Sashe 110
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Justice na shiga É—aki sai ga kiran Hajia Abu. Bai É—au wayar ba sai da ya shiga banÉ—aki yai wanka ya fito tukunna kafin ya kira ta.
Sai da su ka gaisa kafin ta gabatar ma sa da buƙatar ta wanda ya sa shi zama daɓas akan gado.
"Amma Hajia yaushe na yi aure da za a fara maganar wani auren"
"Yanzu Galadima sai mu zubawa yarinyar nan ido har sai ta illata yaran nan. Ina sane da duk abinda ya faru jiya kuma ba zan lamunta da irin wannan ba. Kuka fa sosai Raziya ke yi jiya da ta kirani tana roƙona akan na ma ka magana ka chanja wa Antyn su gida ta takura mu su. Ka san mi hakan ya ke nufi?"
"Zan yiwa Raziya magana kar ki damu Insha Allahu nan da lokaci kaÉ—an za su fahimci juna"
"A taƙaice dai kana so ka sanar da ni ban isa ba kenan?"...
***
Sai da Zaytoonah ta ji ficewar Justice a gidan kafin nan ta fito ta nufi kitchen. Girki ta shiga yiwa yaran ta da za su zo, tana cikin yi Atika itama ta shigo ta hau na ta girkin duk cikin su ba wanda ya tankawa kowa idan ka cire gaisuwar dole da Atikar ta yiwa Zaytoonah.
Tana zaune a falo tana jiran isowar su dan Salman ya ce sun shigo Abuja. Kusan minti sha uku sai ga su sun iso. Da gudu su ka zo suka rungume Zaytoonah suna murna.
"Mom gidan ki na da kyau" Hadid yai maganar yana ƙarewa falon kallo.
"Mom wai Uncle Salman ya ce kwana ɗaya za mu yi, ina tareda ke zamu dinga zama ko?" Hashir yai maganan yana taɓa kafaɗarta.
"Yanzu dai bari ku ci abinci ku huta sai na amsa mu ku duk tambayoyin ku. Kun ji"
Su ka gyaÉ—a ma ta kai.
"Galadima yana gida?" Salman ya tambaya
"Baya nan" ta amsa ma sa.
Lokacin da ta serving É—in su abinci ita da hannunta ta ke ciyar da yaran, idan ta bawa wannan sai ta bawa wannan.
"Mommy ta gaya miki matar Chief Udodiri ta fara processing ɗaukaka ƙara a supreme court?"
"Ina ga ta manta ne"
"Ai Insha Allahu ko anje chan É—in ma hukuncin kisa ne zai tabbata a kan sa"
"Sosai ma kuwa"
Sallamar Justice ya katse mu su hiran ta su. Yayinda yaran su ka tashi daga gaban Zaytoonah da gudu su ka nufi wajen Justice suna kiran "Daddy"
Duk da ɓacin rai da ya ke tattare da shi amma ganin yaran ya sa shi jin wani sanyi a ran sa.
Bayan sun gaisa da Salman ne Zaytoonah ta ce " sannu da zuwa" saboda ganin idon Salman.
Ya amsa ma ta ransa a sake kamar ba komai a tsakanin su.
Abinka da yara tuni su ka buge wai dole Justice sai ya zauna ya cigaba da ba su abinci a baki. Zaytoonah ta daka mu su tsawa amma Justice ya ce ta ƙyale ma sa 'ya'yan sa. Haka ya zauna a wajen ya ƙarisa ciyar da su da hannun sa yayinda su ke taɗi sama-sama da Salman. Ita kan Zaytoonah sai bar mu su wajen ta yi.
Zuwa yamma Salman ya bar gidan dan ya ce ba a nan zai kwana ba duk da kuwa Zaytoonan ta so ya kwana a nan gidan.
Suhailah na dawowa daga Islamiyya da ta ga 'yan biyu tuni ta kama tsalle, ta biyewa yaran aka cigaba da wasa da ƙiriniya kamar ba ita ne ta samu ƙuna jiya ba, dama ƙunar ma ba yawa.
Da dare dai abincin ta Justice ya ci dan tare da 'yan biyu su ka zauna su ka ci.
Yaran da ta sa aka kawo ma ta dan su É—ebe ma ta kewa sai gashi sun tare a wajen Justice su na tsiyar su sun ma manta da ita.
Ƙarfe tara ta shiga falon Justice dan ta koro yaran su zo su yi bacci amma yaran su ka tuɓure wai a wajen Daddyn su za su kwana. Ba halin ta mu su jan ido dan Justice na wajen, dole dai sai komawa ta yi ta je ta ɗauko mu su kayan baccin su ta kawo. Ta fara cirewa Hashir riga yayinda Justice ya cirewa Hadid na shi, su ka sa mu su rigan bacci wanda pyjamas ne mai zane zanen cartoon a jiki, na Hadid sky Blue na Hashir Ash colour.
"Kar ku manta ku yi azkar kafin ku kwanta kun ji?"
" Yes Mom".
Kusan bayan tafiyar Zaytoonah da kusan minti Ishirin yaran su ka yi bacci. Haka ya É—auke su É—aya bayan É—aya ya kai su É—akin sa ya kwantar da su akan gado ya tofa mu su addu'a kafin ya fito falo, kashe kayan kallo yai ya fita ya je É—akin yaran sa dan ya duba su.
Yana fitowa ya haÉ—u da Zaytoonah wanda itama ta fito daga na ta É—akin.
"Ba ki yi bacci ba?"
"Yanzu zan yi. Dama zan gaya ma ka ƙarfe shabiyu zan zo na tashi yaran dan su yi fitsari, idan ba haka ba gadonka zai malale da fitsari"
"Zan tashe su"
"Na gode" ta furta tareda juyawa za ta tafi.
"Ina son magana da ke"
Zuciyar ta ya wani buga damm.
Bin bayan sa ta yi su ka wuce falon sa. Yana zama itama ta É—an É—okanu a kujera opposite da shi.
"Wannan duk haÉ—e fiskar saboda ni ne ko?"
Ta yi saurin girgiza ma sa kai
"Idan ba haka ba to a min murmushi na gani"
"Hmmm" kawai ta iya faÉ—a.
Sai da ya ɗan ɗau lokaci kafin ya ce "Da fatan za a min haƙuri saboda tsawan da na miki jiya"
"Duk wani fushi da ake da ni ayi haƙuri"
"Ni ba fushi na ke ba"
Shi ba yaro ba ne, 'yan biyu daya gani a gidan ya tabbatar ma sa ta É—au abinda ya faru da zafi.
Murmushi yai ya ce "kin tabbata Amarsu ta Angonta"
Sai gashi ga Zaytoonah ta buge da dariya.
Mamakin Justice ta ke yi, wani lokaci idan ya yanko magana kaman ba shi ba....
***
Tunda ta zo gidan yau ne ta fita. Muhsina ce ta kirata akan ta kasa cin abincin gidan ta komai aka dafa wari ya ke ma ta. Kusan ma sati kenan sai dai a karɓo ma ta abinci daga restaurant ta ci to shine yau ta kira akan dan Allah ta ma ta irin miyan Agusin Mommy ta kawo ma ta. Kiran Justice ta yi ta ce ma sa za ta je ta dubo Muhsina ba lafiya ya ce ma ta ta je ba matsala amma ta dawo da wuri, ya ce ta sa Dreban su Raziya ya kaita gidan.
Bayan ta gama miyar ta haÉ—a ma ta da tuwon semo ta jera komai cikin kwando ta fito da shi.
Kamar yadda ya ce kar ta daÉ—e ba ta wani jima ba. Ta dai sa ma ta sauran miyan a fridge saboda miyan dayawa idan ba ta ma sa cin haÉ—ama ba zai kai ma ta sati...
"A'a miyake faruwa?" Zaytoonah ta faɗa tana taɓe baki.
Ɗakinta da ta bari a kimtse shine ta zo ta gan shi kaca-kaca. To ko da ma ace 'yan biyun ta na gidan da wuya ta zarge su kan aikata irin wannan taɓargazan dan ba halin su ba ne.
Tabbas wannan anyi ne da gangan kuma wanda yai yayi ne da gayya. Yaro ma ba zai yi wannan ba dan kayanta na saman closet É—in duk an watso ma ta da su waje.
Koma waye ne ba za ta yi magana ba dan abinda ake so ta yi kenan. Haka ta shiga gyara É—akin na ta. Abin takaici kusan fiye da rabin kayanta da ke goge duk yanzu sai an sake goge su. Akwai matar maigadin gidan Bahijje da ke shigowa tana yin aikin wanki da gugan kayan yaran da ma gyaran gidan amma tunda Zaytoonah ta zo da kan ta ta ke kai kayanta wajen washing machine ta wanke su sannan ta goge.
Kusan ita da ta yi booking da ta zo gida bacci za ta yi, sai da ta shafe fiye da awa ɗaya tana gyaran ɗaki ƙarshe ma ba halin baccin dan la'asar ta yi.
Kaman da wasa bayan kusan kwana huɗu da Zaytoonah ta dawo daga gidan maƙotan su da aka yiwa rasuwa wanda Justice ya ce ta shiga ta mu su ta'aziya. Shigowan da za ta yi ɗaki ta sake ganin an birkita ma ta ɗaki.
Yanzu kam ta tabbatar Raziya ce da wannan banzan halin. Zaginta da ta ke yi a fakaice ba ta tankawa yanzu kuma abin ya kai ga haka. Sai da ta gyara É—akin sannan ta fito ta nufi É—akin yaran.
Raziya na zaune gaban computer tana latsawa da alama dai assignment ta ke yi yayinda Suhailah ke bacci. Ba ta ga Falaq ba ƙila tana falo ko ma waje.
"Raziya na zo ne na faÉ—a miki cewa ya isa haka. Kin yi na farko kin yi na biyu to Wallahi kar a kuma maimaita na uku dan jikin ki ne zai gaya miki"
"To ni mi na yi? Idan ba mugunta ba mi na miki?"
"Ki kiyayi shiga hurumina Raziya dan Wallahi ba za ki ji da daÉ—i ba. Tam"
Daga haka ta fita daga É—akin. Yadda zuciyarta ke tafasa ma kamar ta kama Raziyan da duka ta ke ji.
Ta so gayawa Justice abinda Raziyan ke ma ta amma lokacin da ya shigo da dare sai ta lura kaman ran sa a ɓace ya ke dan ta ma sa maganar abinci ma ya ce ma ta ya ƙoshi.
Washegari kuwa Asabat bayan ta gama girkin safe ta shiga aikin cupcake ranan sun yi baƙi ba ta da komai na lasawa a baki idan ka cire dambun Kaza da ta ke yi duk sati saboda duk Jummu'a ana yanka Kaji a gidan kuma ranan ta yi Dambu da shi sai Justice ya ce ma ta ya ji daɗin dambun ta dinga yi yana so.
Sai da ta gama komai ta saka a cikin oven sannan ta haura sama dan ta san kafin ta je ta yi abinda za ta yi ta fito timer É—in da ta sa ba zai cika ba.