← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 161

Sashe 59

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Alinah ta haɗu da Zuhayr mahaifiyar ta ta jima da rasuwa ita kuma Helena tana gidan tsoffi saboda cutar Alzheimer da ke damun ta. Ƙanin Kakanta Hammad shima ya rasu shi kuma Yusuf Hammad ya koma Saudiyya da zama saboda aiki da ya samu a chan. Aiki ne ya kawota Las Vegas bayan ta yi internship ɗin ta a wajen ta ji daɗin zama a garin ashe kuma ajalinta ke kiranta shiyasa ta bar Michigan ta dawo Las Vegas da zama...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 25

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Frightened*

Zaunar da ita yai a kujera har lokacin tana hawaye. Ya sa babbar yatsar sa ya goge ma ta hawayen da ya zubo na ƙarshe.

"Idan Mommy tana kusa da ke yanzu mi za ta ce miki?" Yai tambayar yana kallon ƙwayar idon ta.

"Cewa za ta yi" sai kuma ta yi shiru

"Ki faÉ—i gaskiya"

Ta sunkuyar da kan ta ta ce "Cewa za ta yi na dena kuka na yi addu'a"

"And yanzu da ba ta nan za ki yi amfani da maganarta ba kenan?"

Ta kalle shi briefly kafin ta kau da kai gefe ta ce "to ai, to ai" sai kuma ta fashe da kuka tunowa da ta yi da Daddyn ta.
Cikin kuka ta ce "ina tsoron za a rasa ta kamar Daddy, ba zan iya jure rasa ta ba"

Jawota yai jikinsa ya rungumeta yana É—an bubbuga bayanta yayinda Zaytoonah kuma ta ci gaba da kuka a jikin sa. Bai hanata kukan ba har sai da ta gaji da kan ta ta yi shiru tana sauke numfashi. A wannan lokacin ne ya fara hura ma ta iska a kunne kaÉ—an-kaÉ—an har ta ji wani sanyi ya fara ratsa ta.

"Idan kin yarda lets make a deal"

Ba tareda ta bar ƙirjinsa ba ta ce "what deal?

"Ina so ki bani kwana 21, cikin kwana ishirin da ɗaya zan sa a nemo miki Mommyn ki, ke kuma in return za ki dena kuka, za ki yi karatu ki ƙarisa exams ɗin ki lafiya, sannan ba za ki sake yin zancen Mommy ba, addu'a kawai za ki dinga ma ta"

Ta yi shiru na É—an wani lokaci kafin ta ce "idan ba a ga Mommy ba fa?"

"Zan kai ki Nigeria da kai na, and duk abinda ki ke so zan mi ki"

"Ko da helicopter É—in ka na ce ina so?"

"Ko da helicopter É—ina ne Zaytoon"

Ba ta yi magana ba wanda shirun ya tabbatar ma sa ta amince da maganar sa. Ta jima a jikin sa, chan ya ji numfashin ta ya chanja sai ya leƙa fiskarta sai ya ga ashe har ta yi bacci. Bai yi ƙoƙarin tashin ta ba sai ya janye jikinsa a hankali ya kwantar da ita akan kujeran sosai. Ƙura ma ta ido yai for the first time yana kallon fiskarta yadda ta ke bacci so peacefully kamar yarinya ƙarama, ko da ya ke yarinya ce ai. Idan ba ma gidadanci irin na Kakan sa ba, taya zai aura ma sa yarinya 'yar shekara shabakwai. Ko da ya ke kamar yadda Mommy ta gaya ma sa auren Zaytoonah ta yi ne kawai saboda shine mafita gareta ma fi sauƙi amma ba wai dan har zuciyarta tana son auren ba.

Tunda ya shigo É—aki ya tsaya yana kallon kan sa ajikin madubi yana huci. Chan ya kai wa madubin naushi yana faÉ—in "babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da kai Zuhayr, babu wanda ya isa ya samu soyayyar ka idan ba ni ba. Becareful Zaytoonah, Becareful"

Hannun sa da ya fara jini ya É—aga sama yana kallon yadda jini ke bin yatsunsa saboda yankuwa da yai da glass ya ce "i can kill for you and i can die for you Zuhayr. No can come between us, absolutely no one"
Chan kuma sai ya fashe da dariya...

Zuhayr bayan ya bar falon É—akin sa ya shiga yai wanka ya chanja kaya ya sauko, har lokacin Zaytoonah ba ta tashi ba. Ya zauna kusa da ita yana latsa wayar sa a haka Ben ya sauko ya same shi, Ben ya tambayeshi ko ya ci abinci ya ce ma sa baya jin yunwa, É—agowan da zai yi sai ya ga hannun sa É—aya naÉ—e da bandeji.
"Miya samu hannun ka?"

Ben ya ce " domestic accident"

Zuhayr ya ce "sorry" Ben yai murmushi dan ba abinda ya ke bala'in so irin ya ga Zuhayr na damuwa da shi , hakan ba ƙaramin faranta ma sa rai ya ke ba.

Da dare bayan ya karɓi numban Auwal a wajen Zaytoonah sai ya kira shi yana tambayar sa gameda ɓatan Mommyn Zaytoonah. Auwal ya ce su ma suna tsumayin abinda ya faru dan har yanzu ba a gano su waye ba, kuma ba a buƙaci kuɗin ramson ba.

Zuhayr ya jinjina maganar yana mamakin yadda aka sace mutum a ƙofar gidan sa rana tsaka amma har ya wuce 24hrs police ba su yi komai ba. Shi kuwa Auwal nuna ma sa yai Nigeria ce fa, Nigeria kuma ba America ba ne.

Zuhayr ya ce ya dinga updating na sa gameda situation ɗin shima kuma zai kira wani top official a ɓangaren Police ya ji ko zai iya taimaka ma sa ta wani ɓangaren, Auwal ya ma sa godiya.
Har zai kashe wayan sai kuma ya tambayeshi ina ƙannen Zaytoonah sai ya ce suna gidan Uncle Muntari, tun jiyan ya zo ya ɗauke su ya maida su gidan sa.
Bayan ya ajiye wayan sai zuciyar sa ta ankara ba wannan Uncle Muntarin ba ne ya yi niyyar aurar da Zaytoonah ga wani illiterate har ta kai Mommy ta amince da tayin Alhaji Iliyasu?
Da sauri ya sake kiran Auwal ya ce ma sa "ka saurareni da kyau, ina da suspect kuma ina so ka yi aiki da hankalin ka saboda mu tabbatar ko shine idan shi É—in ne kuma mu kama shi"

Auwal ya ce "ina jin ka"...

Da ke hankalin ta a dagule ya ke ba ta ci wani abun kirki ba ta kwanta duk yadda Zuhayr ya takura ma ta ƙin ci tayi wai ta loosing appetite ɗin ta. Shi kam na shi ido dan ya san ɗan abincin da ta tsakura ɗin nan ba isar ta zai yi ba ƙarshe sai yunwan dare ya tashe ta. Tun zuwan ta gidan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ya sha ganin ta da tsakar dare tana saukowa kitchen ta je ta nemi abinda za ta ci.

Yau ɗin ma ta tashi fitsari ne ta kasa komawa bacci saboda cikinta da ke ɗan murɗawa. Ganin baccin ya ƙi zuwa ya sa ta sauko ka sa dan ta nemi abu ta ci.
Tana shiga kitchen ta fara buÉ—e fridge dan nan ne za ta yi saurin samun abin sa wa a baki instantly.

Ɗaukewan wutan kitchen ɗin ne ya sa ta tsaya chak, mamaki da tsoro ya shigeta. Tun da ta zo gidan wuta ko shaking bai taɓa yi ba balle ya ɗauke. Ta kore tsoron ta hanyar tunowa da cewa ƙila bulb ɗin kitchen ɗin ne ya mutu, amma duka bulbs ɗin sai su mutu lokaci guda? Ta tambayi kan ta lokacin da ta tuno ta waje uku kitchen ɗin ke samun haske. Ta fara takowa a hankali hannunta a gaba tana shashshafawa saboda kar ta ci karo da wani abu. Ji ta yi an dafa kafaɗan ta ta baya hakan ya sa ta sa ihu haɗeda yin gudu sai dai ba ta yi nisa ba ta bugu da bango hakan ya sa ta tsaya ta juyo jikinta na rawa. Tana hango mutumin na nufota a hankali amma ta kasa motsawa, ba ta ganin fiskar sa saboda duhu. Sai da ya kusa isowa ta ga ya fito da wata ƙatuwar wuƙa.

"Zuhayyyyyyyr" ta challa ihu daidai mutumin ya ɗaga wuƙa zai daɓa ma ta. Faɗuwa ta yi a wajen ta suma tun kafin ma wuƙar ya shigeta.
Ben na ganin haka ya je ya kunna wutan kitchen ɗin ya maida wuƙan jikin sa yai tafiyar sa. Dama tsoratar da ita yai niyyar yi, da haka ya fara yiwa Alinah kafin da ta ƙi rabuwa da masoyin sa Zuhayr ya kai ta inda ba za ta sake ganin Zuhayr ba shima kuma Zuhayr ba zai gan ta ba sai dai a hoto.

Sanyin asuba ne ya farkar da Zaytoonah daga suman da ta yi, kusan minti uku kafin hankalinta ya dawo jikin ta gaba ɗaya, ganin ta a kitchen kuma ga hasken lantarki tarr a kitchen ɗin ya sa ta yi saurin miƙewa zaune tana tattaɓa jikinta ko za ta ji sukan wuƙa amma babu. Mamaki ya cikata yayinda ƙwaƙwalwarta ke tuno ma ta abinda ya faru. Da ƙyar ta saita kan ta ta fita a kitchen ɗin inda ta haɗu da Zuhayr da Ben suna sanye da riga marar hannu da gajeran wando kalar nazy blue za su fita jogging.

"Kar ki ce min a kitchen ki ka kwana?" Zuhayr yai tambayar yana riyawa a ran sa abinci ta je ci bacci ya É—auketa.

"Zuhayr someone tried to kill me last night"

Zuhayr ya bushe da dariya.

"I'm serious Zuhayr, Wallahi"

Ganin ta yi maganar kamar za ta yi kuka ne ya sa shi dena dariyar ya tsaya yana sauraron bayanin ta harda cewa ya biyota kitchen É—in ta nuna ma sa yadda komai ya faru shi kuwa ya bi ta amma zuciyar sa ko kaÉ—an bai yarda da bayanan ta ba, ya fi tunanin sace Mommynta da aka yi ya sa ta ke hallucinating abubuwa.

Bayan ta gama bayani ya kama hannunta duka biyu ya ce "Zaytoonah mafarki ki ke yi, babu wanda ya ke kwana acikin gidan nan sai mu uku and akwai security a gidan nan duk wani wanda zai shiga gida bayan an rufe warning alarm na gidan zai yi ta bugawa. Na san tunanin Mommy ne ya sa kika fara irin wannan mafarkin amma kar ki damu za a sameta"

"Ni fa ba mafarki ba ne, na tashi daga bacci na sauko ƙasa na shiga kitchen zan ci abinci sai aka kashe wuta sai"

"Ba dole kiyi ta imagining abubuwa ba tunda abinci ne a ran ki"
Chapter 59 · 0% Book details