Sashe 133
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga shi dai Zaytoonah ta bar mu su gidan kamar yadda ta so tun farkon zuwanta amma maimakon su ji daÉ—in gidan sai ya zamana kaman ma a takure su ke.
Ala dole Galadima ya maida tradition ɗin cin abinci da 'ya'yan sa. Wannan abin ya tunzura Ghazala matuƙa, da farko ta ɗauka saboda fishi da ya ke da ita ne amma ko da su ka shirya ɗin ma hakan ne ya cigaba. Ko ta kai ma sa shi falon sa a sama sai ya ce a ƙasa zai ci abincin tareda Yaran.
Yau ma suna cin abinci da yaran Raziya ta ce "Daddy yau aka raba mana test É—in da mu ka yi na Maths. I got 10/10"
"Masha Allah. Sai ki ƙara ƙoƙari"
"Daddy tunda Anty Zaytoonah ta fara koya min Maths Allah sai na ga ashe abin ma ba wahala"
"Ya yi kyau"
Suhailah ta ce "Daddy yaushe Anty za ta dawo? i miss her"
Wani kallo Ghazala ta ma ta irin za ki gamu da ni É—in nan.
"I miss her too" Falaq ta faÉ—a a hankali
"Za ta dawo very soon"
"Daddy ka kira mana ita mu yi video call"
"Wai ba na hana surutu idan ana cin abinci ba ne. Suhailah kin fara rashin ji ko"
Gaba É—aya yaran sai su ka yi kalar tausayi.
Har aka gama cin abincin dai babu wanda ya ƙara magana.
***
"Kai Malam ka duba gabanka mana, idan ka buge shi mi za ka ce"
"To shima Baban idan ba Makaho ba ai yana ganin na iho ta nan ɗin amma ya ƙi ya matsa" Ɗan Achaɓar ya faɗa cike da haushin Tsohon da ya kusa bugewa.
"Ja'irin Yaro, gaba É—aya ba tarbiyya"
Ɗan Achaɓar ya kaɗa mashin ɗin sa yai gaba yana muzurai shi a dole dai Tsoho ne da laifi.
"Sannu Baba, yaran zamani ne sai a hankali ƙila ma a buge ya ke yanzu haka"
"Ba komai É—ana, idon ne sai a hankali ba sosai na ke gani ba"
Tsoho mai ƙusumbi wanda aƙalla zai kai shekaru casa'in da uku ya kalli mutumin da ya taimaka mi shi ya ja shi gefe lokacin da mashin ta yo kan sa ya ce " Ɗana ya sunan ka?"
" suna na Shehu" ya faÉ—a yana murmushi.
"Ko za ka taimaka ka raka ni gida nan ƙasa na ke"
Shehu ya ce ba matsala ya kama hannun Baban su ka kama tafiya.
Tafiyar minti biyar su ka yi ta kawo su ƙofar gidan Tsohon inda Almajirai ke zaune a gindin wata bishiya suna bitar karatu.
Tsoho ya ce da Shehu su ƙarisa zaure. Bai yi ma sa musu ba dan tausayin sa ya ke ji.
Sai da su ka zauna kafin Tsohon ya ce "bari a kawo ma ka ruwa"
Tsohon ya É—an É—aga murya ya kira suna Yusufa jim kaÉ—an sai ga yaron ya iso. Tsoho ya ce ya je ya kawo ma sa ruwa.
Bai fi minti É—aya da rabi ba sai ga shi ya dawo É—auke ta kofin tangaran cike da ruwan Randa mai sanyi.
Sai da Tsoho ya karɓi ruwan ya sha kafin ya miƙawa Shehu shima ya karɓa, ya kuwa sha ruwan dayawa duk da bai jima da shan ledar ruwa biyu ba a shagon Ɗalha ɗazu.
Da zai tafi Tsohon da ya kira kan sa da Malam Zulkiflu ya ce ma sa gobe ya zo su sake gaisawa. Shehu ya ma sa godiya sannan ya tafi.
Malam ZulKiflu ya ƙurawa Shehu ido duk da ma dai ido ɗaya ne ke gani itama ɗin ba ƙarfi.
Tabbas hasashen sa ya tabbata akwai sihiri ajikin mutumin nan.
Shehu har ya koma rumfar sa da ya ke saida kayan marmari bai bar mamakin wannan Tsohon ba, shi kan sa bai san ya aka yi ya amince ya bi Tsohon zuwa gidan sa ba, bayan shi ba mutum ne mai son shiga Jama'a.
Shi bayan barin sa garin Sokoto inda yai aikin Gadi a gidan wani Alƙali bai sake aiki ƙarƙashin kowa ba. Iya kuɗin da ke jikin sa da ya fita da shi da ya tafi Zamfara sana'ar Saida Rake ya fara yi cikin ikon Allah kuma ya samu ya tara jari sosai, lokacin da Rake ya ɗaga ƙafa sai ya koma sayarda kayan marmari kaman Lemu, Kankana, Ayaba. Ya taɓa yin sana'ar kayan Marmari lokacin da tafiya ta kai shi garin Bauchi, har ya samu gindin zama amma rana guda ya tatttara komai na sa ya ƙara gaba. Shi kan sa idan aka titsiyashi ba zai iya furta dalilin barin na sa garin ba...
***
"Ni dai na gaya mu ku ba sai kun zo ba"
"Idan kika ce haka Mommy har yanzu fishi kike kenan. Besides Wallahi jikin Zaytoonah ya ce zai duba"
"Auwal ku wuce Nigeria kawai"
"Haba Mommy, yaushe rabon da ki ga first son É—in ki"
Sai da ta yi shiru na kusan sakan goma kafin ta ce "shikenan ku zo É—in"
"Na gode Mommy"
Ba ta amsa ma sa ba ta katse kiran.
Ajiyar zuciya ta yi kafin ta É—au Jacket ta saka sannan ta É—auka gyale ta yi rolling.
Fitowa ta yi É—auke da jaka da waya.
Lokacin da ta fito falo babu kowa a wajen, bayan a wajen ta bar Zaytoonan tana shan coffee.
"Zaytoonah, Adaeze" ta fara kiranta amma shiru. Kitchen ta wuce ta tambayi mai aikin su ko ta ga Zaytoonah amma ta ce ta barta a falo tana kallo.
"Ba ta falo" Mommy ta faÉ—a a rikice tareda ficewa daga kitchen É—in da sauri.
Kai tsaye waje ta tafi inda ta tambayi security É—in gidan ko ya ga Zaytoonah, ya ce ta yi garden. Mommy ta wuce ta baya inda garden É—in gidan ya ke.
Hango Zaytoonah da ta yi kusa da bishiyar zogale ya sa ta ji sanyi a ranta.
"Zaytoonah mi ya kawo ki nan?"
"Zan ciri zogale"
"Ai sai ki ce Madam Leslie ta tsinko miki"
"Mi za ki yi da shi ma tukunna"
"Zan tanadi Tsoho ne yau, kin san yana son kwaÉ—on zogale sosai"
Wannan kalma dai ba yau ta fara jin sa ba, tunda farko-farkon zuwan su kusan kullum sai ta yi maganar tanadin Tsohon nan. Ko mi Tsohon nan ya ke ma ta ma dai a bayan fage to Zaytoonah na alfahari da shi.
Shawaran Likita ta ke bi shiyasa ta hana Zaytoonan magana da Galadima. For now maganar Ben ake so a kawar tukunna although yanzu ta dena tsorata da rana amma ranan da aka gwada yi ma ta test aka barta ita É—aya a office É—in likitan aka kashe wuta sai da ta sake kiran sunan Ben.
"Mu je ciki Madam Leslie za ta ciro miki zogalen"
"Momm..."
"Asibiti za mu je, idan mun dawo sai ki tanadi Tsoho"
Hannunta ta kama su ka wuce cikin gida sai da ta fara ajiye zogalen da ta ciro a kitchen kafin su ka fito inda Dreba ya wuce da su Asibiti inda Zaytoonah za ta yi awu.
***
"Na ce Mahbubi tunda dai kwana biyu ne mi zai hana kawai yaran su yi zaman su idan ya zo ƙarshen wata sai mu tafi da su"
"Ba matsala sai ki zauna da su kawai, ƙarshen wata sai mu je duka"
"Ina nufin ka ga dai yaran nan suna Makaranta idan sun je ba karatu su ke ba sai wasa"
"Ba matsala ki kula da su a nan har su yi karatun"
Shigewa banÉ—aki da yai ne ya rufe maganar.
"Yau na jawa kaina" ta faÉ—a a fili.
Yaran da ba ta so su je weekend tare, su É—in dai ta fita ta nema ta ce su shirya kayan su za su tafi Zaria da yamma...
Wannan karan zuwan da ta je ko Fada ba ta je ba iya kacinta gidan su sai kuma gidan ƙawayenta biyu da ta je. Ranan Lahdi da za su koma sai ga Hajia Abu ta kawo mu su ziyara.
Ala dole ta ma ta ladabin ƙarya harda ba ta haƙuri lokacin da Hajiyar ke faɗa akan rabon da ta zo gidanta har ta manta, ko a waya ma ba ta nemanta. Ghazala ta fake da cewa hidiman Yara ne ke riƙeta ga kuma shagonta da ba a jima da kawo mata kaya ba...
"Wai Yaran nan kuna ta ina ne" Ghazala ta faÉ—a a tsawace.
Galadima ne ya sa ta fita da yaran shopping. Da da ne jiki na rawa za ta yi amma yanzu kam ko kaÉ—an ba ta son wannan aikin wahalan.
Raziya da Suhailah ne su ka fito daga É—aki.
"Ita kuma mai hannu É—aya da rabin fa?"
"Tana kashi" Raziya ta faÉ—a fiska a É—aure.
"Zo nan Maryam" ta kira Suhailah da ke tsaye tana wiki-wiki da ido
MurÉ—e kunnen yarinyar ta yi ta ce "ba na hanaku shiga É—akin Daddyn ku ba, amma shegen kunnen ki jiya harda shiga ki kwanta ki yi bacci"
"Hajiya, Daddy ne fa ya kirata"
"Yi min shiru munafuka, da ya kirata sai ya ce ta kwanta ta yi bacci"
Sheshsheƙar kukan da ta fara ya sa ta sake kunnen tana faɗin " yi min shiru a nan ko na zane ki"
Suhailah ta yi saurin haÉ—iye kukan.
"Falaq idan ba ki fito yanzu ba tafiya zan yi"
Ta faɗa tana sauƙa ƙasa.
Suhailah ta faɗa jikin Raziya tana kuka ƙasa-ƙasa. Ba yau ne ta fara mu su wannan cin zalin ba. Ranƙwashi da jan kunne ya zamar wa Hajiya Ghazala ɗabi'a idan tana yiwa yaran faɗa.
Washegarin ranan da Yaran su ka yi maganar sun yi missing Zaytoonah a wajen cin abinci ma kowannen su sai da kansa ya gaya ma sa dan ranƙwashi bibbiyu ma su kyau ta mu su tareda gargaɗin idan su ka sake kawo maganar Zaytoonah a gidan sai ta mu su duka...
***
Muntari ya samu lafiya sai dai yana zaune akan wheelchair ne saboda ba shi da ƙarfin jiki. Likitocin sun ce zuwa wata huɗu ma zai iya dena amfani da kujerar. Kwanan su huɗu tareda su Mommy kafin su ka wuce Nigeria.
Mommy ta sha addu'o'i da godiya ba adadi a wajen Iya. Dan Iya kam yadda su ka tafi ba ta É—auka Muntari zai yi rai ba...