← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 161

Sashe 3

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ngozi wacce su ke kira da Nne ita ta tsaya ma sa yai primary har ya je sakandare dan Mazi kam ba ya son boko, daga nan ya samu scholarship ya tafi Ingila karatu a chan ya haɗu da Caroline wacce itama karatun ne ya kawota ƙasar sai dai saɓanin shi da ya zo dalilin scholarship ita Caroline Iyayenta ne su ka biya ma ta.
Bayan sun zo gida hutu ne Caroline ta sanar da iyayenta batun Patrick nan fa iyayen su ka ma ta chaa akan ba su yarda ba, kasancewa an riga an yi engagement na ta da wani ɗan abokin Baban ta, na biyu kuma Patrick Igbo ne su kuma ƙabilar Efik ne da ke cikin asalin Jahar Calabar.
Bayan ta koma makaranta ne su ka yi aure da Patrick saboda tana tunanin hakan zai sa Iyayen ta su amince amma hakan bai yiwuba domin shekara da ta zago da su ka zo hutu gidan tareda Patrick mahaifin Caroline korar kare ya mu su tareda cewa ya tsinewa Caroline kar ta sake zuwa wajen sa ko wajen 'yan uwan sa. Tafiyar da su ka yi kenan ba su sake dawowa ba sai bayan shekaru ishirin tareda É—iyar su Nkiru.

Tun kafin su dawo Patrick ya sa ƙanin sa Udodiri ya siya ma sa gida a Owerri dan haka su na zuwa gidan su ka zauna. Nan Patrick ya shiga hidimar buɗe kamfanin sa da zai yi a garin, kusan komai ya kammala akan za a buɗe a farkon sabuwar shekara da za a shiga. Ya ɗauki iyalen sa su ka je ƙauye saboda ɗiyar sa ta ga asalin sa kafin daga baya su nemi iyayen Caroline su nemi gafarar su, ƙila tunda shekaru sun ja kuma har da kyautar 'ya a tsakanin su za su yafewa Caroline su sa wa auren su albarka sai dai Kash! Komai ya juye lokaci guda...

Nkiru ta cigaba da sheshsheƙar kuka tana tunanin ba ta da wata mafita, gara kawai a kasheta ta je ta haɗu da iyayenta a Heaven su cigaba da rayuwar farin ciki.

*To ga fa Mary-Nkiru. Ga kuma T J the mathematician*
Yanzu aka fara tafiyar domin *chronicles of Zaytoonah* ya sha banban da salon tafiyar *Sakatariya ta* infact ya fi shi tsaruwa amma dai mu je zuwa.

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*3-Tijjani Abubakar Djibo*

Modibbo Muhammadu Djibo Kakan T J kenan, Bafulatanin usul ne gaba da baya, kakannin sa daga garin Djibo su ka fito da ke ƙasar Mali sai dai kasancewar su makiyaya ya sa ba sa zama waje ɗaya. A lokacin da kiyo ta kawo su har garin Ringim shine babban su ya fara rashin lafiya. Jinya sosai har kusan shekara, su da ba sa yin shekara a waje sai gashi har shekara na biyu ta same su a garin, kusan shekaru uku kafin Usmanu Djibo ya warke sosai. Karamci da kuma yanayin garin ya sa dukkan su suka haɗa baki su ka tsaida magana akan za su cigaba da zama a garin. Daga nan auratayya ta shiga tsakanin su da fulani 'yan asalin garin, sai aka haɗu aka zama guda.

Kakan T J wato Modibbo Muhammad yana da mata ɗaya Rumaysa'u wacce ake kira Daadawuro, 'ya'yan su biyar Allah ya ma ta rasuwa wannan ya sa aka aura ma sa ƙanwarta Fatima da su ke kira da Yadikko.
Fatima, Khadija, Aisha, Umar da Usman sune 'ya'yan Daada ita kuma Yadikko É—a É—aya Allah ya ba ta wato Abubakar.
A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda aka aurar da yara mata yara mazan ma su ka yi aure ban da Abubakar Auta.
Usman ya auri Maryama su na zaune lafiya shekara huɗu kafin Allah ya bata haihuwa ta samu mace aka sa ma ta Rumaysa'u amma Ruma su ke kiranta. Yarinyar ba ta cika shekara ba Allah yai wa Usman rasuwa. Maryama ta shiga cikin tashin hankali, kusan gaba ɗaya iddar ta ta yi shi cikin jinya ne. Hakan ya sa ko bayan ta gama idda ta cigaba da zama a gidan dama kuma ta haɗa jini da Usman dan auren haɗin gida aka mu su. Shekaru biyu bayan rasuwan Usman Maryama ta samu nitsuwa da kwanciyar hankali, dama har da ƙuruciya da ke daminta shiyasa mutuwar ta girgizata sosai dan tana shekaru sha bakwai Usman ya rasu.

Mahaifin maryama wanda kusan ƙani ya ke ga Modibbo Muhammadu ya samu Modibbo akan ya kamata Maryama ta sake wani aure tunda dai har yanzu da ƙuruciyarta, shima dai yayi tunanin hakan, ganin Maryaman ba ta kwantar da hankalinta ba ne ya sa bai tada maganar ba.
Wasa-wasa duk wanda aka turo ya nemi Maryama sai ta ce ba ta so. Abun ya ishi mahaifinta ya zo har gida ya ma ta faÉ—a ya ce daga yanzu duk wanda ya fito amincewa zai yi tunda alamu sun nuna ba auren ta ke so ba.
Yadikko ta samu Modibbo akan ko za a haɗa Maryama da Yayan mijinta wato Umar. Abin yai wa Malam daɗi sai dai wani hanzari ba gudu ba halin Umar da Usman ba ɗaya ba ne. Yayinda shi marigayi Usman ke da sauƙin kai shi Umar yana da zafi, matan sa biyu amma kullum cikin shari'a ake yi baya mu su adalci kwata-kwata.

"Ni kam ba dan kar ka ce na so kai na dayawa ba da sai na ce a haÉ—a Maryama da yaron wajena"

Modibbo ya kalli Yadikko yana tunanin hikimarta.
Daga nan aka tsaida magana akan za a haÉ—a Abubakar da Maryama wanda tsakanin su kwata-kwata ko shekara bai kai ba. Sa'anni ne dan a shekara É—aya aka haifesu, sun ma yi wasa tare.
Mahaifin maryama yai na'am da maganar ya kuma karɓi sadaki. Amma da aka sanar da Maryama maganar ta ce ba ta san zance ba bazata iya auren ƙanin mijin ta ba. Abu dai aka ja aka ja ƙarshe dai dole ta haƙura aka yi auren.

Da ke ba son auren ta ke ba ba ƙaramin wahala ta bawa Abubakar ba, shi kuwa sarkin haƙuri bai taɓa nuna ma ta damuwa ko ya tsawatar ba. Shekara ta zo ta wuce, auren Maryama da Abubakar a suna ne amma a aikace ba wani abu da ke shiga tsakanin su. Daga ƙarshe dai tausayin Abubakar ya kamata tareda tuna nauyin da ke kanta wanda kullum Yadikko ke zaunar da ita tana ma ta nasiha, daga ƙarshe ta ajiye makaman yaƙi ta rungumi mijinta su ka cigaba da rayuwa cikin farin ciki, bayan wata shabiyar da aure suna zaman kurame.

Aishatu Indo itama 'yar cikin gida ce kuma tun tasowarta ta ke son Abubakar, lokacin auren Abubakar da Maryama tana shekara shauku a duniya. Shekara ta zago aka fara maganar aurar da ita, ta ƙeƙasa ƙasa ta ce Abubakar ta ke so ba Iliyasu da ake son haɗa su ba. Ƙarshe dai dole aka amince tunda auren Abubakar na fari bazawara ya aura. Ba a jima ba aka ɗaura auren Abubakar da Aishatu wacce ta ke ji da tashen balaga da gigin budurci. Kafin auren su, Abubakar da Maryama ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba saboda halin su ya zo ɗaya kuma tun suna yara dama sun yi wasa tare, dama dai kunyar ƙanin miji ya sa Maryama cewa ba za ta iya auren sa ba.

Aishatu da falli ta shigo gidan tana son nuna ita ce aka aureta budurwa, amma ba wannan ba ne a gaban Abubakar. Maimakon ta kwantar da hankalinta ta samu soyayyar miji sai ya zama kullum cikin shiri ta ke yadda za ta muzgunawa Maryama, ko ba matsayin kishiya ba Maryama ta girmi Aishatu amma ba ta ganin wannan haka za ta rufe ido ta yi ta zuba ma ta rashin mutunci. Maryama ba ta kulata dan ta san yarinta ke damunta.

A haka dai aka yi zaman har Aishatu ta haifi ɗa namiji aka sa mi shi suna Usman amma su na kiran shi da Manga. Wannan ya ƙara sawa Aishatu girman kai da tinƙaho ganin har lokacin Maryama ba ta haihu ba. Shekaran Usman biyu ta sake samun ciki wannan karan itama Maryama Allah ya ba ta cikin sai ga shi Aishatu na haihuwa da sati biyu Itama Maryama ta haihu dukkan su kuma maza.
ÆŠan Aishatu ya ci sunan Babban Yayan Aishatun wanda ya rasu a ranan da ta haihu, wato Shehu Tijjani, shi kuma É—an Maryama ya ci su nan Kakan sa wato Muhammad su na kiransa da GidaÉ—o.

Bayan Tijjani Aishatu ta haifi Zainab sannan Mukhtar da su ke kira Muntari. Ita dama Maryama irin matan nan ne da ba sa haihuwa da wuri dan sai da Aishatu ta yaye Muntari kafin ta haifi autar ta Fatima Zahra wato takwarar Yadikko.
Ita kuma Aisha bayan Muntari ta sake haifan Halimatus Sadiya da kuma autar ta Murjanatu.

Zaman Goggo Maryama da Iya Aishatu abin dai har aka tara 'ya'ya bai ƙare ba. Ba abinda ya ƙara kunna wutar rashin jituwar su irin yadda Abubakar ya ɗauki Tijjani ya damƙawa Maryama saboda wani faɗa da su ka taɓa yi akan Tijjanin.
Chapter 3 · 0% Book details