← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 161

Sashe 139

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bacci ne ya kwashe su bayan sun yi wanka a karo na biyu. Ƙarfe biyun dare Zaytoonah ta tashi daga bacci za ta shiga banɗaki ta ga wayar Galadima na haske ashe dai a silent ya saka ta. Ɗaukar wayar ta yi sai ta ga anyi saving da suna *Gimbiya Ghazala*
Wani abu ne ya soketa amma ta dake ta ɗau wayar dan tunda bacci ne ta kasa yi gara ta hanata baccin mai dalili. Ƙasa-ƙasa ta fara magana bayan ta ɗauka kiran.
"Lafiya kika kira da dare haka?"

Daga ɓangaren Ghazala ta ji wani abu ya toshe ma ta maƙoshi, maganar da ta ke son yi ma ta ka sa. "Idan a Nigeria dare bai yi sosai ba plz ƙarfe biyun dare ne a nan. Ki bari gobe ki kira shi, you are interrupting a very private meeting a nan"
Ta kalli Galadima da ke bacci hankali kwance kafin ta maƙe murya cikin kissa ta ce "Sayyidi ka ɗan matsa min wajen nan, Oh Oh Oh"

Tuni Ghazala ta yi cilli da wayar hannunta tareda saka ihu. Tun tana ƙuruciya ita mai kishi ce ko aurenta na farko maganar kishiya na daga cikin babban dalilin da ya sa ta bar gidan, balle yanzu da ta ke auren Galadima.
Yanzu duk abinda ta shirya ya warware kenan? Ko dai shawaran Hajiya Safara'u za ta É—auka ne? To amma ita gaskiya duk iskancinta ya tsaya a kissa da munafurci ba ta yadda da zuwa wajen boka ba.

A ɓangaren Zaytoonah kuma dariya ta yi sannan ta duba wayan ta ga missed calls ɗin Mommy har uku. Kiran wayan ta yi amma ba a ɗauka ba dan haka ta ajiye wayar ta shige banɗaki.

Bayan ta fito ne ta sake gwada kiran wannan karan aka É—auka amma da muryan bacci.
Kasa magana ta yi dan kunyan Mommyn ta ke ji.

"Ina fata dai ki dawo da sassafe dan baifi awa É—aya da ya wuce ba ta yi bacci"

"Ki yi haƙuri" ta faɗa a kunyace

"Mu kwana lafiya" Mommy ta faÉ—a tareda katse kiran.

Zaytoonah ta yi ajiyar zuciya kafin ta wajen Galadima ta kwanta gefen sa ta ɗaura kan ta a ƙirjin sa...

Washegari tun ƙarfe huɗu da rabi da su ka tashi su ka shirya su ka bar hotel ɗin. Taxi su ka shiga su ka wuce gida. Suna zuwa kuwa da Zaytoonah ta haura sama ta samu Mommy na faman lallaɓa Alinah da ke kuka, dama aikinta ne kuka dai-dai lokacin Asuba. A kunyace ta karɓi Alinar a hannun Mommy ta zauna ta shiga ba ta nono...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 69

Bismillahir Rahmanir Rahim

*face to face*

"Sati É—aya?" ta maimaita abinda ya faÉ—a.

"Akwai tarin ayyuka agabana ne Qurratul ayn"

"Hmm" kawai ta ce sannan ta cigaba da zuba ma sa abinci.

Ganin ta haɗa rai ya sa shi riƙe hannunta ya ce "zan so jimawa a nan amma kin san ba zai yiwu ba. Infact Monday munada zama a kotu.

"Ki yi haƙuri kin ji. Zuwa ƙarshen watan nan sai kema ki dawo"

Kallon shi ta yi na 'yan daƙiƙu kafin ta cigaba da abinda ta ke yi. Bayan ta gama zuba abinci ta zauna gefe ba ta ce komai ba. Tana son yi ma sa magana amma kuma wani abu ya tokare ma ta wuya, kuka ta ke son yi amma ta kasa.

"Adaeze ki yi haƙuri Dan Allah. Wallahi da akwai yanda zan yi na zauna a nan kamar na wata ɗaya da zan yi. Kin san..."

"Dan Allah Daddyn Raziya ka bari haka. Na ji za ka tafi nan da kwana uku shikenan Allah ya kaimu lokacin"

Ta miƙe za ta fice daga ɗakin yace

"Ina za ki je?"

"Zan duba Alinah ko ta tashi"

"Dawo ki zauna"

Maimakon ta koma sai ga hawaye sun fara zubowa a idonta. Kukan da ta ke ta dannewa shine ya kufce ma ta.

"Subhanallahi!" Galadima ya faɗa yana miƙewa da sauri.
Yana rungumota jikinsa sai ta fashe da kuka da ƙarfi.

Su biyu ne a gidan sai masu aiki. Mommy ta kwashi yaran sun fita ganin gari.

"Ki daina kuka dan Allah. Ba yanda zan yi ne Zaytoon, try to understand me please"

"Kinga duka yaran suna nan tare da ke. Sai hutun su ya ƙare za su dawo, idan za su dawo sai ku dawo tare"

"Ni ma kin san ba ƙaramin missing ɗin ki zan yi ba. Kinga daga wannan tafiyan idan kin dawo sai kin shekara ba ki taka ko ƙofar gida ba"

Hararan sa ta yi ta ce " sai ka yi mu gani ai"

"Ikon Allah! Mai kuka na harara ne" ya faÉ—a yana dariya. Zaytoonah ta kai ma sa dundu a baya.

"Yallaɓiya ki yi haƙuri kar ki ɓurma bayan Tsoho"

"Gara na ɓurma ɗin ai tunda nawa ne" ta faɗa tana ƙara yi ma sa wani dundun a bayan sa.

Tuni faɗa da lallashi ya juye ya zama soyayya. Tare su ka ci abinci cikin so da ƙauna dan kowa na bawa ɗan uwan sa abincin ne a baki a haka aka ƙarisa cinyewa...

Washegari su ka tattara su ka wuce gidan gonan Kakannin Zuhayr wato *Haddish Ranch* Tun kafin mutuwar Mrs Haddish ta mallakawa 'yan biyu gidan gonan gaba É—aya wanda ya sauya suna zuwa *Zuhayr Ranch*.

Su Raziya sai su ka koma 'yan ƙauye ganin kyan wajen, shi kan sa Galadima wajen ya burgeshi sosai. Dawakai, Shanu, Raguna, Kaji, ga su nan birjik a wajen suna samun kulawa daga ma'aikata.

Zuwan su gidan gonan ya taɓowa Zaytoonah tsohon tabo da ta ke fama da shi a zuciyarta tun da jimawa. Lokacin da su ka shiga gidan gani ta ke kaman za ta ga Zuhayr da kuma Kakannin sa a ciki. Da ke sun sanar da zuwan su an riga an gyara mu su cikin gidan. Ɗakuna uku ne a gidan dan haka Mommy ta ce Galadima da Zaytoonah su ɗauka master bedroom ɗin yayinda ita kuma za ta kwana tareda junior da 'yan biyu.
Su Raziya kuma aka ba su É—aki É—aya.

Bayan sun huta ne Zaytoonah da Manager É—in gidan gonan mai suna Muhammad Chu suka yiwa su Galadima jagora wajen ganin ilahirin gidan gonan.

Dukiya ne jingim a wajen nan, kuma Alhamdulillah duk da kasancewar Zaytoonah ba ta wajen hakan bai sa anyi wasa da kula da lamuran wajen ba. Tun da Zaytoonah ta ɗauki Muhammad Chu a matsayin manager abubuwa suka rinƙa haɓaka sosai. Duk da kasancewar sa mutum ne da bai wuce shekara biyu da ƙarɓan musulunci ba amma kyawawan halayen sa idan ka gani sai ka ɗauka ma tun asali a cikin musulunci ya taso. Muhammad Chu asalin su 'yan Hong Kong ne amma kasancewa iyayen sa a nan ƙasar America su ka haifeshi ya ba shi lasisin zama ɗan ƙasa. Saurayi ne da zai kai shekaru talatin da huɗu a duniya.

Zaytoonah na tsaye tana kallon Galadima na ƙoƙarin ɗaura Junior akan doki tana murmushi ganin yadda Galadima ke nunawa 'ya'yan ta da ƙaninta kulawa. Tunda su ka zo wajen dawakai 'yan biyu su ka ce sai sun hau doki dan haka dole Galadima ya ɗaura su akai.

Sai da ya zauna akan dokin sa sannan ya juyo ya kalli Zaytoonah ya ma ta wani murmushi mai sanyi.
Zaytoonah ta yi saurin dafe ƙirjin ta saboda abinda ta ji daga chan ƙasan ran ta. Wannan murmushi a kullum idan yai, duk da ma bai cika yin ba sai yana cikin tsananin farinciki tuno ma ta ya ke da Zuhayr.
Galadima ya ja linzamin doki ya yi gaba cikin sassarfa, su junior ma su ka bi bayan sa a hankali.

Su Falaq da Suhailah kuma sai tafi su ke yi cike da farin ciki.

Raziya da ke gefen Zaytoonah ta ce "Anty ina idan za mu koma Nigeria tare za mu koma da ke ko?"
Tambayar nan ta ji shi a wajen Suhailah tun ranan da su ka zo amma yanzu da Raziya ta faɗa sai abin ya ba ta mamaki. Ta lura tunda su ka zo ta ke ƙoƙarin shishshige ma ta musamman idan ta ɗauki Alinah sai ta ce a bata ta goyata. Babu wannan rashin kunya da tsiwa ɗin nan da ta ke ma ta a da.
Tunanin ta ko dan sun jima ba su haÉ—u ba ne ya sa ta chanja haka.

"Allah mun missing ɗin ki sosai. Kinga ranan sunan Alinah nima har walima na yi, na gayyaci duk ƙawayena kuma kusan dukkan su sun zo. Har wanda ba su zo ba da na je school sai da na raba mu su souvenir ɗin suna"

Cike da mamaki ta kalleta ta ce "kina so na dawo ne?"

"Sosai ma kuwa. The house is so boring without you"

"Wallahi kuwa" Falaq ta jaddada wanda itama ta ji abinda Raziyan ta faÉ—a.

Zaytoonah ta ce " kuna tareda Hajiya taya gidan zai zama boring?"

"Hajiya ta chanja. Ta dena kula damu har dukan mu tana yi yanzu" Falaq da ba ta cika son magana ba ita ke wannan bayani hakan ya sa Zaytoonah ta gane lallai da gaske yaran ba sa jin daÉ—in zama da Ghazala.

Dama tuntuni ta suspecting zaman munafurci ta ke yi da yaran, duk wani abu da ta ke yi mu su tana yi ne dan samun wuri a wajen Galadima ba dan Allah ba.

Kafin ta yi magana ta jiyo muryan Farha tana ƙwala sunan ta.

Kamar wata yarinya haka ta taho da gudu ta rungumeta saura kaÉ—an ma ta kayar da ita.

"Ya Allah! Zaytoonah ke ce haka?. My Gosh na ga Baby Alinah a wajen Mommy, ashe ta fi hoto kyau. Kai i'm dying to have a cute baby like her. Oh! She's so pretty"

"Ke dai ba za ki girma ba Farha. Yanzu yadda ki ka daka tsalle kika faÉ—a jikina idan kika jimin ciwo fa"

"Forget it Babe. Da na shigo na ga wani handsome man a waje, who is he?"

"Kai Farha!"

"Ok Ok Ok. Yanzu Ina 'ya'ya na su ke?"

Juyar da fiskar Farha ta yi wajen su Raziya ta ce " ga 'ya'ya na nan. This is Raziya, Falaq and my sweetheart Suhailah"
Chapter 139 · 0% Book details