Sashe 25
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maryam ta san ƙarya ya ke yi amma ta ƙyaleshi tunda baya son faɗa ma ta matsalar sa.
Itama ya sanar da ita ƙarshen wata za su koma sabon gida amma har ya saura kwana shida ba ta ga an fara shiri ba. Da ta tambayeshi sai ya ce an fasa tarewar akwai wasu ayyuka da ba a gama ba. Ta yi shiru ba ta kuma cewa komai ba, T J ɗin da ta sani has being behaving strange wanda ta san duk yadda aka yi wani abu ne daya danganci tsakanin sa da Iya.
Tunanin ƙara aure ne ya fara zuwa ma ta. Ƙila tunda ya yi gini Iya ta ce ya ƙara aure su zama su uku. To daga baya kuma sai ta fara tantamar haka. Dan Hajjo da Inna ba za su yadda da wannan ba.
To amma minene?
Ta dai bar tambayar a ranta zuwa lokacin da T J zai furta ma ta matsalarsa da kan sa.
Saura kwana uku tashin su ya sanar da Iya an fasa tashin sai wani watan saboda za'a ƙarisa wasu gurare da ba'a gama ba.
Iya ta fara masifa wai ta san ƙarya ya ke yi. Idan kuwa dan baya son bin maganarta ne to ita gobe za ta bar ma sa gidan idan ya so ya je ya tare da Maryam tunda ya fi son matar sa akan uwar da ta haifeshi.
T J ya shiga ba ta haƙuri amma fir ta ƙi.
Duk abinda aka yi a idon Auwal hakan yasa ya ji haushin Iya sosai.
Maryam na dawowa ya tareta da murna ya fara ƙoƙarin ɗaukan Zaytoonah wacce ke cin biscuit duk ta ɓata bakinta da uniform ɗin ta. Ta maƙe kafaɗa tana faɗin "leave me"
"Auwal ajiyeta kawai tun É—azu ta ke damuna da rigima"
Nursery one Zaytoonah ta ke, da an tashi a makaranta Maryam ke zuwa ta É—aukota ta wuce da ita office É—in ta, idan ta tashi a office sai su dawo tare. Wani lokaci kuwa T J ne ke zuwa ya É—aukota ya wuce da ita na shi office É—in idan ba shi da class a lokacin.
Bayan ta yi wanka ta yi sallar la'asar ne ta fito ta shiga kitchen dan ta fara girkin dare, yanayin jikinta kwana biyun nan ba ta gane ba tana hasashen ma ko ciki gareta dan kwana takwas kenan ba ta ga jininta ba. Tana son zuwa Asibiti ta tabbatar da hasashenta amma gaba É—aya she's busy a office idan ta dawo kuma ta gaji.
Tana yanka alayyaho sai ga Auwal da Zaytoonah sun shigo sanye da uniform É—in Islamiyya.
Zaytoonah na cin wani chocolate baki da hannu duk yayi dumu-dumu da shi.
"Auwal yanzu sai da ka bata chocolate É—in nan bayan na hanaka"
"Mommy cewa ta yi idan ban ba ta ba bazata je Islamiyyan ba"
"Oya come here" Maryam ta faɗa da ɗan ƙarfi
Zaytoonah ta ɓoye a bayan Auwal tana wiki-wiki da ido dan ta san yanzu za ta ƙwace chocolate ɗin.
"Zaytoonah"
Kawai ta ɓare baki da kuka. Maryam ta jijjiga kai kawai ta ce " ku je Auwal amma ka share ma ta baki da hannu kafin ku fita"
"Ke kuma zanyi maganin ki, tukunna ma chocolate nawa kika sha a office yau?"
Zaytoonah ta ɗaga yatsunta huɗu still tana maƙale da Auwal ta ƙi isowa wajen Maryam dan ta san halin mommyn na ta ba ta dukanta amma kunnenta zai sha murɗa.
Bayan sun fita sai kuma Auwal ya dawo da sauri ya fara yiwa Maryam magana ƙasa-ƙasa. Hajjo dai ba ta gida ta fita unguwa amma Iya na ɗaki.
"Mommy yau da rana kafin ki dawo Iya ta dinga yiwa Daddy faɗa, ta ce wai ba za ki koma sabon gida ba. Kuma fa Daddy har kuka ya ma ta amma ta ƙi sauraren shi, ni kam indai ba za ki koma sabon gida ba nima ba zan je ba"
Tunda ya fara maganan ta ƙura ma sa ido. Auwal yana da wayo, shekarun sa goma yanzu, yana aji huɗu a primary. Mafiya yawancin lokaci idan anyi wani abu a gidan a bakin sa ta ke ji, shima ya gane Iya da Hajjo ba sa son Maryam kuma suna ma ta munafurci, shiyasa ma ya tsanesu ya fi damuwa da Mommynsa Maryam.
"Auwal ku wuce Islamiyya" abinda ta iya faÉ—a kenan saboda zuciyarta da ya cunkushe.
Sai yaushe wannan Matar za ta dena ci ma ta fuska.
Ina ma Goggo ce ta haifi Tijjani, da za ta fi kowa sa'ar uwar miji.
Amma Iya, Iya, Iya sai dai kawai Allah ya rabata da ita lafiya.
Iya ta yi kishi da Goggo yanzu kuma da ita ta ke kishi.
Ba ta ga laifin Baffah da ya fi son Goggo ba lokacin yana raye. Kyawawan halayenta su suka sa ta samu babban matsayi a zuciyarta. Iya ta ƙare rayuwan aurenta acikin baƙin kishi, gashi yanzu da tsufanta ma ba ta bar kishin ba.
Illiteracy, Greedy and Envy su ne manyan abubuwan da su ke damun Iya cikin ukun ba ta san wanne ne ma yafi wani yawa a ciki ba.
At first ta É—auka haihuwar Zaytoonah zai sassauta tsanar da Iya ta ma ta amma abun ba haka yake ba. Matar da har sheganta ma ta 'ya ta ke yi.
Tun kafin Zaytoonah ta yi wayo ta gane ƙiyayyar da Iyan ke ma ta yanzu ma da ta fara wayo ko gaisheta ba ta yi.
Countless times ta kan cewa Maryam "Mommy i hate Iya"
Maryam ta kwaɓeta akan ta dena faɗin haka.
Da sanyin jiki ta ƙarisa girkin. Ta gyara kitchen ɗin ta koma ɗaki. Tsayawa ta yi bakin hoton T J da ke jikin frame a bangon ɗakin. Sanye ya ke da kayan bautar ƙasa yana murmushi.
Yana daga cikin ƙaddararta ta haɗu da T J, yana daga ƙaddararta ta faɗa makauniyar soyayyar sa, yana daga ƙaddararta ta wahala a zama da shi.
Despite everything ko kaÉ—an soyayyar da ta ke ma sa bai ragu ba.
Ta jima tana kallon hoton kafin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya ta bar wajen.
Da dare T J bai dawo da wuri ba har goma, gaba É—aya Maryam ta damu sosai.
Ta san maganan Iya ne ya sa shi ƙin dawowa da wuri.
Ƙarfe goma da minti ishirin da biyar ta ji shigowar sa gidan.
Ya buɗe ƙofan ɗakinta ya ga wuta a kunne. Suna ido huɗu da shi yai saurin kau da kai yana faɗin " ba ki kwanta ba?"
Takalmin sa ya cire ya sa gefen ƙofa ya zo ya zauna a gefenta.
"Sorry na tsaya duba assignment É—in yara ne a office ban san dare yayi har haka ba"
Hannun sa ta kamo ta ce " ba sai ka yi bayani ba na san komai. Barin kawo ma ka abinci"
"No ki barshi gobe zan ci ɗumame" ya faɗa yana miƙewa dan ya cire kayan sa
"Da ka ci abincin kuwa sai na maka albishir da abubuwa guda biyu"
Ya É—an juyo ya kalleta ya ce "Maryam dare yayi ba zan iya ci ba. Ki gaya min albishir É—in"
Tausayin sa ta ji ya kamata, hatta maganar sa chanjawa ta yi, ga idon sa da yai jaa.
"To barin haÉ—o ma ka tea"
Tana da flask É—in ruwan zafi a É—aki dan haka fita ta yi ta je kitchen ta É—auko cup da spoon. Ta É—au kayan tea da ke saman drawer ta haÉ—a ma sa tea mai kauri wanda ya ji sugar sosai kaman yadda ya ke so.
Ya cire kaya ya sanya jallabiyar sa da ya ke bacci da shi, yana zaune bakin gado yayi tagumi, ta cire hannunsa daga tagumin da yai ta ce "ka sha tea dan Allah"
Ya karɓi kofin ya ce na gode.
Ta hau gado ta koma bayansa ta fara masa massage É—in goshin sa a hankali a hankali daga nan kuma ta koma wuyan sa zuwa kafaÉ—ar sa.
"Minene Albishir É—in?"
"Ka shanye tea É—in tukunna" ta amsa ma sa ta cigaba da danna ma sa kafaÉ—un sa.
"Adaeze ta miki rigima a office ko?"
"Kai ma ka san za ta yi tunda kai ta É—auko wajen rigima"
Yai murmushi yana lumshe ido saboda yadda ya ke jin daÉ—in tausar da ta ke ma sa.
"Ka san dai kanada hawan jini amma sai ka dinga sawa kan ka damuwa"
"Maryam..."
"Ka bari na gama magana please. Yanzu idan wani abu ya sameka ya ka ke so na yi? Abu na daminka ba za ka faÉ—a ba. Its better ka gaya min tun da wuri rather than sai daga baya na ji ko kuma na ji a bakin wanda bai kamata ba"
"I'm sorry"
"Shshhhh. The first surprise is"
Ta kamo hannunsa ta sa a cikinta.
"I'm 90% sure ina tareda junior Teejay"
Ya juyo da sauri yana zaro ido
"Really?"
"Ban je na yi gwaji ba amma ina jin symptons É—in"
"Alhamdulillah, Maryam you really make my day" ya faÉ—a fiskan sa É—auke da excitement
"And the second surprise is..."
Ya ɗaga gira yana jiran ta ƙarisa maganar
"Na amince zan zauna a nan, its actually a good idea. Rather than na zauna da su Iya ina zama cikin damuwa kullum is better mu zauna gida daban-daban. You dont need to kill yourself because of that"
Jikinsa a sanyaye ya tallafo fiskarta ya ce " its not fair Maryam. Da sunan ki na fara ginin nan and"
Ta sa yatsa ta rufe bakinsa ta ce " idan Allah ya buÉ—a ma ka wani lokacin sai ka gina min nawa gidan ko ka siya min wani gidan. Ni ban ji haushin Iya ba, zaman lafiya ma ta kawo mana"
Cire yatsar ta da ta yi yai daidai da haÉ—e bakin su da yai.
"Mommy tea, i want tea" muryan Zaytoonah ya daki kunnuwan su.
Maryam ta juyo ta kalli 'yartata wacce tuni ta riga ta buÉ—e ido.
"Ya Allah! this girl can eat from morning till night, duk abincin da ki ka ci kafin ki kwanta bai isheki ba"
T J ya ce " kar ki takura min Princess"