Sashe 140
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farha ta miƙawa Raziya hannu su ka gaisa sannan ta bi sauran ma ta mu su musabaha tana faɗin sun ma ta kyau.
A hanyar su ta komawa gidan ne Zaytoonah ta tambayeta ya aka yi ta san suna nan?. Farha ta ce ta je gidan su na Las Vegas ne mai aikin su ta ce sun taho nan shine kawai ta wuco nan É—in.
Lokacin da su Galadima su ka dawo Zaytoonah ta gabatar ma sa da Farha. Farha sai murmushi ta ke yi tana ƙifƙifatawa Zaytoonah ido. Bayan sun keɓe kuwa ta dinga tsokalarta akan wai yadda Galadima ya ke da kyau da kwarjini ya sa ta kasa rabuwa da shi tun farko.
Da dare aka haÉ—a wuta a waje ana shan É—umi. Galadima, Zaytoonah, Farha da sauran yaran suma su ka fito shan É—umi, idan ka cire Mommy, Baby Alinah da kuma Hashir da ya riga yai bacci su kaÉ—ai ne ba su fito ba. Aka haÉ—u aka zagaye wutan aka zauna tareda ma'aikatan wajen ana hira. Daga baya kuma da dare ya fara ja Galadima ya ce su shiga ciki ya isa haka.
Farha kam maƙalewa Muhammad Chu ta yi tana ma sa tambayoyi gameda rayuwar sa. Duk da shi ba mai son yawan magana ba ne amma duk da haka sai da ta sa shi yai ta biye ma ta. Kafin su rabu kusan tarihin rayuwarta kaf ba wanda ba ta gaya ma sa ba.
Kasancewar ba wani ɗaki a gidan Farha a falo ta kwana a saman couch kusan ƙarfe shabiyun dare bayan ta baro wajen Muhammad Chu, dan sai a sannan aka kashe wutan da aka kunna...
Haka su ka yi kwana biyu a gidan gonan nan cikin jin daÉ—i da kwanciyar hankali. Anyi hotuna kuma an yi videos na tarihi. Su Raziya har cewa su ka yi kafin su tafi za su kuma komawa gidan gonan.
Ranan Alhamis Zaytoonah ta raka Galadima zuwa airport inda su ka rabu cike da kewar juna. Ita dai Zaytoonah ba ta bashi tsayayyiyar amsa ba amma sun rabu akan kafin hutun su Raziya ya kare za ta tsaida ranan dawowan ta...
***
Tun ranan da Ghazala ta yi waya da Zaytoonah ta rasa nitsuwarta. Gidan da ta ke tunanin ya zama mallakinta ita kaÉ—ai ashe duk shirme ta ke yi.
Wani mahaukacin kishi ke cin ta. Duk inda ta auna yadda yanayin zaman su zai koma idan Zaytoonah ta dawo sai ta ga ita ce da faɗuwa. Sai dai koma yanene ba za ta bari wannan ƙaramar yarinyar ta sata cikin damuwa ba. Babban damuwarta shine ta samu ciki idan ta samu ciki komai zai zo ƙarshe musamman ta haifi namiji.
Akwai lokutan da shaiɗan ke kawo ma ta shawaran zuwa wajen boka kamar yadda wata ƙawarta ta shawarceta amma kuma idan ta auna abun sai ta ga duk ba riba a ciki. Cikin hikima za ta san yadda za ta yi Zaytoonah ta bar gidan gaba ɗaya.
Lokacin da Galadima ya dawo da farko Ghazala shareshi ta yi ita a dole ta yi fishi tana so miji ya lallaɓeta amma sai ta ga gogan ko kallo ba ta ishe shi ba balle ma ya lura cewa wai fushi ta ke da shi. Ganin kwana huɗu ya shige a haka ya sa ta chanja tsari dan wannan ba zai ficceta ba. Kafin Zaytoonah ta dawo ya kamata ta wanke duk laifukkan ta a wajen Galadima. Ranan jummu'a ta sameshi a ɗaki ta tsugunna a gaban shi tana kuka wiwi tana bashi haƙuri. A yadda ta ke yi ka ɗauka tsakani da Allah ta yi nadama ne.
Da kan ta ta sanar da Galadima cewa ta yi kuskuren dukan ma sa yara da ta ke yi idan su ka yi laifi. Ita tana yi ne dan su rage sangarta.
Ta ce ya yafe ma ta ihu da ta dinga yi ranan da za su tafi, wai kishi ne ke cin ta. Tsakanin miji da mata sai Allah, tuni Galadima ya ce ya yafe ma ta dan ta bashi tausayi irin kukan da ta yi ta yi mai É—imbin nuna nadama...
A chan ɓangaren Zaytoonah kuwa zuwan Galadima ya kwaɗaita ma ta komawa gidan ta. Kafin sati ukun da su Raziya za su yi ya ƙare ta gayawa Mommy akan za ta koma Nigeria. Mommy ta yi na'am da hakan dan dama abin da ya kawo su sun samu. Zaytoonah ta samu lafiya Masha Allahu. Itama kuma Baby Alinah ta yi ƙwari yanzu.
Sanda ta gayawa Galadima desicion ɗin ta kamar ya jawo ranakun haka ya dinga ji. He's very happy. Gashi gidan da ya siyawa Zaytoonah an gama gyaran shi an saka furnitures da komai da komai na buƙatan gida.
Haka nan su ka shiga tattara kayan su dan dawowa gida Nigeria...
***
Ranan talata da safe jirgin su Zaytoonah ya iso Abuja. Abun mamaki Galadima da kan sa ya je É—auko su da shi da Dreban su Raziya.
Da su ka isa gida kuwa Ghazala tana zaune tana jiran su. Ta riga ta sa an shirya mu su abinci kala-kala na welcoming É—in su.
Lokacin da ta ga Mommy ɗauke da jinjira ta nufi wajen ta da sauri ta karɓeta jiki na ɓari tana faɗin "ka ga Gimbiya Alinah 'yar America. Kai yarinyar nan kamanta da Falaq har ya ɓaci. O'o sai manyan ido kamar na uwarta. Baby Baby" ta ƙarisa maganar tana ɗan jan kumatunta yarinya kuwa ta saki kuka.
Zaytoonah ido kawai ta zubawa Ghazala tana ganin yadda ta ke jagwalgwala ma ta 'ya.
Jin ta ƙi shiru ya sa Mommy ta karɓeta a hannun Ghazalar.
"Ku ƙarisa ciki ku ɗan watsa ruwa yanzu za'a serving abinci"
Mommy ta ma ta godiya yayinda Zaytoonah ta riga ta wuce gaba.
"Mommy ki ga yadda ta ke yiwa Alinah, Wallahi idan ta kuskura ta yiwa 'ya ta wani mugun abu sai na kasheta..."
"Wani irin magana ne wannan? Ba na so, ba na so kin ji"
"Amma Mommy matar nan..."
"Ki cigaba da haƙuri da ita a hankali sai ki ga watarana duk wannan ya zama labari"
Zaytoonah dai shiru ta yi amma tsaf ta shirya yin faÉ—a da Ghazala idan wani abu ya samu 'yar ta.
Washegari Mommy ta wuce Zaria tareda 'yan biyu da Junior cike da tsaraban mutanen gida.
Zaytoonah na tsaye tana faman yanka albasa a chopping board Ghazala ta shigo kitchen ɗin. Tsayawa ta yi tana kallon Zaytoonan ciki da bai. Ta ƙara haske sai sheƙi jikinta ke yi. Tunda su ka zo ma sai yau ɗin ne ta ma ta kallon ƙurilla.
Ganin kallon yayi yawa ya sa Zaytoonah ta É—ago ta ce " Malama dan Allah kallon ya isa haka, kar ki cinye kurwata"
Murmushi Ghazala ta yi ta ce "Zaytoonah kenan! Ashe da gaske kin samu lafiya. To sannu da dawowa ko"
Kallon tuhuma Zaytoonah ta bi Ghazala da shi har ta ɗauki bowl ɗin kankana da aka yanka ƙanana a fridge ta fice daga kitchen ɗin.
Maganar Raziya ne ya faÉ—o ma ta ranan da su ke shirin barin Las Vegas.
*"Anty idan mun koma ki yi hankali da Hajiya. Ba ta son ki, ba fa son ki da Daddy"*
Ta tambayeta dalilin yin wannan magana ammaba ta ce komai ba amma kaman akwai abinda ta sani ta ke ɓoyewa.
2/11/21, 10:04 PM - ****: 70
Bismillahir Rahmanir Rahim
*Trial of my marriage*
Ƙarfe tara saura kwata na dare agogon ɗakin Zaytoonah ya nuna. Ba ita ke da girki ba dan haka bayan ta fito daga wanka kayan bacci kawai ta saka ta zauna a kujera tana duba wasu documents da Mommy ta ba ta. Takardu ne na filin da aka siya a ƙauyen su Mommyn, tun ma kafin tafiyar su America.
Bayan ta gama abinda ta ke yi ta miƙe ta tattara takardun ta sa a file ta maida shi cikin drawer. Falon ƙasa ta wuce dan ta taso Yaran akan su je su kwanta dan karfe tara ne lokacin baccin su. Hadid kam sai da ta ja shi da ƙarfi dan maƙalewa yai a jikin kujera saboda film ɗin spiderman da su ke kallo.
Sai da ta tabbatar da duka yaran sun kwanta kafin ta wuce falon Galadima. Tun takwas Alinah ke wajen sa ƙila ma ta yi bacci gara ta ɗauko 'yarta kafin Ghazala ta fara bala'in za a hanata jin daɗi.
Sai da ta kwanƙwasa ƙofar falon kafin ta shiga da sallama.
Yana kishingiɗe aƙasan carpet yana duba takardu.
"Sannu da aiki" ta faÉ—a ma sa sannan ta fara waige-waigen inda za ta ga 'yar ta.
"Ba dai ka kwantar da Alinah a É—akin ka ba?"
"Tana wajen Ghazala"
"Ghazala?"
Ya É—an É—ago ido ya kalleta.
"Ranka shi daÉ—e Ghazala fa. Ni gaskiya ba na so"
"Zaytoon"
"I'm serious ba na so. Idan ka É—au waya ka kirani na zo na É—auketa ai ba laifi ba ne"
Bai yi magana ba sai ya maida hankalin sa kan takardun da ke gaban sa.
Buɗe ƙofa aka yi Ghazala ta shigo goye da Alinah.
"Dear ai na gaya ma ka kashi ta ke ji shiyasa ta ke kuka"
Zaytoonah ta kalli Ghazala sannan ta maida dubanta ga mutumin da ya ajiye su duka.
Ta ƙarasa gaban Ghazala ta ce "Madam sauko min ita ko"
"Ta riga ta yi bacci ki barta kawai a wajena" Ghazala ta yi maganar tana satar kallon Galadima, ga shi dai takardun gaban sa ya ke kallo amma hankalin sa na kan matan na sa.
"Ki sauko min 'ya ta" Zaytoonah ta faɗa da ɗan ƙarfi.
Ghazala ta marairaice murya ta ce "yau da ban taɓa haihuwa ba da sai na ce gori kike min. Amma nima Allah ya bani biyu kuma har yanzu ban cire rai ba. Kar ki manta ɗa dai na kowa ne"
Zaytoonah ba ta ce ƙala ba ta karɓi 'yarta ta fice daga Falon ranta a ɓace. Ta rasa yaushe matar nan za ta dena shishshigi.