Sashe 2
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ƙauyen Okwuohia ya cika da Jama'a maza da mata, 'yan ƙauyen da kuma 'yan ƙauyukan gefen su, kai hatta daga manyan garuruwan da ke kusa da su anzo domin halartar bikin Mbom-uzo da ake yi a ƙauyen na shekarar 1985.
Bisa dagewar Eze dole T J ya biyoshi su ka halarci bikin. Su isu isu 'yan bautar ƙasa sun je dayawa, dan za su kai su goma shabiyu a wajen. A nan T J ya haɗu da wani Corper ɗan uwan sa musulmi kuma Bahaushe ɗan Jahar Katsina mai suna Hassan, shi kuma daga Orlu local government ya taho.
Waje guda aka ware su dan a karramasu, dukkan su kuwa suna sanye da uniform É—insu hakan ya sa su ka fito su ka yi kyau.
Bayan anje anyi zagaye-zagaye an gudanar da mafiya yawancin abinda bikin ya ƙunsa gameda tsafta da gyara muhalli tukunna aka zazzauna yayinda wa su dayawa ke tsaye, nan aka fara tafi saboda shigowar 'yanmata filin da za su gudanar da rawan su na Atilogwu.
Kai tsaye wajen Sarki su ka je su ka tsugunna su ka gaisheshi sannan su ka cigaba da gudanar da rawan.
T J dai ya ji an chanja kiÉ—a kuma ana ta ihu da shewa amma bai É—ago kan sa ba saboda lissafi da ya ke yi a É—an littafin da ya taho da shi.
Eze da ke gefen sa ya taƙale shi yana nuna ma sa 'yan matan da ke rawa a tsakiyar fili. Sai a lokacin T J ya ɗago idonsa yana kallon ma su rawan, da ɗai ɗai ya ke kallon su har ya kai kan wata budurwa da ke rawa, abin da ya banbantata da sauran shine ita ta ɗan fi su jiki, kayan da ta sa irin na sauran ne amma sai ya fi amsar jikin ta sosai. Wrapper ce aka ɗaura wanda ya tsaya iya rabin cinya sai uban jigida da ke ƙugun su. Saman ma dai wrapper ɗin ce aka ɗaura iya wajen nonuwa amma an tamke shi sosai yadda ya kama nonon sosai kamar wani bra, sai beads da ke wuyan su, hannun su da ma tsintsiyar ƙafa. Yadda ta ke rawan tana shaking hips ɗinta da ya fito sosai ya tafi da imanin T J. Shagala yai da kallon wannan budurwa ita kaɗai, dan gani ya ke yi kamar ita ɗaya ke rawa a filin. Duk yadda ta ke ɗaga ƙafa tana swirling ƙafar da hannu abun ya ƙayatar da shi yana tracing every step ɗinta da ido. Tin da ya baro garin su ya zo Imo state, daga camp har zuwa yau bai taɓa ganin macen da ta burgeshi lokaci guda ba kamar wannan yarinyar. Komai na ta ya burgeshi musamman yadda dimple ɗin ta ke lotsawa idan ta yi murmushi.
Eze dai har miƙewa yai tsaye ya fara rawa saboda kiɗan da ke shigar sa abinka da shima ɗan ƙabilar Igbo sai ya kasance jin abinda ake faɗa a waƙar ya sa shi jin nishaɗi sosai.
A wajen T J kuwa har 'yan matan su ka gama rawan mace ɗaya ya ke kallo. Yana ji da za su tafi ta ƙwalawa Babanta kira tana ɗaga ma sa hannu tana murmushi. T J bai san lokacin da biron hannun sa ya suɓuce daga hannun sa ba ganin yadda dimple ɗin fiskan ta ya lotsa ya ƙara haskaka kyakyawar fiskarta, bai yi ƙoƙarin ɗauka ba dan kar yarinyar ta tafi ba tareda ya gama kallon ta ba.
" Allah yayi halitta a nan, Abokina ba ƙarya Yarinyar ta haɗu"
Sai a lokacin T J ya juyo ya kalli Hassan da ke riƙe da biron sa. Murmushi yai dan ya ji kunya da har Hassan ya gane irin kallon da ya ke wa wannan yarinya.
Shi dai har su ka bar ƙauyen ba abinda ya burgeshi a wajen festival ɗin kaman wannan yarinya da ya gani tana rawa.
A hanya kuwa Eze da Hassan su ka sa shi gaba da tsokala. Eze har da cewa za su koma ƙauyen nan ba da jimawa ba su nemi gidan su yarinyar. T J dai bai tanka mu su ba...
***
Nkiru baki har kunne lokacin da su ka koma gida musamman da iyayenta su ka nuna ma ta tafi kowa iya rawa a wajen.
Shirin kwanciya su ka yi dukkan su ukun. Rashin yarda da 'yan uwan mijin ta ya sa Caroline ba ta yarda sun raba makwanci da É—iyarta ba, tare su ke kwana a É—aki dukkan su uku.
"Mary" Caroline ta kira sunan É—iyar ta cikin wani siga na jan hankali.
"Yes Mommy" ta amsa tana kallon mahaifiyarta dan indai ta ma ta irin wannan kira to ta san akwai abu mai mahimmanci da ta ke son faÉ—a ma ta.
Caroline ta nisa kafin ta fara yiwa 'yarta bayani kan tafiyar su gobe da sassafe. Nkiru ta tambayi dalilin tafiyar bayan da ance sai bayan christmas za su koma gidan su da ke Owerri.
"Ban yadda da ƙauyen nan ba, ina ji ajikina akwai mugaye a gidan nan wanda za su iya cutar da mu"
"But Mommy..."
"Kar ki damu, in the mighty name of Jesus ba abinda zai samemu"
Mary ta amsa da Amin tareda faÉ—in "i love you Mommy"
Caroline ta amsa da " i love you too"
Patrick kan tuni yayi bacci dan haka su É—in ma baccin su ka yi...
Wata Zakara ke ta chara ba kakkautawa hakan ya sa Nkiru buɗe idanun ta inda ta ga haske ya soma karaɗe ɗakin na su. Gajiyar jiya bai saketa ba dan haka ta ƙara gyara kwanciyar ta ta cigaba da bacci, sai dai charan Zakaran da ɗan hayaniya da ke tashi a gidan ya sa ta kasa samun bacci dole ta buɗe ido tareda miƙewa zaune. Daddy da Mommy duk su na bacci wanda ya sa Nkiru mamaki dan kullum ita ce ƙarshen tashi a cikin su.
Ta fara bubbuga kafaɗar Caroline tana cewa ta tashi safiya ta yi amma shiru. Ganin ta ƙi kulata ne ya sa ta koma gefen Patrick ta fara bubbuga shi.
Wani ƙara ta challa lokacin da ta ankara cewa duk yadda take tashin iyayen na ta ba wanda ya motsa a cikin su. Ƙaran da ta yi ne kuma ya sa mutanen gida su ka fara shigowa ɗakin da gudu. Mutum na farko da ya fara shiga kuwa shine Uncle ɗin Nkiru wato Uncle Augustus Udodiri. Tun safe ya ke safa da marwa yana jiran wani ya shiga ɗakin Yayan na sa ya ce ya samesu a mace da shi da iyalin sa sai dai kowa harkan gaban sa ya ke ba wanda ya waiwayi ɗakin Patrick shiyasa ya ke ta sintiri a kusa da ɗakin.
Mamaki ne ya É—an kamashi na lokaci kaÉ—an saboda ganin Patrick da matarsa a kwance amma Nkiru na zaune tana rusa kuka, mi hakan ke nufi? Ba dai ba ta ci abincin ba ne?
Wajen Patrick ya nufa yana taɓa shi tareda tabbatarwa kan sa cewa lallai Patrick ya mutu...
***
Kuka ta ke yi mai tsuma zuciya na yadda rayuwarta ya juya lokaci guda. Daddy da Mommy sun mutu ga ta nan É—aure a É—an tsurkukun É—aki wai ana tuhumarta da maita, wai ita ta kashe iyayen ta. Uncle Udodiri har da cewa ita ta cinye 'yan biyun ta Magdalene. 'Yan biyun ta da a hoto kawai ta ganta ba ta iya tuno ta saboda ba su cika shekara biyu bama ta mutu. 'Yan biyunta da an tabbatar pneumonia ne yai sanadiyyar mutuwar ta shine Uncle Udo ke cewa ita ta cinyeta. Da wanne ma za ta ji, da mutuwar iyaye ko da sharri da aka ma ta.
Kwana ɗaya kenan da mutuwar kuma ance ba za a bisine iyayen ta ba sai an tabbatar da maitancin Nkiru a fili an kuma ƙona ta saboda kar ta cinye sauran 'yan gidan.Ashe maganar Mommy gaskiya ne da ta ce ba ta yarda da 'yan uwan Daddyn ta ba.
Kakan ta wato mahaifin Patrick asalin ɗan gargajiya ne shiyasa ya tara mata dayawa, ciki kuwa biyu ne kawai ya auresu kamar yadda al'ada ta tanada mahaifiyar Patrick wanda ta mutu wajen haihuwarsa sai Ngozi wacce ta raini Patrick ɗin sai dai kasancewar Ngozi ba ta haihu ba har shekara uku ya sa Kakan Nkiru mai suna Ozoemena ya taho da Mistress ɗin sa wacce ke ɗauke da cikin sa a lokacin. Lokacin da ta haihu kuwa ta samu namiji aka sa mi shi suna Udodiri. Daga nan kuwa Mazi Ozoemena ya rinƙa tara mistress har guda bakwai ciki kuwa duk sun haihu idan ka cire matar sa Ngozi da ba ta samu haihuwa ba sai ɗan da ta riƙe wato Emeka. Mazi ya mutu ya bar yara shatakwas amma uku sun mutu kafin mutuwar sa, ciki kuwa biyar ne kawai maza. Bayan mutuwar sa ne kuwa aka samu cikin yaran da matan waɗanda su ka koma zuwa addinin kiristanci. Emeka kam ya jima da zama sai dai tsoron Baban su ya sa ya ke ɓoyewa, amma da Baban ya mutu shine ya fito fili ya bayyana aƙidar sa har ya je aka baptizing na sa a church aka ba shi suna Patrick.