Sashe 55
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun iso gidan da aka umurce su su ka kira Alhajin da ya aike su, sai ga Alhaji ya fito fiska É—auke da farin ciki. Duk da jikin Maryam a sake ya ke bai hana Muntari iya É—aukan ta ba, ya wuce da ita cikin gidan yana É—auke da ita kamar Amarya. Kai tsaye kan gado ya kwantar da ita ya gyara ma ta kwanciya yana kallon kyakykyawar fiskarta.
Kusan minti Arba'in da kwantar da ita maganin da aka shaƙa ma ta ya saketa. Ta buɗe ido a hankali, tana ƙyafƙyafta idon saboda idon da ya ma ta nauyi. Kusan minti ɗaya kafin hankalinta ya kawo ma ta abinda ya faru lokaci guda ta tashi zaune tana faɗin Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun.
"Relax ni ne" ya faɗa yana ƙoƙarin zama a gefen gadon.
"Muntari, Muntari ka ji tsoron Allah. Ka ji tsoron Allah" sai kuma ta fashe da kuka dan ba ta san mi za ta faÉ—i ba bayan haka.
"Ki kwantar da hankalin ki dan ba abinda zan miki. Da ina son ki ta ƙarfi da tun ɗazu na yi abinda ki ke tsoron. Abu ɗaya na ke so Maryam, abu ɗaya tak shi zai sa na samu kwanciyar hankali kuma kema ki samu. Ki aure ni"
Idon ta cike da hawaye ta ce "Muntari dan Allah, indai ka yarda da Allah to ka rabu da ni, ka bar ni na koma wajen 'ya'yana. Muntari idan kana sona kamar yadda ka ke iƙirari to ka rabu da ni dan Allah"
Fashewa da dariya yai wanda ya ƙara tsoratar da Maryam. Lamarin Muntari kam ta tabbata ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa.
"Ba zan iya rabuwa da ke ba, ke tawa ce kuma ba zan taɓa haƙura ba sai na same ki. Idan a baya Tijjani ya min ƙwace to yanzu babu shi kuma ba zai taɓa dawowa ba idan ma wannan ki ke jira gara ki dena"
"Subhanallah! Muntari mi ka yiwa Mijina? Kashe shi ka yi? Mi ka mishi ?"
Bindigar da ya fito da shi ne ya sa ta yi shiru tana zare ido. Ba rayuwarta ba ne ya sa ta tsoro illa tunanin da ya dirar ma ta lokaci guda na cewa Muntari kashe ma ta Tijjani yai.
"Na sani yanzu ba abinda kika fi so sama da 'ya'yan ki. Idan ba ki amince da aure na ba tamkar kin kashe Salman da Sadiq ne da hannun ki"
"Muntari" ta faÉ—a murya a raunane
"Kashe su zan yi Maryam. Ba su kaÉ—ai ba har Zaytoonah. Ba a Las Vegas ta ke ba?"
Zuciyar Maryam bugawa ne kawai bai yi ba amma ta firgita matuƙa.
"Akan ki zan iya yin komai"
" Muntari ka yi haƙuri kar ka kashemin 'ya'ya, ka tuna fa su jinin ka ne"
"Zan baki zuwa gobe ki yi shawara ko ki aureni ko kuma kiyi sallama da 'ya'yan ki" ...
***
Abinda ta gani jiya bai sa ta iya cin abinci ba sai chan tsakar dare tana bacci yunwa ya addabeta ya tada ta dan haka ta sauko ta nufi kitchen fridge ta buɗe ko za ta samu abun ci ta buɗe fridge ta ɗau apple guda biyu ta fara ci tukunna kafin ta ga ragowan strawberry cake da ta ci ta rage da safe dan haka ta fito da shi ta hau ci tareda Madara, sai da ta ji ta ƙoshi kafin ta koma ɗaki ta je ta kwanta. Washegari makara ta yi ba ta tashi da wuri ba. Lokacin da ta tashi ta yi sallah ta yi wanka ta fito ƙasa sai ta samu Ben da Zuhayr suna karyawa. Hoton jiya kawai ta ke gani dan haka ta ja dogon tsaki ta wuce su.
Kitchen ta shiga ta samu Chef Green har ya gama aikin sa na safe yana gyara abinda zai yi amfani da shi da safe. Gaishe shi ta yi sannan ta fito da ƙwai huɗu da kifin gwangwani ta kunna wuta ta haɗa scramble egg mai rai da lafiya, ta ɗau bread ta zauna a kujeran kitchen ɗin ta fara ci bayan Chef Green ya ajiye ma ta tea a gabanta dan har yanzu ba ta iya dafa shayi irin na sa ba sai ta ce ya haɗa ma ta lokacin da ta ke kan haɗa ƙwan.
Tana cikin cin abincin ta tambayi Chef Green ko ya san alaƙar da ke tsakanin Ben da Zuhayr.
Chef Green ya ce ma ta kaman 'yan uwa su ke saboda tare su ka taso.
"Do you know that they are gay?" Ta yi tambayar tana kallon Chef Green.
"I dont know" ya amsa bayan yayi nazari.
"They are sleeping tog..." ƙarrarrawar kitchen ɗin yai ƙara Chef Green ya ce "excuse me" kafin ya bar kitchen ɗin dan ya san Zuhayr ke kira.
ÆŠaga kafaÉ—a ta yi tana faÉ—in "inma dukkan su jirgi É—aya ya kwaso su shikenan, dama America is a free country"
Bayan ta yi maganar sai tausayin Zuhayr ya kama ta dole ya ce ba za su yi mu'amalar aure ba tunda yanada matar sa Benedict a gefe. Sai yanzu ta ke gane ma'anar kallon da Ben ke ma ta ashe kallon kishi ne.
"Ka yi ta yi ni ba ruwana, karatu na zo yi kuma shi zan yi na tafi ba ruwana da mijin ka"...
Yau za ta je school har ta fito sai ta manta wayarta a É—aki za ta koma É—auka shi kuma sun fito za su tafi Office.
"Allah dai ya shirya" ta furta a fili tana haÉ—e fiska bayan sun yi ido huÉ—u da Zuhayr.
Har ta juya ta ji ya kira sunan ta "Zaytoon"
"Zan yi tafiya amma gobe zan dawo"
"Kai da za ka tafi da matar ka miye haɗin ka da ni. A je a shaƙata lafiya"
Tana faÉ—in haka ta wuce ciki da sauri...
A makaranta bayan ta sauka a mota ta fara tafiya sai ta ji ana yi ma ta magana
"Excuse me, Excuse me"
Ta juyo a hankali dan har yanzu ba ta da aboki a makarantar, iya kaci akwai wata Zoey 'yar ajin su da su ke É—an magana sama-sama haka.
"Ki yi haƙuri na tsaida ke, sunana Linda Cannel"
"Zaytoonah"
"Na ganki a wata mota mai lambar ZMI da alama ke 'yar uwar Mr Zuhayr ne?"
Zaytoonah ta gyaÉ—a ma ta kai.
"Ƙanwar shi ce ke?"
Nan ma ta gyaÉ—a ma ta kai.
Linda ta yi murmushi ta fito da katin ta ta ce "za ki iya kirana idan kina son bayani akan mutuwar Alinah"
"Waye Alinah?"
"Zuhayr's ex"
Kafin Zaytoonah ta yi wata tambayar sai ta juya ta tafi. Zaytoonah ta buɗe baki tana kallonta har ta ƙule ba ta bar kallon ta ba.
Har ta koma gida ba ta dena juyayin abinda ta ji yau ba Zuhayr's ex kuma ta mutu. Miya faru? Dama Zuhayr ba gay ba ne ko kuma dai daga baya ya zama?
Ta tambayi Chef Green ko ya san Alinah amma ya ce bai sani ba. Haka dai ta kwana da tarraradin maganar a ranta tareda tunanin gobe idan ta dawo daga School za ta kira Linda ta ma ta ƙarin bayani.
Washe gari a hanyar ta na dawowa daga school numbar Mommy ya kirata, ta yi saurin ƙatsewa ta kira zuciyarta cike da farin ciki. Maimakon muryan Mommy sai ta ji muryan Salman.
"Adaeze an sace Mommy"
"What? An sace Mommy kamar ya?"
"Tun jiya har yanzu ba mu ganta ba, Junior ya ce wani ne ya zo ya ɗauketa. An yi reporting a police station amma har yanzu ba a ganta ba" ya ƙarisa maganar yana kuka. Cikin kuka ta ke cewa ya kaiwa Ya Auwal wayan amma ya ce Auwal baya gida kuma ya hanashi ya gaya ma ta abinda ke faruwa.
Kuka ta ke yi har su ka iso gida Mr Smith ya tambayeta ko lafiya amma ba ta kulashi ba sai kuka.
Tana shiga É—aki ta É—au jaka ta fara haÉ—a kayanta tareda neman visa da credit card É—in da Zuhayr ya ba ta ta sa a jaka ta fito da gudu kamar wata zararriya.
A ƙofar gida ta samu Zuhayr yana sauraron bayanin da Mr Smith ke ma sa su ma isowan su kenan.
"Zuhayr an sace Mommy na gida zan tafi" ta ƙarisa maganar tana kuka.
"Relax Zaytoonah, ba inda za ki je, besides za ki fara exams jibi"
"To hell with the exams. My Mommy is missing, she's being kidnapped"
Ta kalli Mr Smith ta ce ya kaita airport. Za ta wuce shi ta shiga mota ya tare hanyar. "Ki kwantar da hankalin ki, mu shiga ciki tukunna" ta chanja hanya za ta wuce yai saurin jawota ta faÉ—a jikin sa.
"Ka sakeni na tafi, ka sake..." maganar ta kafe lokacin da ta ji bakinsa cikin na ta.
"Relax, ba abinda zai samu Mommy i Promise you" ya faÉ—a bayan ya raba kiss É—in. Mutuwar tsaye tayi a wajen dan maganan sa ma ba ji ta yi ba.
Ben ya dunƙule hannun sa da ƙarfi yana huci yayinda idanun sa su ka kaɗa su ka yi jaa...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 26
Bismillahir Rahmanir Rahim
*Alinah*
Kafin a tafi da Alhaji Muntari sai da aka yi drama sosai dan kuwa titsiyewa yai akan shi bai yi komai ba babu yadda za'ayi a arresting ɗin sa. Tanimu ya riga ya tona asirin akwai matar da Alhaji ya ajiye a gidan amma Muntari ya ƙaryata hakan.
Auwal da wani police ne su ka shiga gidan su ka duba inda su ka samu ƙofar ɗakin da Maryam ta ke a rufe, komawa su ka yi waje inda ake riƙe da Muntari yana zage-zage bayan anyi nasaran saka ma sa ankwa a hannu. Da su ka chaje shi sai su ka ɗauki key ɗin gidan su ka koma su ka je su ka buɗe Maryam. Auwal na ganin Mommy sai ya fashe da kuka, lokacin da Zuhayr ya ce ma sa yana suspecting ɗin Muntari bai yarda a zuciyar sa cewa ƙanin mahaifin na sa zai iya aikata irin wannan abu ba.