Sashe 86
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Complete wata shida ta yi tana attending theraphy da farko a wajen Doctor Malak lokacin suna Saudiyya daga baya da su ka koma America kuma Dr Rerdon ya dinga kula da ita. A hankali da yardar Allah ta fara samun sauƙi. Kamar a mafarki haka ta tashi watarana ta shirya ta wuce makaranta, ta loosing semester ɗaya amma ba ta damu ba dan ta ɗau aniyar ƙarisa karatun ta kamar yadda ta yiwa Zuhayr Alƙawari. Hatta Ballet dance da ta ajiye gefe tuntuni sai da ta re-enrolling ta fara attending class. Yaranta na samun kulawan da ya kamata a wajen Dada duk lokacin da Zaytoonah ke makaranta suna maƙale da Dada ko kuka ba sa yi sai dai yunwa da an basu abinci kuma shikenan. Daga lokacin da su ka fara rarrafe ne kuwa ƙiriniyar su ta fara fitowa har yau kuma da su ke shekaru huɗu a duniya.
Da ke duk wani abinda zai tada ciwon Zaytoonah ana kiyayewa shiyasa ma yanzu abin ya yi kusan shekara bai tashi ba. Taƙare degree ɗin ta inda ta fara Law school na ta a Abuja. Dawowan ta Nigeria ne ta dawo tareda 'yan biyun ta duk da kuwa da farko Uncle Aliyu ya so ta bar yaran a wajen sa. Dukkan su a gidan Mommy su ke zaune sai dai duk weekend a gidan Kakannin su su ke yin sa wani lokaci haka kawai ma sai su bushi iska su tafi gidan Baba tsoho ko kuma idan Salman ya dake su sunyi fishi sai su yi yaji su tafi chan gidan.
Babban burin Mommy shine ta ga Zaytoonah ta zama cikakkiyar Barrister saboda akwai aikin da ta tanada ma ta...
Abbati ne ya tiso ƙeyar Hashir da Hadid har cikin gida. Jikan gidan Baba Tsoho ne shima. Idon su yayi wuri-wuri.
"Abbati lafiya, mi su ka yi?" Zaytoonah kenan ta yi maganar saboda ta san halin 'Ya'yan na ta.
"Anty Zaytoonah yaran nan fa su ka takura wai sai na tafi da su masallaci wajen wazifa. Ashe sun san abinda su ka shirya ne. Muna cikin wazifa su ka je su ka zubawa Zakiri Aminu cirnaku a kan sa da cikin rigan sa"
Yana maganan Hashir da Hadid na girgiza kai saboda sun san kashin su ya bushe a wajen Mom. Dan ta hanasu irin wannan, akwai lokacin da su ka je su gidan cirnaku irin sun firfito dayawa ɗin nan suka dinga tsinta suna sakawa a leda. Da dare da Salman yai bacci su ka je su ka zuba ma sa a jiki da kan gado, cirnaku su ka yi ta cizon sa. Da farko ya ɗauka ma sauro ne sai da ya ji zafin yayi yawa kuma cizon ba waje ɗaya ba sannan ya tashi ya je ya kunna wutan ɗakin ai kuwa ya ci karo da cirnaku akan gado wasu kuma sun riga sun sauka ƙasa, ya dinga tsalle yana karkaɗa jiki a ɗaki daga baya ma sai da ya je yai wanka dan ganin su da yai dayawa haka sai tsikar jikin sa ya tashi. Ya duba ko'ina a ɗakin amma bai ga alamun ta ina cirnakun su ka shigo ba ƙarshe ya sa a ran sa cewa 'yan biyu ne tunda da yammacin ranan ya dake su...
Wani kallo da ta wurga mu su ya sa suka yi kneel down a wajen ba shiri.
"Ban hanaku zuwa tsince cirnaku ba? Ban hanaku sawa mutane cirnaku a jiki ba?"
"Mom shi ne Malam Aminu mai murÉ—e mana kunne a Makaranta kuma..."
"Shut up!. Ai na gane shi sarai. Shine ya kawo ƙaran ku kwanaki akan ba kwa mai da hankali a karatu kuma kuna damun yara a makaranta"
Ta kalli Abbati ta ce ma sa ya bawa Malam Aminu haƙuri za ta aika Salman idan ya dawo ya bashi haƙuri.
Bayan tafiyar Abbati Zaytoonah ta kalli 'yan tagwayen 'ya'yan na ta. Yadda Mommy ba ta duka haka itama ba ta yarda da dukan yaranta ba sai dai ta basu punishment ɗin abinda ba sa so mafiya yawanci kuwa ta fi sa su yin rubutun Allo tunda ba sa so. Sun sha cewa ma ta cire su a makarantar Allon amma ta ƙi. Baba Tsoho (Alhaji Iliyasu) ne ya saka su da kan sa tun ma kafin ta sasu a Islamiyya.
Ta cigaba da karatun da take yi saboda exams ne a gaban su. Exam ɗin da daga shi idan har ta haye shikenan sai ayi call to Bar. Hashir da Hadid kuma sai ƙunƙuni su ke yi kowa da Allo a hannun sa yana rubutu. Sau goma ta ce za su cika Allon amma a na ukun da su ke rubutawa Mommy ta dawo ta ce rubutun ya isa haka tunda dai sun ba da haƙuri. Ko da wasa Mommy ba ta son a takurawa jikokin na ta.
Ana gobe Zaytoonah za ta koma school lokacin Mommy ta tafi Ringim 'yan biyu su ka shirya plan É—in su. Goggo ne ba lafiya kusan cikin 'yan watannin nan ma sintirin Asibiti ake yi da ita yanzu ma ba a jima da maida ita gida ba bayan tayi kusan sati uku tana kwance a Asibitin Murtala da ke Kano.
Babu wuta dan haka generator ne ke aiki tuntuni saboda Zaytoonah na tsoron duhu. Tana cikin banÉ—aki tana Alwalar da za tayi sallar Isha Generator ya mutu. Hashir da Hadid ne su ka je su ka kashe switch É—in tunda sun san yadda ake kashewa suna gani idan Junior ko Salman na yi.
Ƙoƙarin fitowa ta yi daga banɗakin da sauri tunda ta san mi duhu ke jawo ma ta shiyasa ko ba wuta su kan kwana da Gen a kunne.
Da lalube ta buɗe ƙofar banɗakin ta fito a hankali ƙirjin ta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Turo ƙofar ɗakin da aka yi a hankali ya sa ta daskarewa a wajen jikinta ya fara maƙyarƙyata. Maimakon a shigo ɗakin sai aka sake jawo ƙofar da ƙarfi ta yi ƙara baaam.
"Zuhayr, Zuhayr, help! Ben zai kashe ni. Ben is here. Zuhayr, Zuhayr"
Tana ƙwala kiran Zuhayr Yaran nan na bakin ƙofa suna wasa da shi su buɗe su kulle. Sai dariya su ke ƙasa-ƙasa yau kan sun yi maganin Mom.
Dawowar Salman daga wajen kallon ƙwallo ya ga gidan da duhu ya je wajen da ake ajiye generator ya gan ta a kashe amma kuma ma ba a kashe wajen mai ba balle a cire waya kawai switch ɗin aka kashe. Yai saurin tada Generator ɗin dan ya tabbatar da lafiyar Gen ɗin ai kuwa Gen ya tashi lokaci guda.
Hashir da Hadid na jin an kunna Gen su ka yi saurin guduwa zuwa ɗakin su har da ɗauko littafi suna karatun ƙarya dan sun san ba makawa Uncle Salman ne, Junior Zaytoonah ta aikeshi chan ta ƙasan layin su.
Ɗakin Zaytoonah ya fara shiga dan ya tabbatar da lafiyar ta, ai kuwa a sume ta sameta a ƙasa. Yai saurin kaiwa wajen ta yana kiran sunan ta da ƙarfi. Jin yanda Salman ke kiran sunan Mom ɗin su ya sa su ka ajiye pretence ɗin su ka shigo ɗakin da gudu. Suna son Mom ɗin su sosai kawai rigimar yaran ne ta yi yawa.
Suna ganin Salman na shafawa Zaytoonah ruwa a fiska su ka tsugunna a wajen suna kuka suna faÉ—in we are sorry Mom.
"Ku ne ku ka kashe Gen ko?" Salman ya daka mu su tsawa. Ba su bashi amsa ba sai ma ƙara sautin kukan su da su ka yi.
A hankali Zaytoonah ta buÉ—e ido tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, ganin fiskar Salman ya sa hankalin ta ya kwanta ta kira sunan sa a hankali "Salman"
Salman ya so dukan yaran amma Zaytoonah ta hana shi. Sai ma jawo yaranta da tayi jiki tana rarrashin su.
"Miya sa ku ka tsoratar da ni?" Ta yi tambayar tana kallon yaran na ta ɗaya bayan ɗaya. Wanka ta mu su ta shirya su cikin kayan bacci. Maƙale ma ta su ka yi wai tare za su kwana a maimakon ɗakin su da su ke kwana da junior.
Kallon-kallon su ka tsaya yi kafin su ka ce ma ta saboda ta sa su rubutun Allo ne.
"Kuna so na tafi Aljannah wajen Dad É—in ku na bar ku a nan?"
"No Mom" su ka faÉ—a da sauri
"To ku dena tsoratani kun ji. Duhu yana sani rashin lafiya"
Sorry Mom su ka faÉ—i tareda shigewa jikinta.
Daren ranan tare da su ta kwana É—aya na gefenta na hagu É—aya a na dama. Ta rungume su a hakan su ka yi bacci.
'Yan biyu sun gane illar da duhu ke wa Mom ɗin su ne farkon dawowan su Nigeria lokacin suna shekara uku. Ana tsakiyar kallo a falo da dare kwatsam sai Nepa su ka ɗauke wuta. Mommy ba ta falon Zaytoonah ce da 'yan biyunta sai Junior. Hashir da ke gefenta ne mistakenly ya ɗaura ƙafar sa akan na ta ƙafa shikenan hankalin ta ya tashi ta shiga maƙyarƙyata ta fara kiran sunan Zuhayr. Mommy da ke sallah a ɗaki sai jin ihun Zaytoonah ta yi tana kiran sunan Zuhayr da ƙarfi, Zuhayr ɗin da ya jima a cikin ƙasa. Ba shiri ta yanke sallar ta fito daga ɗaki da torchlight a hannunta. Yadda Zaytoonah ta takure kan kujera tana maƙyarƙyata ka ɗauka wani Aljani ta gani. Sai da ta rungumeta ta dinga ce ma ta nine, nine Mommy kafin da ƙyar hankalinta ya dawo jikinta. Ranan kam Mommy ta ja Allah ya isa wa Ben yafi a irga. Duk treatment ɗin da ake ma ta farko-farkon haihuwar Zaytoonan da har ake tunanin ko haukacewa ta yi Mommy ba ta taɓa tunanin abin haka ya ke ba. Dada ne ta san komai gameda rashin lafiyar Zaytoonah saboda kar ta tada hankalin Mommy ba komai ta ke faɗa ma ta ba. Bayan ta koma Las Vegas Mommy ta je ta dubata sau ɗaya kuma lokacin ta fara samun sauƙi dan haka ba ta ga irin halinda Zaytoonah ke shiga ba idan ciwonta ya tashi...