Sashe 58
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari sai gashi da sassafe a gidan wai ya zo duba lafiyar ta. Da tunanin ta ya kwana shiyasa ya kasa haƙura dole sai da ya zo ya dubata. Daga muryanta ya gane mura ya kamata dan haka ya ce ta zo su je asibiti a dubata amma ta ƙi. Wasa wasa sai gashi Zuhayr sai da ya kwashe kwana uku a jere yana zuwa yana dubata, a rana ta ukun kuma ya kawo ma ta takardar shaidar aiki wato ya dawo da ita aikin ta. Da farko ta ƙi amma bayan ya ba ta haƙuri sai ta amince ta koma.
Shikenan kuma alaƙar su ta ɗin ke daga lokacin. Time to time yana zuwa gidan ta su gaisa hakanan a office ma kusan kullum sai sun haɗu. Wannan chanji ya sa hankalin Ben ya tashi saboda zargin soyayya da ya ke yiwa Zuhayr da Alinah ɗin duk da kuwa Zuhayr ɗin ya ƙaryata hakan ya kuma nuna cewa tausayawa Alinah kawai ya ke yi saboda ba ta da kowa. A lokacin sallar Layya ne Alinah ta gabatar da Zuhayr a muslim community da ke Vegas wanda shi duk zamanshi a garin bai san da su ba. Yadda su ka yi hidimar sallah cikin farin ciki da soyayyar juna ya sa har ya ji shauƙin musuluncin ya dawo ma sa. Bayan angama hidimar sallah watarana da ya je gidan Alinah ya ke gaya ma ta yana so ya zama musulmin ƙwarai kamar ta dan baya damuwa da yin sallah akan lokaci, wasu lokutan ma bayayi ya ce ma ta Azumi ma kusan ya jima bi azumci duka Azumin Ramadan ba, idan yai ya gaji sai ya ajiye.
Wannan confession na shi ya sa Alinah ta dage akan sa ta hanyar koyar da shi musulunci ta kuma ƙarfafa ma sa gwiwa ya dinga zuwa ɗaukan karatu a wajen Sheikh Hassan Lewis. Cikin wata shida Zuhayr ya chanja sosai ya koma yana ƙoƙarin yin ibada yadda ya kamata. Harta sallar Jummu'a da bai taɓa zuwa ba idan ba lokacin da ya je Nigeria ba da kuma lokacin da ya je wajen Uncle Aliyu to yanzu tare su ke zuwa ma da Alinah. Shi bai ɗauka akwai babban masallaci ba ma a garin saboda bai damuba.
A wannan yanayi na shaƙuwa ne soyayya mai ƙarfi ta shiga tskanin su wanda bai gane hakan ba sai ranan da Sheikh Hassan ke ma sa tayin auren Alinah.
Tun bayan maganar da su ka yi da Sheikh sai ya kasa samun nitsuwa yana tsoron kar ya yiwa Alinah magana ta ƙi shi dan akwai wani ɗan India Faisal Khan da ya ke gani yana shishshige ma ta wanda lokuta da dama idan ya gan su tare ya kan ji baƙin ciki a ran sa ashe kishi ya ke bai sani ba.
Bayan ya yi shiru da zancen yana jiran Perfect time da zai gaya ma ta ƙwatsam sai gashi Alinah ta ma sa maganar wai ya ba ta shawara Faisal Khan ya ce yana son aurenta.
Zuhayr ya harzuƙa matuƙa ya nuna shi ba ruwan sa rayuwarta ne tayi duk abinda ta ke so. Daga haka sai ya janye jiki da ita ya dena kulata. A kwana na biyar sai gashi bayan sallar jumu'ah sheikh ya sanar da cewa ƙarshen wata za ayi auren Faisal Khan da Zarah Ayyub Shahid. Sai a lokacin zuciyar Zuhayr yai sanyi ya kuma ji kunyar kan sa na fushin da yai da Alinah.
Text ya tura ma ta yana ba ta haƙuri ita kuma ta ma sa reply da cewa idan bai fito da abinda ke zuciyar sa ba akwai single guys dayawa a muslim community. Yai dariya bayan ya karanta saƙon kafin ya tura na ta reply da cewa abinda ke zuciyar sa a bayyane ya ke a fiskar sa makaho ne kawai ba zai gani ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci su ka fara gudanar da soyayya mai tsabta, a lokacin ne kuwa Alinah ta bawa Zuhayr labarin rayuwar ta inda shi kuwa yai ma ta alƙawarin zai kula da ita har ƙarshen rayuwar sa.
Wata biyu aka sa auren su kafin lokacin Zuhayr ya gama shirya komai, ya kai ta gidan Uncle ɗin sa sun gaisa da shi da iyalen sa. Ya shirya mu su tafiya immediately bayan anyi auren su, za su fara zuwa Nigeria su yi sati biyu kafin su wuce Saudiyya su yi Umara. Sai dai kafin wata biyun su cika abubuwa da dama sun faru wanda ya kai daga ƙarshe Alinah Amir Jones ta rasa ranta.
Ƙaramar hauka Zuhayr yai lokacin da Alinah ta rasu musamman da aka tabbatar da cewa kashe kan ta tayi, mutane da dama ba su yadda Alinah za ta iya kashe kan ta ba tunda ba ta da matsalar komai amma bisa report da aka bayar Alinah ta kashe kan ta ne saboda matsalar ƙwaƙwalwa tunda lokacin da ta ke ƙarama ta yi fama da ciwon damuwa, sai ake ganin kamar auren da ta ke son yi ne ya haddasa ma ta da damuwa har ciwon ta ya dawo. Haka aka rufe case ɗin da cewa Alinah Amir Jones commited suicide...
Alinah Amir shine asalin sunan ta, iyayen ta 'yan ƙasar Palestine ne wanda sanadiyyar yaƙi ya sa ta rasa mahaifinta da babban Yayan ta. Ita da mahaifiyarta su ka yi gudun hijira daga Palestine zuwa America. Da farko a wani refugee camp su ke a ƙasar Jordan daga baya su ka samu wani yai mu su hanya su ka isa ƙasar America akan Sarah mahaifiyar Alinah za ta isa wajen Ƙanin Baban ta wanda ya jima da komawa America da zama da daɗewa. Da ƙyar ta samu ƙanin Baban na ta bayan sun sha gararin rayuwa, shima dai ba wani abun azo a gani ya ke da shi ba amma ya karɓesu hannu bibbiyu.
Alinah na da shekara shaɗaya wanda ya kama wata shauku kenan da zuwan su America aka ma ta fyaɗe, not just fyaɗe kawai gang raping ɗin ta aka yi har mutum uku. Wasu taƙadarun mutane ne abokanan aikin Hammad wanda su ka samu sa'insa da shi a wajen aiki har ta kai ya kai su ƙara wajen Ogan su, Ogan ya ba wa Hammad gaskiya. Shine su ka yi alƙawarin muzguna ma sa, ɗan sa ɗaya da ya ke da shi ba sa tare saboda shima yanada na sa iyalin a can garin Detriot. Shine su ka nemi tarwatsa rayuwar jikar sa Alinah.
A yashe aka samu Alinah bayan an jima ana neman ta. Wanda su ka sameta ne su ka je su ka faÉ—awa Hammad bayan an kira ambulance sun tafi da Alinah wacce har lokacin ke sume.
Hammad da matar sa Nadeem da kuma Sarah mahaifiyar Alinah ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba da jin abinda ya faru da Alinah. Ko jini ba ta fara ba lokacin da aka ma ta fyalen.
Tunda Alinah ta buɗe ido a asibiti ta rikice ta fara zabure-zabure musamman da ta ga likita namiji akan ta, sai da aka haɗa da yi ma ta allura kafin ta nitsu. Kusan watan su ɗaya a asibiti kafin aka sallameta ba wai kuma dan ta gama warkewa ba. An dai ma ta taimako na gaggawa an gyarata amma matsalarta ta zabura da firgita har lokacin da saura sun ce a kaita psychiatric saboda anan za a bata kulawa dan matsalarta ta ƙwaƙwalwa ce.
Hammad ya shigar da ƙara amma rashin shaidu ma su ƙarfi da kuma kasancewar sa Musulmi ya sa aka yi watsi da ƙaran. Ga shi dai suna da report na fyaɗe daga Asibiti amma haka aka wanke sunan Bradley, Fred da kuma Austin.
A wannan yanayi ne Yusuf ɗan Hammad ya ba su shawaran su nemi wani Lawyer da ake kira da David Jones ko zai taimaka mu su dan yayi ƙaurin suna wajen kare hakkin bil'adama musamman ƙananun yara, an shaide shi da gaskiya da kuma amana, a cikin aikin sa baya banbanta yare, addini ko kuma kalar fata.
Sai da su ka jera sati biyu suna neman ganawa da shi amma ba su samu ba saboda mutane da ke ma sa yawa a sati na uku suka samu daman ganawa da shi.
Sosai ya ba su mamaki lokacin da ya ce zai wakilce su a sake ɗaukaka ƙara.
Abu na farko da yai shine ya adopting Alinah a matsayin 'yar sa, bayan ya gama yin duk wani legal documentation kafin ya shigar da ƙara akan fyaɗe da aka yiwa 'yar sa Alinah. Nan da nan aka fara shari'a, aka shiga aka fita har dai David Jones yai nasara inda aka yankewa mutanen nan uku hukuncin ƙare rayuwar su a gidan yari.
Ba tareda ko sisin su Hammad ba David Jones ya kai Alinah psychiatric aka fara kula da ita. Warkewanta was a very slow process dan kafin Alinah ta fara yadda namiji ya zauna kusa da ita ma sai da aka fi shekara ɗaya. Shekaranta uku ana kula da ita kafin aka sallemeta amma duk sati za ta dinga zuwa tana ganin likita. Sai da aka yi shekara huɗu cur da maganan fyaɗe kafin ta iya komawa makaranta da ke ance chanja muhalli zai sa ta samu saurin warkewa ya sa David Jones ya tafi da ita Michigan inda a nan ma aka yi ta treating ɗin ta. David da matar sa Helen sun riƙe Alinah da amana tamkar 'yar da su ka haifa a cikin su, 'yar su ɗaya Anna amma ta mutu tun tana ƙarama kuma ba su sake samun haihuwa ba. Ba su damu da cewa Alinah musulma ba ne su kuma christain infact David ke kaita masallaci duk Jummu'a kuma ya kaita makarantar da ake koyar da karatun musulunci sau huɗu a sati. Bayan an samawa mahaifiyar ta Sarah aiki sai ya zamana itama ta dawo Michigan da zama inda ta cigaba da kula da 'yar ta. Lokacin da Alinah ta shiga Jami'a ne David Jones ya mutu bayan an halbeshi sau uku da bindiga a office ɗin sa.