Sashe 82
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni kam miyasa gashinka ke yawan karyewa ne yanzu?" Ta yi tambayar tana kallon sa. Tun zuwanta yai saurin chanja abinda ya ke rubutawa zuwa wani wajen saboda kar ta lura da will É—in sa da ya ke typing.
Sai da ta sake tambayar kafin ya juyo ya kalleta ya ce "ba na kula da shi ne shiyasa amma zan yi aski".
Ranan da yamma bayan ya fita sai gashi daya dawo kuma kan sa ƙwanƙwal ba gashi ko ɗaya. Zaytoonah ta dinga ma sa dariya har Dada ma ta taya ta suna ma sa waƙar Zuhayr mai ƙwaryar molo, shi kuwa sai murmushi ya ke mu su.
Da dare suna kwance akan gado ya ce " nan da shekaru kaÉ—an za ki zama cikakkiyar Lawyer. Barrister Zaytoon"
"Ni kam..." ta yi maganar tana turo baki.
"Ki min Alƙawari Zaytoon, duk abinda ya faru ba za ki yi watsi da karatun ki ba. Zan yi alfahari da ke idan har za ki tsaya tsayin daka har ki ƙarisa karatun ki lafiya. Ina so ki zama abin alfahari ga 'ya'ya na. A Barrister and a Ballerina"
"Idan kana tare da ni zan iya zama koma minene"
Ya shafa kan ta ya ce "idan Allah yana tareda ke ba kya buƙatar kowa, domin shi ɗan Adam mai gushewa ne Allahu kuwa shine farko, shine ƙarshe. Shi ya ke jiɓintar dukkan lamurran mu. Zai iya yiwuwa ranan da za ki ƙare karatun ki bana nan, zai iya yiwuwa ranan da za ki fara aiki ba na nan, zai iya yiwuwa ranan da Muhammad da Ahmad za su fara makaranta ba na nan. Amma ina so ki sani Allah na nan kuma shi zai riƙeku a lokacin da babu ni"
"Ka dena irin wannan maganar dan Allah. Ba abinda zai sameka, ina ce Likita ya sallameka ne saboda ka samu lafiya, ina ce kullum kana ce min jikin ka da sauƙi..."
"Za mu je Madina" ya katse maganar ta ganin tana shirin kuka.
"Nan da kwana biyar za mu tashi, zamuje mu sauke farali Insha Allah. Kinga duk dukiyar dana tara idan har ban je na sauke farali ba babu amfanin dukiyata. Za mu je mu yi Umura Baby. Na yi magana da Likitan ki ya ce ba matsala za mu iya tafiya. Tareda Dada za mu je Insha Allah" ya ƙarisa maganar yana kamo yatsunta.
Maganar zuwa Umurah da yai sai ya kawar da maganar farko da ya fara ma ta. Ta shiga murna, ƙarshe kuma ta haɗe rai ta ce tayi fishi saboda bai ma gaya ma ta ba sai da tafiyar ta matso kusa, sai da ya lallasheta kafin ta haƙura su ka kwanta cike da farin ciki.
Ana saura kwana uku za su tafi sai ga Saifullahi ƙanin Muhsina ya zo ashe har da shi za ayi tafiyar.
Dada da Saifullahi ke magana lokacin da Zaytoonah ta sauko dan ta taya su hira saboda ta gaji da zaman É—aki. Chak ta tsaya lokacin da ta ji maganar da Saifullahi yayi.
" ni fa tunda Uncle ya gaya min jikina yai sanyi. Mahaifiyar sa ma haka aka ce ba za ta wuce wata shida ba amma ko kaiwa wata shidan ba ta yi ba ta rasu. Ina tsananin tausayin Zuhayr"
"Rayuwa da mutuwa duk na Allah ne. Idan Allah ya bashi tsawon rai sai ka ga ya samu lafiya. Ai Likitoci ƙoƙari su ke yi amma Allah ne mai kashewa kuma mai rayawa"
Zuwa lokacin hawaye ya cika idanunta.
"Dada wa ye aka ce zai mutu?" Ta yi maganar cikin kuka lokacin da ta ƙariso wajen su da sauri.
"Ba dai mijina ba ko?, ba dai Zuhayr É—ina ba ko?"
Dada ta taso ta kamo hannunta ta zaunar da ita a kujera.
"Na sha faɗa miki a wannan hali da ki ke ciki kina buƙatar nitsuwa da kwanciyar hankali saboda lafiyar 'ya'yan ki"
"Ba Zuhayr É—ina ku ke magana ba ko?"
Dada ta gyaÉ—a kai yayinda Saifullahi ya ce "muna maganar Alhaji ne. Kin san jikin tsufa"
Duk da wani ɓangare na zuciyar ta ya so ƙaryata maganar Saifullahi amma da ta daure ta yaƙice wasi-wasin da zuciyarta ke yi, ta sa a ranta Alhaji Iliyasu Kakan Zuhayr ɗin ne ake magana.
Lokacin da Zuhayr ya shigo ɗaki tana sallar Isha'i. A bakin gado ya zauna yana ƙare ma ta kallo. Ba abinda ya ke riyawa a ransa face watarana duk yadda ya ke son ta dole su rabu, rabuwa ta har abada wanda haɗuwar su sai dai a lahira. Ta dalilin sa rayuwar ta ya shiga haɗari a lokuta da dama wanda ba dan kariyar Allah ba da itama ta tafi kamar yadda Alinah ta tafi. Yanzu da ake faɗa ma sa survival rate na shi is very low sai ya kasance yanzun ne kuma ya ke son rayuwan, yanzun ne ya ke son nunawa Zaytoonah soyayya da tsantsar kulawa. Yana fata ko da baya nan Allah ya ba ta wanda zai riƙeta tsakani da Allah. Lokaci na da mahimmanci a rayuwar Ɗan Adam, amma sai ya kasance Ɗan Adam ɗin baya duba gudun lokaci baya duba mahimmancin lokaci. Ina ma yayi amfani da lokacin da su ka kasance tare tun farkon zuwan ta?
"D lafiya?" Muryan Zaytoonah ya dawo da shi daga dogon nazarin da ya ke yi.
Yai ma ta murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo.
"D wai da gaske Alhaji bashida lafiya?"
Saifullahi ya gaya ma sa yadda su ka yi da Zaytoonah É—azu shiyasa ya tabbatar ma ta da cewa da gasken Alhaji ne ke ciwo.
"Ina kai kam lafiyar ka ƙalau?"
Ya jawota ya ɗaurata kan cinyarsa yana faɗin lafiyata ƙalau.
"Ban maka nauyi ba?"
Ya sa hannu ya shafa cikinta ya ce "ko da Boys ɗina irin ƙashin ki su ka ɗauko ai zan iya ɗaukan ku duka uku lokaci guda"
"Kayya! Da wani jikin?"
Yai ƙaramar dariya ya ce "da jikin da na ke gaisawa da su mana"
Ta rufe fiskanta da tafukan hannunta tana faÉ—in har ka sa na ji kunya.
"Barin yi wanka sai na gaishe da boys É—ina"
Ta tashi daga kan cinyarsa tana É—an nishi.
"Are you Ok" ya faÉ—a in a concern tune.
Ta gyaÉ—a ma sa kai. Sai da ya kissing goshinta kafin ya wuce banÉ—akin, ta bi bayan sa da kallo. Normally Zuhayr was skinny amma kuma yanzu da ta lura sai ta ga kamar ya zama extra skinny. Ta yi saurin É—auke tunanin ta hanyar cewa diet É—in sa da aka chanja ma sa ne tun lokacin da ya fara jinya ya sa shi ramewa haka.
Ana gobe za su wuce ƙasa mai tsarki Zuhayr ya kawo ma ta wasu takardu kusan kashi takwas ya ce ta dinga sa hannu. Bai ba ta damar karanta miye a cikin takardun ba, ce ma ta yai na tafiyar da za su yi ne.
Washegari su ka wuce Saudi Arabia. Jirgin su ya sauka a Riyadh kafin su ka wuce birnin Makkah ta mota. Kwana uku kafin tahowar su su ka je wajen Sheikh Hassan yai mu su sharen fage gameda ibadar da za su yi idan sun je. Lokaci ne da babu chunkoso dan saura kusan wata biyu a fara Azumi shiyasa su ka samu damar gudanar da ibadun su cikin kwanciyar hankali. Idan ka cire kumburin ƙafa da ke damun Zaytoonah a duk lokacin da su ka je masallaci suna ibada ba ta da wata matsalar komai. Kullum su ka je masallacin Ka'aba addu'ar da ta fi bawa mahimmanci shins Allah ya ƙarawa Zuhayr lafiya ya kuma sa ta sauka lafiya yai wa 'ya'yan ta Albarka. Mahaifinta kuma tana addu'ar idan yana raye Allah Ubangiji ya bayyana mu su shi idan kuma ya rasu Allah ya kyautata makwancinsa.
Ranan da za su wuce Madina Zuhayr ya fara zazzaɓi. Da farko sun so tsayawa zuwa ya warke amma ya ce ba komai zai iya zuwa Madinah birnin Manzo (SAW).
Haka su ka ƙarisa tare bayan ya sha magani jikin na sa ya ɗan lafa, sai dai a wheel chair Saifullahi ke turashi saboda jikinsa da yai weak sosai, kafin su wuce Madinan aka sa ma sa nasal canula saboda numfashin sa ya dai-dai ta. Jikin Zaytoonah yai mugun sanyi da yadda ta ga Saifullahi na tura Zuhayr, sai ta ke ganin kamar akwai abinda ya ke ɓoye ma ta amma koma minene za ta bari su gama ibadar da ya kawo su tukunna kafin ta dameshi har sai ya gaya ma ta gaskiya.
Alhamdulillah kuma zuwan su Madina sai zazzaɓin na sa ya lafa ma sa sosai.
Haka su ka kammala Umara lafiya har suna shirin komawa Makkah gobe. A ranan ne kuma su ka je Raudha inda su ka samu damar gabatar da gaisuwa ga fiyayyen halitta. Lokacin da Zuhayr ya bar wajen ƙofar murmushi ne mai sanyi ɗauke a fiskar sa. Irin murmushi na contentment ɗin nan.
Sallar Isha aka idar yayinda aka zauna ana yin addu'o'i. Bayan sun kai kusan awa ɗaya suna jero addu'o'i kafin Saifullahi ya juyo wajen Zuhayr dan ya tambayeshi ko su wuce masaukin su ko kuma dai su ƙara jira kaɗan. Akwai maganin da Zubayr ɗin ke sha duk ƙarfe tara na dare shiyasa ma ya ke son su tafin.
Kan sa a duƙe lokacin da Saifullahi ke taɓa shi, maimakon ya ga Zuhayr ya ɗago sai ya ji shiru.
Wani Balarabe da ke gefen Zuhayr ne ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun yana magana yana ɗago kan Zuhayr da ke duƙe fiskar ɗauke da murmushi.
Yadda Balaraben ke ta zuba larabci da kuma mutanen da su ka fara tasowa suna zuwa wajen ya sa Saifullahi farfaÉ—owa daga daskarewa da yai a wajen na hucin gadi.
Abinda su ka fara yi shine su ka cicciɓi gawar Zuhayr daga wheel chair su ka shimfiɗa shi a ƙasa. Saifullahi ya bi fiskar Zuhayr da kallo yana hawaye. Maimakon ɗazu da aka ɗago da fiskar idon shi na buɗe yanzu anriga an rufe ma sa idon, rufewa ta har abada.
Ba za su iya cewa ga takamaimai lokacin da Zuhayr ya rasu ba. Walau suna sallar Isha ɗin ne ko kuma kafin sallar, ko kuma ma dai bayan an idar da sallan Allah ya karɓi ran sa.