← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 161

Sashe 122

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tsaye a wajen sink tana wanke-wanke ta ji ana ƙwanƙwasa mu su ƙofa. Sunan Junior ta fara kira amma tuni yayi bacci a falo. Jin shiru ya sa ta fito falon da zimmar ta ma sa faɗa ƙila kallon da ya sa a gaba ne ya sa bai ji kiran na ta ba. Ganin yana bacci ya sa ta wuce ɗakin ta ta ɗau mayafi ta yafa sannan ta fito.
Wanda ta gani tsaye bayan ta buɗe ƙofar ne ya sa ta zaro ido waje.

"Muntari" ta furta a bayyane
2/11/21, 10:04 PM - ****: 60

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Revelation*

"Maryam ba za ki ba ni ko ruwa ba"

Muntari ya faɗa yana murmushi wanda ya bayyana korayen haƙoran sa. Tunda Mommy ta bashi dama ya shigo falo ta kasa ɗauke ido akan sa. Ya rame ya zabge yayi duhu sosai, kallon ɗaya za ka ma sa ka danganta shi da mai cutar ƙanjamau wanda ciwon ya ci shi sosai. Wannan jiki lub-lub da ya ke da shi a lokacin da ya ke amsa sunan Alhaji Muntari babu shi yanzu. Idan ba farin sani ka ma sa ba da ka kalleshi sau ɗaya ba za ka ce shi ɗin ba ne, ga uwa uba furfurar wahala da ya dabaibaiye ilahirin gashin kan sa zuwa gamun sa.

A iya sanin ta saura shekaru biyu a sake shi amma...

"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan iya yi"

Maganar sa ya yanke tunanin da ke. Jiki a sanyaye ta miƙe ta wuce kitchen. Abincin Salman da Auwal da ta ajiye ta ɗauko ta saka a faffaɗan tray da su ke haɗuwa su ci abinci. Ta ɗaura plate da sokali akai sannan ta buɗe fridge ta ɗauko ruwan gora mai sanyi ta ɗaura akai tareda kofin glass. Ta ɗauko tray ɗin ta ajiye a centre table ta jawo table ɗin gaban sa.

"Bismillah" ta faÉ—a tana zama kusa da Junior da har lokacin ke bacci.

Cire hannun sa daga tagumin da yai yayi sannan ya buɗe food warmer ɗin haɗe da ɗauko plate ɗin ya fara zuba jollof ɗin shinkafa mai kyau da ya ji kayan lambu da kuma nama da hanta wanda aka yanka ƙanana.

Mommy hannun sa ta ke dubawa yadda ya koma, har wani kaushi-kaushi ne a jikin yatsun hannun na sa. Yadda ya ke kai loman abincin da sauri ka ce ya yi wata bai sa abinci a baki ba. Tabbas akwai yunwa a tattare da shi.

"Ikon Allah" ta faÉ—i a ranta tana tuno wasu shekaru da Muntari yai ma ta dirar mikiya a wannan gidan wanda daga nan ne komai ya chanja mu su. A wannan lokaci ya zo a matsayin Alhaji Muntari amma yanzu sai ga shi nan a miskini dan ko Almajiri ya fi shi daraja. Duniya kenan.

Bayan ya gama cin plate É—aya sai da ya sake cikawa ya ci kafin ya É—au goran ruwa ya kwankwaÉ—a. Zuwa lokacin kuwa babu wanda yai magana tsakanin su.

"Gidan nan ya chanja sosai, da ƙyar na iya gane shi" ya furta lokacin da ya ajiye goran ruwan.

"Anyi sauye-sauye dayawa a gidan kam"

"Abinci yayi daÉ—i sosai, na gode"

Mommy ba ta ce komai ba sai dai ido da ta bishi da shi tana karantar yanayin sa.

"Ina 'ya'ya na Zaytoonah da Salman. Wannan shine Mai sunan Baffa ko?"
Ya faÉ—a yana nuna Junior

"Suna nan lafiya"

"Allah ya mu su Albarka, ya ƙara mu su danƙon soyayya da zumunci Amin"

Amin Mommy ta faɗa a ƙasan ran ta.

"Baby tana wajen Hanne ko?"

Ashe dai ya tuna cewa yanada 'ya É—aya tilo a duniya.

"Eh, ta kan kawo mana ita idan sun yi hutu"

"Humairah ta yi aure ne?"

Mommy ta gyaÉ—a ma sa kai.

"Ba ka je gidan Iya ba ne?"

Dariya ne ya suɓuce ma sa wanda Mommy ta tsorata da yanayin sa. Daga tambaya sai dariya.

Yana dariyan kuma sai ga hawaye sun fara zubo ma sa, daga dariya sai ya koma kuka. Abin sai ya ɗaurewa Mommy kai musamman da ta ga zahiri dai kuka ya ke bil haƙƙi.

"Muntari ko ma minene ka yi haƙuri dan Allah. Kuka ba zai yi maganin komai ba" ta faɗa dan yanzu kam tausayi ya ba ta.

Ya jima yana kuka kafin daga baya ya goge hawaye ya kalli Maryam ya ce " ban ɗauka zan yi rai ba Maryam. Ina gani Allah ne ya bani dama ta ƙarshe domin na tuba na gyara kura-kurai na"

Haka ya zayyane ma ta irin wahalhalun da ya sha a prison É—in da aka kaishi a Warri da ke Jahar Delta.
Gabannin a sake shi yayi rashin lafiya sosai. Typhoid ne ya ma sa mummunan kamu har ta kai sai da aka fita da shi Asibiti dan ƙaramin clinic na prison sun kasa treating ɗin sa. Bayan ya warke da aka dawo da shi prison ko wata uku bai yi ba aka saka sunan sa cikin mutanen da shugaban ƙasa ya mu su alfarma aka sake shi. Da ya fito daga prison ba shi da komai hakan ya sa sai da yai dako na kusan sati uku kafin ya samu kuɗin mota zuwa Kaduna daga nan kuma ya ƙariso Zaria. Kai tsaye gidan Mommy ya zo dan nan ɗin ya ga ya dace ya je duk da ba shi da tabbacin ko har yanzu suna nan ɗin. Yadda gidan ya sha gyara ya chanja fasali kwata-kwata bai gane ba dan dai yaron da ya rako shin ya tabbatar ma sa cewa nan ɗin ne gidan Malama Maryam, Maman Salman.

Mommy sai da ta yi hawaye jin labarin sa. Tunda aka ɗauke shi daga Prison ɗin Kaduna dama ta san akwai abu a ƙasa.
Ba ta sanar da shi badaƙalar da Alhaji Rabi'u ya ke da dukiyar sa ba balle walaƙancin da ya yiwa su Iya. Bayan ya ɗan nitsu ta ce zai fi ya je ya duba Iya saboda itama hankalin ta ya kwanta. Bai musa ba dan ya ga alama a takure ta ke da shi. Junior da ya riga ya tashi tuntuni ta sa ya raka Muntari zuwa gidan Iya. Da ke sanda aka ɗaure Muntari yana ƙarami bai iya tuno shi ba.

Suna fita daga gidan ta kira Auwal ta ce dan Allah ya dawo gida yanzu akwai baƙo mai muhimmanci da ke jiran sa.

***

"Zannoon" ta kira sunan sa a hankali.

"Ba ka ce komai ba"

"Adaeze tambayar da ki ka yi ya dace. A ganin ki ya dace?"

"I'm confused. Dr Malak ta ce a hankali zan samu lafiya amma har yau abu É—aya na ke. May be gaskiyar Hajia Ghazala da ta ce ciwon hauka gareni, may be its true that i'm crazy"

"Kar ki sake kiran hauka wa kan ki ba na so"

"Ka yi haƙuri amma..."

"Shshshsh" ya faÉ—a bayan ya É—aura yatsarsa É—aya a bakin ta.

"Kamata yai ki biya bashin jiya ki tanade ni amma kin tsaya surutu"

Kissin yatsar sa ta yi tareda faÉ—in "bani minti biyu na shiga banÉ—aki, zan zo na tanadi Tsoho. Yau tanadi na musammamn za ayi"
Ta faÉ—a tana tashi daga kan gadon.

Bayan ta fito daga banɗaki Galadima ya miƙa ma ta waya akan Mommy ta kirata har sau biyu. Karɓan wayan ta yi ta zauna tareda dialling numbar wanda ringing ɗaya aka ɗauka. Bayan sun gaisa Mommy ta ce ma ta idan da hali ta tambayi Galadima ya barta ta zo gida.

"Mommy lafiya?"

"Lafiya Zaytoonah. Akwai baƙon da mu ka yi ne kuma ya kamata ku gaisa kafin ku koma Abuja. Ina goben za ku tafi?"

"Ok zan tambayeshi"

Tana ajiye wayar ta juya ta kalli Justice da ya haÉ—e rai.

"Haba shalele na, wannan fiskar ai ta waje ce ba ta É—akina ba"

Ƙarisowa ta yi wajen sa ta manna ma sa kiss a goshi, hanci kafin ta sauka kan bakin sa nan da nan kuma ya amshe ya shiga kissing ɗin ta shima. Sun yi nisa cikin kula da juna su ka tsinkayi knocking ɗin da ake yi.

"Daddy Hajiya Babba ta zo"

Rigan ta da Justice ya ɗage yana wasa da ƙirjinta ta saukar tana kallon yadda ya ke cize leɓe abinda ya ke mafiya yawan lokaci idan ya ji haushin wannan abu.

Hajiya Abu ba baƙuwar da zai ajiye ba ne shiyasa ma ta fara kimtsa kan ta.

"Da gaske dai ba za a tanade ni ba"

"Safiyar yau dai babu rabonka" ta faÉ—a tana dariya.

"Za ki shigo hannu Yarinya" ya faɗa tareda miƙewa. Banɗaki ya shiga kusan minti shida sai gashi ya fito. Zuwa lokacin Zaytoonah ta gyara gadon na su da ya ɗan fara yamutsewa.

"Na je Wajen Mommyn ?"

"Idan Hajia ta tafi sai ki je" ya amsa ma ta kafin ya fice daga É—akin...

Magana ce dai akan abinda ya faru jiya ya kawota.. Ko miye na ta a ciki idan ma Zaytoonah na da Aljanu oho.

Tambayar gaskiyar zance ta yi dan a tunaninta idan har da gaske Zaytoonah na da Aljanu to kuwa dole a nema ma ta magani tun kafin ta shafawa yaran sa.

Shiru ta yi na kusan minti biyar tana tace maganganun da Galadima ya ma ta akan Zaytoonah. Karon farko da ta ji tausayin ta kenan.

"Amma ana warkewa?" Ta tambaya bayan dogon shiru.

"Sosai ma, Insha Allah itama za ta warke , ina so idan har Allah ya kaimu hutun ƙarshen shekara zan sake kaita wajen Likita"

"Allah ya ba ta lafiya"

Ya amsa da Amin.

Sun É—an jima suna hira kafin daga baya Zaytoonah ta sauko su ka gaisa. Har da yi ma ta ya jiki.
Da ke Ghazala ta je Fada sai ya zamana suna gaisawa Hajia Abu ta tafi.

Bayan tafiyar Hajiyar da minti talatin itama ta shiga mota Dreba ya kaita gidan su...

***

"Mommy da gaske Uncle Muntar ya zoi" ta maimaita a karo na uku.

"Idan ba ki yarda ba yana gidan Iya ki je ki tabbatar wa idon ki"

"Mommy i'm just surprise. Ni fa har na manta da shi, idan ba Baby na gani ba ma kwata-kwata mantawa na ke da shi a duniya"

"He's alive and free. Ki je ku gaisa dan ya tambayeki"
Chapter 122 · 0% Book details