Sashe 151
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Galadima ya sake tura ma ta text har sau biyu amma babu wanda ta ma sa reply. Ba ta san mi za ta faɗa ma sa ba. Ta dena jin haushin sa amma kuma ta kasa samun ƙarfin gwiwar tura ma sa reply.
Abinda Salman ya gaya ma ta ya birkitata to the core, a wani ɓangare kuma tana tuhumar kan ta da miyasa ba ta yiwa Galadima uzuri ba a lokacin da komai ya shige ma ta duhu? Miyasa ta yi tunanin Galadima zai iya walaƙantata a karan kan sa?. Shin ba ta yarda da soyayyar da ya ke ma ta ba ne ko kuma dai ta ɗauka har abada rayuwar su zai tafi cikin jin daɗi ba tareda matsala ba ne.
A lokacin she ought to fight for him, for herself, amma ba ta yi ba. She was too angry, too jealous to think straight.
Da dare kafin ta kwanta da Mommy ta kawo ma ta Alinah sai da ta ma ta nasiha kan haƙuri da juriya a gidan miji.
"Idan har ba za ki iya haƙuri ba, idan har ba za ki iya jurewa ba to ba lallai auren ki yai ƙargo ba. Ko da kuwa yayi to ba lallai ki samu ladan da ake samu na haƙuri ba.
Akwai lokutan da za ki dinga ji a ran ki miyasa ma kika yi aure, miyasa ki ka auri wannan mutumin da ke cusa mi ki baƙin ciki son ran sa. Miyasa za ki ma sa biyayya bayan shi ba ya miki adalci.
But then, kar ki manta da cewa daga ƙarshe ba yardar shi ki ke nema ba, daga ƙarshe ba sakawar sa ki ke so ba. Ba wai dan ya zauna da ke ke ɗaya ba, ba dan ya zama tamkar bawan ki ba.
Abinda ki ke so da haƙurin ki a wannan aure shine ranan gobe, bayan babu ke a duniya, bayan rai ya fita ya bar gangan jikin ki da ke fankololo a cikin ƙasa. k
Kina fatan a ranan da aka yi hisabi aka nuna miki ladan sallah da sauran ibadun ki sai Allah Maɗaukakin Sarki ya ce 'wace 'yar wace, kin auri wane ɗan wane lokacin kina duniya. A rayuwar auren ku kin yi haƙuri dayawa saboda NI, kin jure saboda NI, kin yi biyayyar aure saboda NI' sai Allah ya saka mi ki da abinda idanu ba za su iya aunawa ba, ya saka mi ki da daraja a gidan Aljannah.
Kowa da tashi kalar jarrabawar Zaytoonah. Ba kuka za ki yi ba, sai dai ki dinga godewa Allah da ya ke kareki a kowanne lokaci. Ki cigaba da addu'a kawai Insha Allahu ba abinda zai sameki"
Murya a sanyaye Zaytoonah ta ce "thank you Mommy"
***
Washegari su ka tarkaÉ—a su ka wuce Ringim inda T J ya je gida ganin 'yan uwan sa. Irin farin cikin da su ka tsinci kan su a ciki ba zai misaltu ba.
Kwanan su huɗu a Ringim su ka dawo Zaria, har lokacin Zaytoonah ta ƙi ɗaukan wayan Galadima dan kunyar sa ta ke ji. Ba ya gajiya da tura ma ta text every now and then, duk text ɗin da ya turo sai ta karanta ya fi sau goma.
A wani rana da Mommy ta tambayeta yaushe za ta koma gidan ta cewa ta yi wai ba ta gama ganin Daddyn ta ba. Mommy ta zuba ma ta ido tunda ta ga T J ma goyon bayan Zaytoonan ya ke.
Bayan kwana uku da dawowan su daga Zaria Ummi (Pendo) ta zo daga Bauchi.
Zaytoonah ta fito daga kitchen kenan ta tsinkayi muryan Ummi na yiwa Mommy bayanin wani haÉ—i da ta kawo ma ta.
"Mommy, Mommy, wannan haÉ—e-haÉ—en an kusa shiga Azumi fa"
Zaytoonah ta faÉ—a lokacin da ta sako kai falon.
Mommy ta É—au remote ta wurga ma ta, Zaytoonah ta kauce tana dariya.
"Ummi ina nawa haÉ—in?, anyi wa tsohuwa an manta da ni"
"Ki fita a idona Zaytoonah" Mommy ta faÉ—a tana nunata da yatsa.
" Ai sai dai ki yi haƙuri idan kin haihu sai ki zo na gyara ki. Haiwuwar Alinah ba abinda aka mi ki na gyara, gashi kuma du kin ɗauko wani cikin"
"Nifa ba ni da komai, ba ni da komai, tammm" ta faÉ—a kamar za ta yi kuka. Ta wuce É—aki cikin fushi.
Mommy da Ummi su ka yi dariya.
Shirye-shiryen Azumi ake yi dan ana batun saura kwana takwas ko bakwai ne. Har lokacin Zaytoonah ta ƙi komawa gidan ta, yanzu kam ta fara amsa wayar Galadima kuma duk hiran su ta ƙare akan jayayyar yaushe za ta koma Abuja ne, ta ce sai bayan sallah ta koma, shi kuma ya ce bai yarda ba dole ta zo kafin a fara Azumi.
Kaman da wasa tun bayan dawowar su daga Ringim sai laulayi ya sa ta a gaba, zazzaɓin safe da kuma rashin cin abinci. Abincinta ya koma daga kunu, tea, romo sai ko gwate. Ba ta sanar da Galadima gameda cikin ba dan albishir ɗin da ta ke son bashi kenan ranan da za su haɗu.
Bisa shawaran Likita ta yaye Alinah 'yar wata shida da sati uku. Yarinyar dama nono bai dameta ba sosai shiyasa first two days ɗin da aka yayeta ba ta wani damu ba, sai a kwana na huɗu kuma ta fara rashin lafiya har sai da su ka kaita Asibiti. Da yamma da su ka dawo su ka tarar da yaran Galadima a gidan sun kawo mu su ziyara. Sun ji daɗin ganin Zaytoonah dan ba ƙaramin missing ɗin ta su ka yi ba. A bakin Raziya ta ji wai Daddyn su ya rabu da Hajiya Ghazala wai har ma an kwashe kayan ta a gidan. Galadima bai gaya ma ta ya saki Ghazala ba shiyasa abin ya zo ma ta a bazata.
Ta É—an ji tausayinta kaÉ—an dan mutuwar aure ba wasa ba ne. But halin ta ne ya ja ma ta.
Ba ta gama fita daga shock É—in sakin Ghazala ba Raziya ta ba ta labarin da ya sa ta cikin ruÉ—u. Wai a Fada ta ji ana hiran Daddyn su zai auri Anty Mubaraka.
"Dan Allah ki ce Daddy kar ya ƙara aure, ya kamata mu zauna mu kaɗan mu, and be a happy family"
Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce " Raziya kenan, ai namiji mijin mata huÉ—u ne. Daddyn ku yanada 'yancin cikata mata huÉ—u"
Tana maganan ne amma zuciyarta na suka.
Ita ina ruwanta idan ma mata É—ari zai aura, abu É—aya ta sani ba za ta sake zama gida É—aya da kowacce shegiya ba.
Bayan tafiyar su Raziya tukunna ta samu damar kiran Galadima. Farkon kiransa kenan cikin kwanaki dayawa.
Lokacin da ta kira shi yana hanyar sa ta dawowa daga Kogi.
Ko sallamar da yai ba ta amsa ba ta fara magana muryanta a shaƙe kamar za ta yi kuka.
"Congratulations Daddyn Raziya, ashe liyafa ta cigaba ka rabu da tsohuwa za ka auri budurwa. Allah ya ba da sa'a"
Kafin ya ce wani abu ta riga ta kashe wayar ya sake kira ba a ɗauka ba ƙarshe ya ji numbar na ta is switched off.
Yai murmushin jin daÉ—i. Zaytoonah na da kishi sai dai duk sanda za ta expressing kishinta to in a childish way ne, and he love that about her.
Zaytoonah sai da ta gama mirgine-mirgine a kan gado kafin ta fito wajen su Mommy da ke falo suna kallo, dan idan ta cigaba da zama ita É—aya a É—akin zuciyarta na iya bugawa. Abinda ko lokacin auren Ghazala ba ta ji ba shi take ji yanzu. Ba ta san waye Mubaraka ba amma jin ita É—in budurwace ba bazawara ba makes her feel threaten. What if idan ya aurota itama ta zo da na ta salon iskancin, what if Galadima ya ga budurwa ya koma ja baya da ita.
Daddy baya nan ya tafi gidan Baba Tsoho. Kusan yanzu a wajen Alhaji Ilyasu kaÉ—ai ya ke zuwa hira, ko bai je ba za ka ga ya aiko a kira shi ko kuma ya kirashi a waya. Alhaji tsufan ya fara shigan sa dan wani lokaci bayan sun sha hira Daddy ya dawo gida sai ka ji da yamma an sake aikowa wai Daddy ya je, idan ya je kuwa sai Alhajin ya ce ai ya jima ba su haÉ—u ba ne shiyasa ya kirashi. Daddy yai murmushi ya ce idan aka ce ka tsufa ka ce har yanzu ba ka tsufa ba da sauran ka. Su yi ta tsokalar juna.
"Ta yi bacci ko?" Mommy ta katse ma ta tunani
"Yes Mommy. Ni kam Mommy sai da na ji kamar na ba ta nono É—azu, ta bani tausayi sosai"
"Ba daÉ—i kam, a haka dai za ki jure har ta saba"
Sai da Mommyn ta kalleta da kyau kafin ta ce "Zaytoonah kuka ki ka yi?"
"A'a" ta faÉ—a tana murza ido
"Da kunnen ki kin ji abinda Likita ya faÉ—a miki. Ke ba yarinya ba ce"
Tana so ta faɗa ma ta maganar da ta ji na ƙarin auren da Galadima zai yi ko za ta ji sauƙi a ranta amma ta san halin Mommy, tana kawo maganar za ta fara ma ta nasiha. But it hurts, it damn fucking hurts ace mijin ka zai ƙara aure.
Maganar tafiya Umara da Mommyn ta yi ne ya É—an É—auke ma ta hankali. Mommy ta biya mu su tafiya Umara ita da Daddy su biyu. Life long wishes É—in su ne da bai cika ba saboda dalilai ma su yawa to amma dama aikin Umara da Hajji sai wanda Allah ya kira, sai wanda Allah ya ba wa iko...
A ɓangaren Daddy kuwa bayan sun fito daga masallaci shi da 'yan biyu da Junior su ka raka Alhaji Iliyasu gida. A veranda inda ya ke yawan zama ya huta a nan su ka zazzauna a kan ƙatuwar darduma sai shi Alhajin da ya zauna akan kujerar sa da ke tsakiya. Bayan su Daddy akwai Dreban Alhajin da kuma wani maƙocin su aka zauna ana hira. Watan Azumi da aka dosa shi su ke tattaunawa akai. Magana ɗaya da Alhajin yai ya sa jikin su yai sanyi.