Sashe 79
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farha ta girgiza kai. Shigowar Mrs Haddish Kakar Zuhayr É—akin ne ya sa Zaytoonah ta maida hankalinta gareta.
"GrandMa, Zuhayr Zuhayr" sai kuma ta fashe da kuka. Mrs Haddish ta yi saurin ƙarasawa wajenta ta zauna bakin gadon tana ba ta haƙuri...
Anyi nasarar cire bullet É—in wanda ikon Allah ne ya sa bai kai ga zuciyar Zuhayr ba sai ya zama na gefen zuciyar ya tsaya. Bayan likitoci sun bawa Ben albishir É—in Zuhayr yanada 65% chance na rayuwa amma duk da haka ana so ya cigaba da addu'a. Kasancewar bai jima da treatment É—in Chemotherapy ba sai ya sa gaba É—aya jikin sa ya ke a sake.
An bawa Ben damar shiga ya duba Zuhayr briefly.
Ganin yadda Zuhayr ke numfashi ta Oxygen ya ƙara karya zuciyar Ben. Ya tsugunna a wajen ya kamo hannun Ben ya sumbata ya ce "i'm sorry my love, i'm very sorry"
Ya jima a wajen har sai da wata nurse ta shigo ta ce ya fita. Lokacin da ya kai bakin ƙofa juyowa yai ya kalli Zuhayr a ransa ya ce "its all her fault, but this time she wont go free"...
Zaytoonah ba ta kwantar da hankalinta ba har sai da aka turata a keke zuwa ɗakin da aka kwantar da Zuhayr. Duk da ta yi wa Mrs Haddish alƙawarin ba za ta yi kuka ba amma ganin Zuhayr a wannan yanayi ya karya ma ta zuciya. Kuka sosai ta ke yi wanda ya sa hawayen da Mrs Haddish ɗin ma ke dannewa dole su ka zubo...
Washegari Uncle Aliyu da iyalen sa su ka zo duba Zuhayr. A nan su ke gayawa Zaytoonah cewa su Alhaji Iliyasu ma na hanya, Visar da za ayiwa Mommy ne ma ya sa ba za su taho a ranan ba. Itakam Zaytoonah jikin da sauƙi sosai kuma babies ɗinta suna nan lafiya. Ta so a sallameta ma ta koma wajen Zuhayr amma Likita ya ce sai bayan kwana biyu idan ta samu ƙarfin jiki sosai.
Ben ko damuwa da halin da Zaytoonah ta ke bai yi ba, ko leƙa ɗakin da aka kwantar da ita bai yi ba balle ya sa ran zai gaisheta, duk da yana sane cewa tun jiya tana Asibitin...
Fitowar sa daga Asibitin ne ya ji wayar sa na ringing ya ɗau wayar ya amsa kiran wanda daga office ne ake buƙatar wani abu. Yana gama wayar ya fara laluba jikinsa ko zai ga ɗaya wayar sa amma wayam ba komai. Waya ce da ya ke dukkan ayyukan sa da shi hankalinshi ya tashi lokacin da ya tuna cewa saƙon text ya ke turawa hitman ɗin da ya ɗauka lokacin da ya ga halbin da aka yiwa Zuhayr.
Da gudu yai wajen motar sa dan komawa wajen da abin ya faru ko zai samu wayar duk da kuwa ya san da wuya dan tun jiya aka killace wajen police suna investigating wajen.
Lokacin da ya isa wajen daga cikin motar sa ya ke hango wajen da aka killace da ribbons na police inda police men ke shige da fice a wajen. Idan har ya je wajen za a zarge shi, sannan tunanin sa ya bashi a yadda police su ka yi ta sintiri a wajen tun daren jiya zuwa yau ba mamaki sun riga sun É—au wayar.
Za su ga saƙonnin da ya turawa hitman ɗin idan an bincika amma kuma ba lallai su san cewa shi ne mai wayar ba tunda da fake ID ya buɗe layin da ya ke amfani da shi. Da wannan tunanin ya sa hankalinsa ya ɗan kwanta ya juya kan motar dan ya je office sannan ya koma Asibiti wajen Zuhayr wanda har lokacin bai farfaɗo ba.
Tunda labarin abinda ya faru ya riski gida aka sanar da Alhaji Iliyasu. Hankalinsa ya tashi da jin wannan mummunan labari. Tuni ya ce a shirya ma sa tafiya zuwa Las Vegas dan ya je ya ga jikan sa. Da Hajiya Nenne za su je saboda Hajiya Saudah ba ta da lafiya. Daga baya Hajiya Saudar ta yiwa Alhaji magana akan a tafi da Mommy saboda itama ta ga lafiyar 'yarta. Hakan kuwa aka yi wanda ya tsaida tafiyar na su ba su samu zuwa ba sai ranan Monday wanda ya kama kwana shida kenan da harbe Zuhayr da aka yi.
Kafin su zo an ma sallami Zaytoonah dan ta ji sauƙi. Jikin Zuhayr ma akwai improvement sosai dan ya farfaɗo kuma yana gane mutane...
"Daddyn twins ya jikin?" Zaytoonah ta faɗa tana kissing goshin sa. Daga gida ta ke inda ta je ta ɗauko wasu kaya. Tun kwana huɗu da su ka wuce aka tabbatar mu su cewa Zaytoonah na ɗauke da 'yan biyu Maza, saƙon da ta fara bashi kenan ranan da ya farfaɗo, hatta hoton scan ɗin da aka yi sai da ta nuna ma sa ba shi kaɗai ba ma, Mommy da ke Nigeria ma sai da ta turawa hoton ta waya.
Murmushi yai mai ciwo saboda yadda ya ke jin jiki.
"Su Mommy na hanya yau. Ina ga zuwa dare za su iso nan"
A hankali ya furta "Allah ya kawo su lafiya"
Ta amsa da Amin.
Ta zauna gefen sa ta cigaba da yi ma sa surutu wanda duk zancen na ta gameda 'yan biyun su ne.
Ƙarfe shaɗaya na dare jirgin su Mommy ya sauka a Las Vegas. Daga airport aka ɗauko su da motocin Zuhayr har zuwa Asibitin. Duk da Zuhayr ya so ya ga zuwan su amma tuni yai bacci bayan alluran da aka ma sa.
Da su ka zo ba su tashe shi ba sun dai shiga ɗakin sun kalleshi sannan su ka fito suna yiwa Zaytoonah sannu. Zaytoonah ba kunya ta maƙale jikin Mommy tana zuba shagwaɓa.
Bayan an gama gaishe-gaishe sai Zaytoonah ta mu su jagora zuwa gidan su dan su samu su kwana gashi duk sun ɗebo gajiyar zaman jirgi. Dan ba direct daga Nigeria su ka iso Las Vegas ba sai da su ka shiga connecting flight sau biyu. Yadda su ka ɗau tafiya ba alaman tsayawa ya sa Alhaji ya tambayi ko garin za su bari Dreba ya ce a'a. Shi dai ya riƙe baki dan sun jima da wuce area ma su gidaje yanzu gidajen tsilla-tsilla su ke gani. Da su ka iso gidan kowa taɓe baki yai yana mamakin gidan, gida kusa da teku.
Bayan kowa ya samu masaukin sa ne Zaytoonah ta yi niyyar komawa Asibitin dan ta je ta kwana wajen Zuhayr amma Mommy ta hanata dan haka dole ta kwana a gidan.
Washegari da sassafe su ka ɗunguma zuwa Asibitin. Zuhayr ya ji daɗin ganin Kakan na sa sosai. Sun ji daɗin ganin ya fara sauƙi, kwanaki biyun farko da aka kawo shi Asibitin ma sai ka ɗauka ba zai yi rai ba saboda yadda ake ta sintirin ƙara ma sa jini da yi ma sa aiki...
***
Yau kwanan Zuhayr goma shatakwas a Asibiti kuma sauƙi sai daɗa samuwa ya ke yi babu wani complications. Su Mommy sati ɗaya su ka mu su suka koma Nigeria yanzu da ita da Mrs Haddish da Ben ne su ke jinyar Zuhayr hakan ya sa ta koma makaranta bayan Zuhayr ɗin ya buƙaci hakan. Investigation kam an cigaba da yi kuma abinda ba su sani ba shine sau uku ana kiran Ben yana zuwa police station yana amsa tambayoyi. Shi kan sa wannan tambayoyi da ake yawan yi ma sa ya sa shi haƙura da aiwatar da next plan ɗin sa a kan Zaytoonah. Yanzu neman hanyar da Zaytoonah za ta yi mutuwar da za a kira da natural death ya ke nema, duk cikin abinda ya rubuta na hanyoyin da ya ke so ya kashe Zaytoonah sai ya ga idan anyi bincike za a gano cewa kasheta aka yi shi kuma ba ya son haka dan yaga yanzu police na suspecting ɗin sa.
Sai da Zuhayr yai sati biyar a Asibiti sannan aka sallameshi, da farko a wheel chair ya ke zama kafin daga baya kuma ya koma amfani da walking stick, har su ka koma gida da walking stick ya ke amfani.
Kulawa na musamman ya ke samu daga wajen Zaytoonah da Kakarsa wacce ta tare a gidan saboda taimakawa Zaytoonah wajen kula da shi tunda tana zuwa Makaranta.
A dawowar su gidan ne su ka samu an chanja mai dafa mu su abinci daga Chef Green zuwa Chef Foster. A yadda da su ka samu labari daga sauran ma'aikatan Chef Green ne yai retire saboda tsufa da kuma ciwon sugar da ya ke fama da shi wanda a zahiri ba hakan ba ne. Shi ne ya kawo Chef Foster a matsayin wanda zai maye gurbin sa tunda shima ƙwararren wanda ya iya girki ne...
Watanni biyu ne su ka shuÉ—e da sallamar Zuhayr daga Asibiti wanda ya kama cikin Zaytoonah na wata bakwai, cikin da ake mugun tattalin sa. Tsatstsauran tsaro da takunkuni aka sa a gidan na su da ma duk inda za su je...
Bajewa ta yi a ƙasa tana cin gasashshiyar kifi yayinda Zuhayr ke zaune akan kujera yana yiwa kafaɗumta massage. Watanni huɗu na cikinta ba ta son cin abinci amma tunda ya shiga wata shida yanayin cin abincinta ya chanja, ta koma ci kamar gara.
"D har yanzu ba ka zaɓi suna ba fa" ta faɗa cike da shagwaɓa
"Da sauran lokaci ai"
"Tun a Asibiti kake faÉ—in haka har yau. Kaman yau ne fa wata tara zai cika"
Ya rankwafo kan sa ya kissing tsakiyar ƙeyar ta ya ce "ina jiran sunan da ya dace da su ne"
"Mu saka sunan Daddy na da Daddyn ka"
"My Dear kar ki damu za mu sa idan lokaci yayi"...
***
Bacci su ke yi hankali kwance. Kimanin kusan ƙarfe ɗaya na dare kenan. A hankali ya tako cikin ɗakin yana sanɗa har ya ƙarasa bakin gadon. Tulelen cikin Zaytoonah ya kalla sannan ya ɗaga wuƙar hannun sa sama ya daɓa ma ta nan da nan ta challa ƙara yayinda jini ya fara ɓulɓula har ta sama.
Ƙaran da ta yi a cikin mafarki ne ya kawota har waje.
Zuhayr yai saurin kunna bedside lamp da ke gefen gadon tareda jawota jikinsa yana lallashi.
"Zuhayr zai kasheni, zai kasheni"