← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 161

Sashe 69

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"You look beautiful"

Tsikar jikinta ya fara tashi dan har lokacin bai saketa ba tana jin saukar numfashin sa a wuyanta.

Ta yi saurin cewa "ehm Chef Green ya iya girki, wannan kifin ba ƙaramin daɗi zai yi ba"

"Idan za ki yabi wanda yai girki to ni za ki yaba. I did all this by myself"

"Da gaske?"

Dawowa yai É—aya kujeran ya zauna sannan ya ce "kin san mijin na ki gwani ne wajen girki"

"Shiyasa ban taɓa ganin ka a kitchen ba ai. Sai dai a dinga ba da order"

Ta fara kwaikwayon muryan sa "Chef Green i'll like to have lasagna, salad and chocolate ganache"

Yai murmushi har sai da haƙoransa su ka bayyana.

"Da gaske kai ka yi girkin?" ta sake tambaya tana kallon abincin kan table É—in.

" i only grilled the fish"

"Ka yi ƙoƙari ai, wannan karan ba ka samu babban kifi ba" ta faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin ɗiban kifin a plate ɗin ta.

"Da kina wajen mai kamar ki zan kamo"

ÆŠago ido ta yi ta watsa ma sa harara.

"Sorry Dear" ya faÉ—a yana kashe ma ta ido.

Su na cin abinci suna hira har su ka ƙoshi.

"Care to dance?" Ya faɗa yana miƙa ma ta hannu

" yau dai ina ga wani abun ka sha a wajen Ben ko?" Ta faÉ—a tana É—aga gira

Yadda ta ga ya haɗe rai ne ya sa ta yi saurin sa hannu cikin na shi ta miƙe.

Hannunta biyu ta ɗaura a kafaɗar sa shi kuma ya sa na sa hannun a ƙugun ta.

Kallon juna su ke kowa da abinda ya ke rayawa a zuciyar sa.
"Babu waƙa ai?"
Tsayawa yai da juyawar da su ke yi a hankali, ya sa hannun sa ɗaya dai-dai ƙirjin ta ya ce " daga nan waƙar ke zuwa"

Ta yi saurin sunkuyar da kanta tana murmushi.

"Zaytoon" ya kira da wata murya mai sanyi.

Ta É—ago a hankali tana kallon sa "kin san yau ne ya cika shekara É—aya da sati biyu da É—aura auren mu. Ni ma ban tuna ba sai jiya, kuma ke ma na san ba ki tuna ba"

Ta gyaÉ—a ma sa kai.

"Barin gaya mi ki wani sirri yau. Lokacin da Alhaji ya kirani ya min maganar za a ɗaura min aure da wata yarinya, i was furious. Ni na farko aure ba ya gaba na, na biyu har lokacin ina tuhumar kaina da mutuwar Alinah so ba na son mu'amala ta haɗa ni da wata mace. Na gaya mi shi ba zan iya auren ki ba amma sai ya nuna min dalilin sa na son haɗa auren, at first ban yadda ba daga baya sai na yadda. Lokacin da Mommyn ki ta kirani mu ka yi magana sai ta jaddada min za ta amince da auren ne idan har zan bari ki cigaba da karatu. She sound desperate so i obliged. The next thing sai ta turo min hoton ki wai na gani ko zan iya zama da ke a matsayin mata dan ba ta so a walaƙanta ma ta 'ya. Kin san mi ya faru?"

Zaytoonah ta girgiza kai

"Dariya na yi, na yi dariya saboda kin yi ƙarama, na yi dariya saboda ƙiban ki saboda ina ganin @16yrs kina da wannan ƙiba ai abun ya ɓaci. Ni da Ben lokacin mun jima muna dariya, but then bayan na sake kallon hoton sai na ji tausayin ki ya kamani. With all the details da Alhaji ya gaya min da kuma maganar da mu ka yi da Mommy sai na ga idan ban amince ba na zama marar tausayi kenan. Na gayawa Ben zan aureki ba dan komai ba sai dan ki samu kiyi karatu cikin sauƙi. Then na kira Mommy na ce kin min ba ni da matsala da ƙiban ki, infact ina son mata ma su ƙiba"

Zuwa lokacin hawaye ya gama wanke fiskar Zaytoonah. Ba abun da ta ke hangowa sai Zuhayr zaune da Ben su na kallon hoton ta suna dariya, ko wani hoto ma Mommy ta tura ma sa oho. Ita an nuna ma ta hoton sa tana murna ashe shi dariya ya dinga yi. Ba laifin sa ba ne tunda idan za ta yiwa kan ta adalci to ko da ba ta da ƙiba Zuhayr ya fi ƙarfinta.

"Shshhh dont cry please" ya faɗa yana ƙoƙarin share ma ta hawaye

"Zan je cikin gida" ta faÉ—a cikin muryan kuka.

"Dan Allah ki saurareni har ƙarshe, then you can decide what to do next"

Ya tallafo fiskarta ya ce " na kiraki na baki option biyu kuma ki ka zaɓi ɗaya. Ki ka zo gidana with the intention kin zo ki yi karatu ne ba kin zo zaman aure ba. Cikin watannin da mu ka yi tare na gane ko wacece Zaytoon. Na san abunda ta ke son ci da abinda ba ta so, na san irin kayan da ta fi so da wanda ba ta so. Na san ya ta ke dariya da yadda ta ke tsumewa, na san mutane mafi kusa da ita a rayuwarta, na san minene burinta a rayuwa, na san mi ya ke ba ta tsoro mi kuma ke sa ta farinciki. Mi ya ke jawo saurin fushinta mi kuma ya ke saurin kwantar ma ta da hankali. Na san wani sirri na ta wanda ba kowa ne ya sani ba"

"Mi ne?"

Yai murmushi ya ce "cin abinci hobby É—in ki ne, musamman ma nama"

"na san ƙarshe ma Kura za ka kirani" ta faɗa tana tura baki.

"I like you Zaytoon. The real you, the chubby you, I like you so much"

Ta yi saurin zaro ido tana kallon sa.

"Ina fata ko da kaÉ—an ne nima ina da matsayi a wajen ki?"

Ta girgiza kai

"Ba kya so na ko?"

Nan ma ta girgiza kai

"Kina sona?"

Ta tura baki ta ce "Bayan kai da Ben kun gama min dariyan shine za ka wani zo ka ce wai wai wai..."

Ya riga ya san lagonta, the moment ya haɗa bakin su to shikenan ba ta da ƙarfin yin wani abu kuma.

Kissing É—in ta ya ke yi a hankali and for the first time sai itama ta fara maida ma sa martani, itama yanzu ta gane yadda ya ke ma ta dan haka lokacin da kiss É—in yai nisa ita ta ke jagorantan su. Sun jima a haka kafin ya breaking kiss É—in yana faÉ—in "is that a Yes?"

Sai kuma ta ji kunya ta sunkuyar da kai tana dariya...

Hannun su sarƙe cikin na juna su ka shigo gidan kowannen su fiskarsa shimfiɗe da murmushi.
Suna shiga É—aki ya jawota jikin sa ya ce "na bari ki cika shatakwas ko kuma kin shirya?"

"Na shirya me?" Ta faÉ—a cikin rashin fahimta.

"Ki bani dama na gaida Baby na"

Cikin rashin fahimta ta kamo hannun sa ta É—aura akan cikinta tana faÉ—in "itama na gaida ka dan na san mace ce"

Yai dariyan wautar ta sannan ya ce barin nuna miki yadda ake gaida yaron ciki. Kafin ta ce wani abu ya shiga ba ta kiss mai zafi, this time around bai tsaya iya nan ba sai da ya tabbatar ya cikata ladar shi...

***

Exams ɗaya ya rage ma ta wanda za ta yi gobe. Tana kwance ƙasa tana duba littafi tana ɗan wasa da ƙafafuwanta. Bayan ya gama wayan da ya ke yi ne ya kamo ƙafuwanta biyu yana ma ta tafiyar tsotsa a tafin ƙafarta.

"Mr Ilyas You're distracting me"

Ya yiwa tafin ƙafar kiss ya ce " tafiyar mu ranan Thursday sai ki fara shiri"

Ta juyo da sauri tana murmushi ta ce " har da su Muhsina É—in za mu tafi?"

"Nope, gobe za su tafi kin san bikin ku na Nigeria sai a hankali"

"Jibe ka, sai ka ce kai É—in ba É—an Nigeria ba ne"

"In kin ce ni É—an Nigeria ne to na yarda amma ni na san Dad É—ina ne É—an Nigeria ni ba É—an chan ba ne"

"Allah ko! To sannu Ba Amurke É—an gidan Gorge Washington"

Rungumeta yai ya ce " kinga sai ki koma Mrs Washington kawai"

Ƙara shigewa jikinsa ta yi sannan ta ce "ban siyawa su Mommy komai ba"

"Bayan exams É—in ki na gobe sai mu fita shopping"

"Thank you D"

"D?"

"Ni fa D ɗin nan ban gane ma sa ba ƙila D for Donkey ki ke nufi"

"Kayya ba ranan na gaya ma ka ba"

"Ni gaskiya a dinga cikatawa idan aka ji D Donkey za a É—auka ki ke nufi"

Ta sa hannunta a kafaÉ—un sa ta ce "D for Darling, D for Dear, D for Dil, D for Daffodil, D for Dagger..."

"Dagger?"

"Yes Dagger, kai ne makamin da ke kareni a duk lokacin da na buƙaci kariya" ta ƙarisa maganar tana kissing goshin sa...

Kaman da wasa ana saura kwana biyu tafiyar ya ce ma ta za su tafi da Ben ne, nan da nan ya ga ta haɗe rai ta ce indai da Ben za a tafi ta yafe tafiyar. Ya yi rarrashin amma ta ƙi sauraron sa ƙarshe dole ya bi abinda ta ke so, ya samu Ben ya bashi haƙuri. Dama ba shi ne ya ma sa tayin tafiyar ba, da ya gayawa Ben ɗin za su je hutu Nigeria ne sai shima ya ce zai bi su musamman wai saboda yana son ganin yadda ake biki a Nigeria tunda a ƙarshen shekara za a yi bikin cousin ɗin sa Muhsina.
Ben bai ji daɗi ba amma saboda ya ƙara samun yardar Ben sai ya ce ma sa ya haƙura da tafiyar har da cewa ya taho ma sa da tsaraban Nigeria Zuhayr yai murmushi. Har ga Allah ya so su tafi da Ben ko don ya ƙara ganin yadda ake musulunci a Nigeria amma kuma farincikin Zaytoon ya fi ma sa komai yanzu.
Chapter 69 · 0% Book details