji abinda ta ce. He wish zai iya bin ta ya tambayeta sunan ta da makarantar da ta ke amma ƙasaita da sarautar sa ba za su bar shi ba. Tambayar da ya ma ta ma ya jima yana jujjuyawa a ransa kafin ya fito da shi waje da ƙyar ganin fa tabbas rabuwa za su yi daga nan kuma bai san komai gameda ita ba...

*A nan na kawo ƙarshen free pages na chronicles of Zaytoonah. Za ki iya supporting ɗina ta hanyar biyan #300 domin samun cigaban labarin*

***

*ya rayuwar auren Zaytoonah za ta kasance da Zuhair Muhammad Ilyas wanda ba ta taɓa gani ba sai a hoto?*

*shin wace irin ƙaddara ke tattare da Zaytoonah ayayinda ta buɗe wani sabon babi a rayuwarta akan wannan aure da akayi bisa sharaɗi mai sarƙaƙiya?*

*Muntari zai haƙura da Maryam kuwa? Ko kuma dai zai tuba ne ya faɗi abinda ya sa aka yiwa T J?*

*shin bayan aurar da Zaytoonah Maryam za ta samu kwanciyar hankali? Ko kuma dai ya rayuwar ta zai kasance with the beast Muntari?*

*wai ina T J ne? Yana raye ko ya mutu? Shin ma wai zai dawo ga iyalinsa kuwa?*
*shin wanene wannan mutumin da Zaytoonah ta haÉ—u da shi har sau biyu sannan wani rawa zai taka a rayuwar ta?*

*daga ƙarshe shin Barrister Zaytoonah za ta iya jayayya da ƙanin kakanta kuwa? Wato Augustus Udodiri Uzodinma, wanda ya kashe Kakannin ta ya kuma cinye dukiyar su?*

Da sannu za ku gano komai a cikin paid group na labarin chronicles of Zaytoonah.

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 22

Bismillahir Rahmanir Rahim

Cikin sati biyu ta kammala komai na makarantar ta ta zama full student. Sai dai ta je class ta É—au darasi, har ta fara sabawa.
A gida kam the same routine gareta kullum. Ta yi wanka ta ci abinci ta je makaranta, idan ta dawo ta ci abinci, kallo sai bacci. Duk bayan kwana biyu ta kan kira gida su gaisa.
Kamar yadda Ben ya gargaɗeta ba ta shiga ko'ina a ɗakunan sama sai ɗakin ta. A ƙasan akwai study room, gym room, kitchen da dining akwai kuma ɗakuna biyu wandanta ke tunanin guest room ne.
Kulkum sai ta ga Ben amma Zuhayr sai ta yi kwana biyu uku ba ta sa shi a ido ba. Ko sun haÉ—u tsakanin su gaisuwa ne sai shi ya tambayeta ya karatun?.

Yau Sunday tana gida tun safe ba abinda ta ke yi sai bacci. Bayan ta tashi ta yi wanka ta fito daga ɗakin ta, haka kawai ta ji sha'awar duba ɗakunan saman ta ga miye a ciki da ake ɓoye ma ta. Ɗaki na gefen na ta ta fara dubawa wanda shima ɗakine kamar na ta sai dai furnitures ɗin ciki sun banbanta da na ta. Ɗaki na gaba da ta buɗe ta ji shi a rufe ta yi tsaki ta wuce gaba, ta sa hannu za ta tura ƙofar ta ji a dafa kafaɗarta sai da ta firgita.

"Mi ki ke son yi?"

Ta juyo a tsorace amma ganin Ben ya sa ta haÉ—e fiska ta ce "shine za ka tsoratani"

"Na gaya mi ki iya limit É—in ki a cikin gidan nan dan haka ki kiyaye"

"Ni matar Zuhayr ce zan, iya shiga duk inda na ke so a gidan nan" ta faɗa da ƙarfi duk da kuwa yanayin da Ben ɗin ke kallon ta ya ɗan girgiza ta.

"Stay within your limits" ya faɗa yana buga hannunsa a jikin bango. Da ƙyar ta haɗiyi miyau dan yadda ya bugi ginin sai da 'yan hanjinta su ka kaɗa

"Its a warning, Zaytoonah"...

Bayan ta sauka ƙasa ta hango Zuhayr yana cin abinci a dinning.

"Tun safe ki ke bacci, ba kya gajiya da bacci ne?"

"Ina ruwanka" ta faÉ—a tana zaunawa a kujerar da ke opposite É—in sa.

Kallon yadda ta ke cika plate É—in ta da abinci ya ke yi yana mamaki a ran sa.

Tana É—aga ido idon su ya haÉ—u "ko abincin ma za a hanani ci ne? Tunda na ga komai a gidan ka doka ne"

Zuhayr ya girgiza kai.

Za ta sake magana sai ga Ben dan haka sai ta yi shiru. Bai wani ci abincin ba sosai ya tashi ya haura sama shima Ben ya bi bayan sa, mamakin maƙalemata da Ben ke yiwa Zuhayr ta ke yi. Kullum haka za ka ga yana bin sa kamar bindi. Ita kam jan girkinta ta yi mai kyau kafin ta bar wajen.

Da yammacin ranan Zuhayr ya ce ma ta ta shirya za su je ƙauye gobe ta gaida Kakannin sa.

"Dama a America akwai ƙauye ne?"
Bai kulata ba sai dai murmushin gefen baki da yai.

"Ehhm kwana nawa za mu yi?"

Wannan karan Ben ne ya amsa ma ta da cewa ba za su kwana ba.

Ta harareshi ta ce "shegen shishshigi, ko waya tambayeka oho"

Zuhayr yana jin ta amma bai ce komai ba.

***

A Helicopter ɗin sa su ka tafi wanda shi ne ya tuƙata, maimakon Dreban da ya tuƙo su rannan da ta fara zuwa garin.

A tsakiyar filin da Dawaki ke kiwo ya sauka.

"Masha Allah" ta furta lokacin da ta sauka.

HADDISH RANCH kenan su ka iso, gidan gonan kakannin Zuhayr ta wajen uwa.
Su na tafiya tana ma sa tambayoyi amma ko uffan ba ya faÉ—a, wani lokaci Ben na amsa ma ta tambayoyin wani lokaci shima yai shiru.
Ta ga alama shi Zuhayr idan ba shi ya kawo magana ba baya so a ma sa magana. Haka dai su ka ƙarisa madaidaicin gidan da ke tsakiyar gidan gonan.

Tana tsaye Zuhayr ya je ya kissing goshin wani tsohon bature da ke zaune akan sofa yana karatu, shima Ben É—in haka ya ma sa.
Ba ta ji mi Zuhayr ya ce da tsohon ba dan ƙasa-ƙasa yai maganar, ta dai ga tsohon ya ɗaga ma ta hannu alaman ta zo. Ta ƙarisa wajen sa ta tsugunna ta ce "good morning GrandPa"

"Morning pretty girl" ya amsa yana murmushi itama murmushin ta yi tareda miƙewa.

A kitchen su ka haÉ—u da GrandMa tana girki. Matar tana kama sosai da mahaifiyar Zuhayr. Itakam bayan Zuhayr ya nuna Zaytoonah zuwa ta yi ta rungumeta tana yi ma ta maraba da zuwa gidan gonan su.
Zuhayr da Ben su ka bar ta a kitchen ita da GrandMa.

Tsayawa ta yi tana kallon kitchen É—in wanda yawanci abubuwan ciki tsofi ne.
GrandMa ce ta katse shirun da cewa "ina fata Zuhayr yana kula da ke?"

Zaytoonah ta gyaÉ—a ma ta kai.

"Yana cikin kaÉ—aici har yanzu. Da ya faÉ—amin an ma sa aure a Nigeria na É—auka babbar mace ce amma sai ya ce ba ki ma kai 18yrs ba"

" yes, just recently na cika 17yrs"

" ki kula da shi"
Ta furta tana buÉ—e oven.

Cikin zuciyarta ta maimaita kalmar da tsohuwar ta faɗa tana ƙoƙarin gane me ta ke nufi da hakan.

Ƙarfin hali ta yi ta tambayeta abinda ke ci ma ta tuwo a ƙwarya tun zuwan ta Vegas. Abinda Muhsina ta gaya ma ta gameda Zuhayr bai gamsar da ita ba ga ɗimbin tambayoyin da ta ke da shi a kan sa.

"Waye Zuhayr?"

GrandMa ta kalleta na ɗan wasu daƙiƙai kafin ta ce " kar ki damu za ki san kowaye shi a hankali"...

Bayan ta gama girkin, Zaytoonah ta taya ta jerawa a kan dinning area É—in wanda duk a cikin kitchen É—in ne. Sannan aka kira mazan su ka shigo dan aci abinci.
Chapter 51 · 0% Book details