Sashe 149
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ghazala ce ta fara shiga ciki kafin daga baya aka yiwa Galadima iso a falon mijin Hajiya Abu saboda tanada baƙi a nata falon.
Kusan minti shabiyar sannan Hajiya Abu ta sallami baƙinta ta taho wajen Galadima da Ghazala.
Bayan sun gaisa ne Ghazalan ta ari bakin Galadima ta ce dama tafiya ce za su yi shine su ka zo yi ma ta sallama.
"Tafiya kuma? Ina kenan?"
" Baltimore, America" Ghazala ta faÉ—a tana murmushi.
"Lafiya dai ko?" Hajiya ta san ba kasafai Galadima ke son fita waje ba sai dai idan ya zama dole, balle yaushe-yaushe ne ya je American duba Zaytoonah lokacin tana chan.
"Lafiya Hajia" Ghazala ta faɗa dan ba ta son ƙwaƙwƙwafin matar nan.
Hajiya Abu ta kalli Ghazala a takaice kafin ta mayar da kallon ta ga ƙanin na ta wanda tun tasowar sa ta ke matsayin uwa a gareshi.
"Ranka shi daÉ—e ba ka gaya min inda maganar mu ta kwana ba?"
Maganar Mubaraka ta ke nufi kuma ba shi da niyyar ƙara aure ko da kuwa Ghazala ba ta yi ma sa wannan laifin ba.
Sai da ya É—an É—au lokaci bai ce komai ba kafin ya ce"Hajiya magana ne mai muhimmanci ya kawo ni nan"
Ghazala da ke ɗan daddanna waya ta yi saurin ɗago ido ta kalleshi. Tunaninta faɗawa Hajiya Abu zai yi akan ba zai karɓin haɗin da ta ke shirin yi ma sa ba, sai kuma ta ji ya kama wani zance daban.
"Idan ba ki manta ba Hajiya, ke kika kwaɗaita min auren Ghazala. Amma a yau ina so ki shaida cewa aure na da Ghazala ya ƙare, domin na saketa saki ɗaya"
Ya fito da takardar da ya rubuta yau da safe ya ajiye a kan centre table.
Ghazala dai jinta ta yi a wani duniya daban. Gani ma ta ke yi sarawan da kan ta ke yi ne ya tsatstsafo da ruwan da ya toshe ma ta dodon kunne shiyasa ta ke jin maganan Galadima a bai-bai.
Hajiya Abu ba ta yi saurin tare shi ba saboda ta san akwai sauran magana a bakin sa. Halin sa ne magana a hankali kuma ko yanzun ma a hankalin ya ke magana.
"Zan iya kauda kai a ƙarya da munafurci amma sihiri ba zan iya kauda kai ba. Matar da ta yarda da cewa wani abu ba Allah ba zai iya biya ma ta buƙata ba macen da ya kamata na raɓeta ba ne, ba macen da ta dace da gidana ba ne domin akwai barazanar cutar da iyalina a tattare da ita"
Ya kalli Ghazala ya ce " mi ki ke nema dan ban miki ba? Mi kike so da ba na yi miki?"
"Abu RRRRazz...? Ta faɗa da ƙyar.
"Wallahil Azim da yadda ki ka riƙe min 'ya'ya na kafin na aureki haka ki ka riƙe su bayan na aureki da kin samu wani daraja na daban a wajena, darajan da Zaytoonah ba za ta samu ba amma babu tsoron Allah a lamarin ki shiyasa ki ka yi abinda ki ka ga ya dace da son zuciyar ki"
Hajiya Abu was getting impatient dan haka ta ce "Yunusa mi ya ke faruwa ne?"
Bai yi magana ba sai ya ɗau wayar sa ya kunna audio ɗin da ya tura a wayar Kubra. Sai da ya ƙure volume ɗin wayan sa dan maganar bai fito sosai ba.
"Salallahu Alaihi wa Sallam. Ghazalatu!"
"Na shiga uku, Abu Razz haɗa mu ake son yi. Wallahi ba ni ba ne" ta faɗa a ƙoƙarinta na son kare kan ta ta ko wanni hali. Tana maganar ne idonta na fitar da hawaye.
Ya É—au wayar ya binciko inda hoton ya ke ya nuna ma ta wayar "ko ba wannan ba ne layar?"
"Na shiga uku ni Ghazala. Ranka shi daÉ—e ban san ina ka samu wannan ba. Ni na san sharrin Zaytoonah ne wannan. Hajia wallahi asirin Inyamurai ta mishi"
Hajiya Abu kam ta san É—an uwanta sarai, ta kuma yarda da shi, haka kawai ba zai zo da abunda bai tabbatar ba.
" sharrin Zaytoonah ya sa ki ka dinga tsoratar da ita sai da ta fara zama tamkar mahaukaciya? sharrin Zaytoonah ya sa ki ka ce na kaita gidan ki da ke Zuba?, sharrin Zaytoonah ya sa ki ka ce na sawwaƙa ma ta?, sharrin Zaytoonah ya sa ki ka hana 'ya'yana sakewa a gidan Uban su..."
Miƙewa yai tsaye dan idan ya ce zai cigaba da magana sai jinin sa ya hau. Ta maida shi mahaukaci, tana son rena ma sa hankali ne ma.
Ganin ya miƙe ya sa Ghazala ta yi saurin zuwa gaban sa ta durƙusa tana kuka.
"Dan Allah ka yi haƙuri, ka saurareni Dan Allah"
"Za'a kai mi ki kayan ki tsohon gidan ki. Na nan Zaria za a kai miki gidan ku"
"Abu Raziya Dan Allah ka yafe mini. Kar ka tona min asiri. Ciki gareni, ka san ba kyau saki idan mace na da ciki"
Dariya ne ya so ƙwace ma sa amma ya dake. Lallai Ghazala na da buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa.
"Idan appointment É—in ki da Dr Thompson Russel ne ki adana shi zuwa lokacin da ki ka sake wani auren. Ni Yunus ba na wannan shashancin"
Ba ta san cewa ya san komai ba, daga maganar Zaytoonah, zuwa layar da ta karɓo zuwa aikin da za a ma ta a America. Shin Galadima Aljani ne? Ya akayi ya sani?
"Hajia a gaida Alhaji idan ya dawo" Galadima ya faɗa yana ƙoƙarin fita Ghazala ta yi saurin riƙe ƙafar sa tana bashi haƙuri. Juyowa yai ya ma ta wani kallo wanda ba shiri ta sake ma sa ƙafan ya fice abinsa.
Hajia Abu dai aka barta da kallon drama dan ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa yi...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 73
Bismillahir Rahmanir Rahim
*crazy for you*
Ghazala ta rarrafa gaban Hajiya Abu tana kuka tana ba ta haƙuri.
"Wallahi ba hali na ba ne Hajia, ke kin san komai..."
Saukar marin da ta ji ya sa maganar da ta ke ya tsaya.
"Kin bani mamaki Ghazalatu. Asiri ki ke son yiwa Yunusa saboda ke mahaukaciya ce. Ai wallahi ya min dai-dai, dan ko da bai sake ki ba ni zan sa ya sake ki. Wannan wani irin masifa ce ni Zainabu! Akan namiji? Wannan son zuciya ne kawai irin na ki"
Miƙewa itama Hajiyar ta yi ta ce "ki yi maza ki bar min gida, Munafuka"
Bayan fitan Hajia Abu daga falon Ghazala ta bi takardar sakin da ke kan centre table da kallo. A yadda aka naɗe takardar ta tabbatar ɗaya daga cikin memo na office ɗin sa ne. With every strength da ta ke da shi tana son ganin da gaske ne yai ma ta sakin ko kuma wani abun ne daban. Ta sani Galadima ba zai taɓa yi ma ta wasan saki ba but still 0.05% da ke nuna ma ta cewa ba saki ba ne shi ta ke so ta bi.
Hannun ta na rawa ta ɗauka takardar ta warwareta. Ƙanshin turaren sa da ta shaƙa ajikin takardar shi ya sake kashe ma ta jiki.
Ta yi hasashen gaskiya domin letter headed memo na office ɗin sa ne. Wanda ya ke ɗauke da tambarin Nigerian Court of Apeal. Kafin idon ta ya sauka kan rubutun da aka yi da baƙin biro sunan sa da ke jikin takardar ɓaro-ɓaro shi ya ƙara sa bugun zuciyarta ya ƙaru.
*Justice Yunus Muhammad Abbas* there is pride a cikin kasancewarta matar shi. There's diginity and honour a cikin kiranta matar Honorable Justice Yunus. Akwai kwarjini a kasancewarta matar Galadiman Zazzau amma duk wannan ya watse da rubutun da bai wuce layi biyar ba sai signature da kuma date da ke ta ƙasa.
Rubutun sa ya ma ta kyau, sai dai abinda aka rubuta babu kyau a cikin sa ko kaÉ—an. Saki É—aya ne kamar yadda ya faÉ—a. Saki É—aya za a iya kome ai. Zai iya maida ta ai, ko yanzu zai iya maidata. Abinda ta ke tunani kenan
"Mai Martaba zan samu, Galadima baya jayayya da mahaifinsa, zai mayar da ni É—aki na idan mahaifin sa ya sa shi dole" ta furta a fili.
"Maryam idan Ghazalatu ta fita daga falon Alhaji ki tabbar kin share kin goge sosai kin ji"
"Hajiya ba É—azu aka gyara ba"
"Za ki je ki yi abinda na ce ko sai na make ki"...
Daga sama ta ke jin muryar Hajiya Abu da jikarta Maryam. Kamar tsikarar allura haka sunan Maryam ya ankarar da ita da 'yar uwarta Maryam.
Tun farko da ita za ta auri Galadima, if only ba ta saka son zuciya a lamarin ta ba.
"ki faÉ—awa Abba ya fasa haÉ—a auren ki da Yarima Yunus. Ina son shi, kuma shi zan aura"
"Ghazala ba kya ganin son zuciyar ki yayi yawa. Ke kika ce ba kya son shi. Ni nan sai da na ce miki Yaya Zannoon yana da kirki ki amince da shi amma ki ka yi biris kika ce ba kya son shi, Alhaji Bashir ki ke so..."
"Ai ban san haka ya ke ba ne, shiyasa. Kuma ma yanzu zaɓin iyaye zan bi dan ya fi Albarka"
Maryam ta yi murmushi sannan ta ce "Ghazala ba ki san soyayya ba, ba haka ake soyayya ba. Soyayyar da ki ka yiwa Alhaji Bashir ta suna ne da ɗaukaka. Sannan soyayyar da ki ka yi iƙirarin kina yiwa Yarima ba komai ba ne face sha'awa. Soyayya mai tsabta ba a gina shi da waɗannan kuma..."
"Ba na son wa'azi Malama Maryama. Saurayi dai ni aka fara yiwa tayin sa kuma ina son abu na yanzu, ki bar min shi"
"Duk abinda Abba ya zaɓa mana ba zan bijire ma sa ba. Amma ki sani, indai rayuwar ki a kullum zai tafi wajen son zuciya ne to wallahi sai kin yi nadama Ghazala"
*to wallahi sai kin yi nadama Ghazala* maganan Maryam na ƙarshe ya dinga ringing a kunnen ta.
"Bakin Maryam ya kamani" ta furta a hankali
Ta ƙanƙame takardar da ke hannunta, ta cigaba da zubda hawaye.
***