Sashe 111
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Red handed ta kama Raziya na ɓata ma ta ɗaki. Abin takaici har da ɗebo ruwa ta kwarara a kan carpet ɗin ɗakin.
Zaytoonah ta haɗa hannu a ƙirji ta ce "yawwa! yayi kyau haka, kin kyauta sosai. Kinga yadda ki ka ɓata mun ɗaki to haka na ke so ki gyara komai yadda ki ka same shi"
"Ba abinda zan gyara" ta faÉ—a da tsiwa tareda ture empty bucket É—in da ta gama juye ruwan a tsakiyan É—akin.
Ta tako za ta wuce Zaytoonah ta jawota baya ta ce " na miki kama da wanda ke wasa da ke? Oya maza ki fara gyarawa kafin jikin ki ya gaya miki a gidan nan. Yau ko uban ki bai isa ya hana ki gyara É—akin nan ba"
Ba da wasa ta yi maganan ba dan yadda ta ke zare ido kaɗai ya tsoratar da ita. Ta sani ko dukan ta Zaytoonan ta yi ba me ƙwacen ta dan Justice ya tafi Zaria yau da safe.
"Oya fara!"
Haka ta shiga tattare kayan tana naɗewa wanda su ka jiƙa kuma tana ajiyewa gefe.
Zaytoonah ta ɗauko ɗaya daga cikin belt ɗin ta ta naɗe a hannu ta jawo stool ta zauna tana kallon Raziya da ke yin aiki tana hawaye. Ashe ɓatawa da daɗi amma gyara da wahala.
Bayan ta gama naɗe kayan ta ce ta dinga jera ma ta su yadda ta same su. Sai ta ɗauko za ta saka wannan ta ce ma ta ba anan ya ke ba. Kusan sun shafe minti talatin wajen jera kayan. Tun Raziya na yin kuka a hankali har ta koma tana yi da ƙarfi amma ko gizau Zaytoonah ba ta ji a ranta ba. Ta dai riƙe belt ɗin ne amma ba dukan ta za ta yi da shi ba duk barazana ce. Abinda ta sani shine yau dai sai ta koyawa yarinyar nan hankali nan gaba ɗakinta ma ba za ta shiga ba balle ta taɓa ma ta kaya.
Ba ta damu da cupcake É—in ta da ke oven ba dan ta san timer É—in na cika zai kashe kan sa.
"Kin ga waɗannan jiƙaƙƙun kayan mu je ki shanya su tukunna kafin ki zo ki naɗe carpet ɗin nan ki goge ruwan da ke ƙasan"
Ba sabawa ta yi da aiki ba dan wannan da ta yi gaba É—aya ta gaji. Jin maganan Zaytoonah ya sa ta zaro rinannun idanun ta.
"Ki zaro idon da kyau, aiki ne sai kin yi dan ni ba baiwar ki ba ce da zaki ɓata min ɗaki na gyara"
Fashewa ta yi da kuka wiwi a ganin ta Zaytoonan za ta ɗaga ma ta ƙafa.
"Ki gama kukan ki cigaba da aiki ba"
Kukan ta ne Atika ta jiyo ta shigo É—akin da sauri dan ganin mi ya ke faruwa.
Ganin Zaytoonah riƙe da Belt ya sa ta concluding ai kawai dukan Raziyan ta yi "Haba Hajiya. Yanzu 'yar marainiyar Allah ki ke duka, Haba Hajiya"
"Fita min a ɗaki!" Zaytoonah ta daka ma ta tsawa. Ba shiri ta fita da sauri har buge ƙafa ta yi saboda gulma da ke cin ta.
Tana zuwa ɗakin ta ta ɗau waya ta kira Hajia Ghazala ta shiga labarta ma ta gaskiya da ƙarya. Hajia Ghazala jiki na mazari ta ce ga ta nan zuwa. Amma kafin ta zo sai da ta kira Hajia Abu tana kukan ƙarya tana faɗa ma ta abinda Atika ta gaya ma ta harda itama na ta ƙarin gishirin.
"Yanzu haka ina hanya kenan zan je gidan, koma minene yau za ayita ta ƙare"
Galadima sai yanzu ya samu ganawa da mai martaba a falon sa da ba kowa ke da ikon shiga ba.
Suna cikin tattaunawa sai ga kiran Hajia Abu. Bai É—auka ba sai ya rage volume É—in kiran. Mai martaba ya ce ba matsala ya É—au kiran kawai.
"Abba, Hajia Abu ce zan kira daga baya"
"Zainabu Abu ikon Allah. Da Allah yayo min ita a namiji da ba ƙaramin ƙasaita za ta buga ba"
Galadima yai murmushi dan shima ya san halin Yar ta sa.
"Ta same ni akan maganar ka da Ghazala yana É—aya daga cikin abinda ya sa na ce ina son ganin ka"
Galadima ya É—an sha jinin jikin sa yana sauraron Mai Martaba...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 51
Bismillahir Rahmanir Rahim
*The fat bride*
"Shiga da Bismillah Gimbiya" abinda Hajia Ni'ima ta faɗa kenan da ke riƙe da hannun Zaytoonah sai kuma Ummi da ita ma ke riƙe da hannun ta na hagu sashen Hajja aka fara kawota tunda ita ce Uwargida.
Already she's feeling suffocated da wannan shegen Alkyabba da aka kakaɓa ma ta, wata marar hankalin kuma ta zo ta ƙara buɗe ta da turare daga shigar su falon Hajja.
Sai da su ka kaita gaban Hajja kafin su ka É—aga ma ta hulan Alkyabbar wanda da ya rufe fiye da rabin fiskarta. Sai guÉ—a ake yi ana bugawa Amarya kirari.
Addu'a Hajja ta yi tareda yiwa Amarya kyauta. Daga nan kuma aka wuce da Zaytoonah É—akin sauran matan Sarkin. Bayan an gama gaishe-gaishe sannan aka maida Amarya sashen Hajja saboda a nan za ta kwana sai washegari a kaita gidan ta.
Duk da ba sa shiri da Zaytoonah ba a barta a baya ba wajen kawo Amarya ba. Ummi ce ta ma ta faɗa lokacin da ta zo sai dai deep down itama na son shiga 'yan kawo Amarya saboda ba ta taɓa shiga Fada ba.
Su huÉ—u su ka kwana a É—akin da aka bawa Amarya. Zaytoonah, Ummi, Humairah da kuma Goggo Mariya.
Bayan sun shiga ɗakin ma sai da aka yi ta shigowa ganin Amarya. Ba su suka kwanta ba sai kusan shabiyun dare. Da ƙyar Zaytoonah ta iya cire kaya ta yi wanka kafin ta yi bacci, gajiya ne a tattare da ita kamar me, ga bacci da ya cika ma ta ido.
Washegari aka yi wuni a Fada wanda Zaytoonah ta sha kyaututtuka daga ahalin mai martaba. Wasu sun yi tsakani da Allah wasu kuwa ganin ido ya sa su ka yi kar a ce wace ta yi ita ba ta yi ba. Tsakanin safe da yamma sai da Zaytoonah ta chanja kaya kala shida. Anyi hotuna kuwa kamar ba gobe.
Bayan sallar magariba aka wuce da Amarya Zaytoonah gidan Angonta da ke nan Zaria ɗin. Already su Hajia Ni'ima na gidan suna jiran zuwan Amarya, ita ta jagoranci 'yan rakiya har zuwa ƙaton ɗakin Zaytoonah wanda ya sha gyara da tsadaddun kayan ɗaki na zamani.
Sai da aka ci aka sha kafin aka fara watsewa a hankali - a hankali har ya saura 'yan tsiraru. Zuwa ƙarfe goma gidan yai tsit, daga Zaytoonah sai ko ma su aiki da ke gidan.
Jin shirun yayi yawa ya sa Zaytoonah ta É—au waya ta kira Mommy. Maimakon Mommy sai muryan Junior ta ji wanda ya sanar ma ta Mommy na falo.
" Hashir da Hadid sun yi bacci ne?"
Ya amsa ma ta da eh tareda cewa ai da kuka su ka yi bacci dan sun ce za su je su wajen Daddy Uncle Salman ya mu su faÉ—a. Ta yi murmushi dan ta san ba dan shi É—in ba da yanzu suna nan suna yiwa Mommy kukan sakarci.
"Kai mata wayar" ta bashi umurni.
Cikin baƙin da za su kwana a nan ne ake ta hira da ban gajiyan biki.
Mommy ta amshi wayar tareda miƙewa ta wuce ɗaki.
"Amarya hope lafiya?"
"Kai Mommy daga kira"
"Ba dole ba"
Zaytoonah ta yi dariya tana faÉ—in
"Mommy na missing É—in ki sosai"
"Tun yanzu"
"Jiya fa ban gan ki ba yau ma ban gan ki ba"
"Kin ga dare yayi ki bari gobe ma yi magana. Asuba tagari " daga haka ta kashe wayan dan ta san idan ta biye ta sai su jaa lokaci a haka.
Cikin ran ta tana godiya wa Allah bisa ni'imar da yai ma ta. A karo na biyu ta aurar da Zaytoonah a hannu na gari wanda shine burin kowanni iyaye...
Bayan ta fito daga wanka ta sanya doguwar rigan bacci ta kwanta, sai da ta ɗan duba wasu saƙon da aka tura ma ta ta email kafin ta yi addu'a ta kwanta. Ko minti biyu ba ta yi ba da rufe idon Justice ya turo ƙofa tareda sallama. Da ke ba ta bacci a cikin duhu yana buɗe ƙofar ya hango ta kwance a tsakiyar gado.
Ya so ya shigo da wuri amma mutane 'yan gaisuwa suka riƙe shi. Yana shigowa gidan wanka ya fara yi sannan ya saka sabuwar jallabiyar sa ruwan ƙasa. Ya ɗan fesa turare kaɗan kafin ya fito riƙe da leda a hannun sa ya nufi ɗakin Amarya.
A bakin gadon ya zauna ya ɗan taɓa kafaɗarta yana kiran sunan ta a hankali. Tana jin sa dan ba ta yi baccin ba amma ta share shi. Ya sake kiran sunan ta wannan karan da ɗan ƙarfi sai dai nan ma shirun ta yi.
Ganin haka ya sa Justice ya miƙe tsaye yana faɗin "Asuba ta gari Amarya" har ga Allah ya ɗauka baccin na ta ne yai nisa fita yai daga ɗakin ya wuce na shi ɗakin. Kazar da ya siyo ya buɗe ledar ya sa ta a fridge da ke falon sa kafin ya shige ɗakin sa. Ya kalli makeken gadon sa da ke ɗakin yai murmushi, rabon da gadon ya samu baƙo shekaru biyu da wata takwas kenan. Ya kwanta kan gadon ya sa hannu ya shafa gefen sa da ke fankololo. Ya so ace ko da ba abinda zai shiga tsakanin su yau ya ji ɗumin mace a jikin sa, sai dai kamar yadda ya iya haƙuri na kusan shekaru uku to zai haƙura na yau ɗin. Shima kan sa da gajiya a tattare da shi balle ita Amaryar ta sa wacce za ta yi kwanan baƙun ta.
Alarm ɗin ta na ƙarfe biyar ne ya tashe ta daga bacci, ta ɗan mirgina ta ɗau wayar ta kashe alarm ɗin saboda na biyu kenan da ya ke snoozing dan ta sa shi a snooze bayan kowanni minti biyu.
Sai da ta ƙara kusan minti huɗu akan gadon kafin ta iya miƙewa ta shiga banɗaki ta yi tsarki sannan ta ɗaura alwala.