Sashe 152
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan ta zo nan da kwana bakwai mai rai kaÉ—ai zai gan ta"
"Hakane Alhaji"
Dreban sa Malam Muhammadu ya faÉ—a yana jinjina kai.
Wajen yai shiru saboda jikin su da yai sanyi.
'Yan biyu da su ka fara faÉ—a a gefe ne ya É—auke shirun da su ke ciki. Daddy na mu su magana ma ba su kula shi ba. Sai da Malam Muhammadu ya daka mu su tsawa kafin su ka nitsu.
Kusan ƙarfe tara da rabi saura kaɗan Daddy ya ɗaga ido dan ya cewa Alhajin zai wuce gida sai ya ga idon Alhaji a rufe kamar mai bacci.
Ya kalli Malam Muhammadu ya ce "kaman Alhaji yayi bacci, mu zamu wuce"
"Sai da safe Malam Tijjani"
"Allah ya bamu alkhairi"
Daddy ya miƙe daga kan darduman yana cewa 'yan biyu su tashi su tafi.
Ko taku bakwai bai yi ba ya ji muryan Alhaji ÆŠayyabu ya kira sunan sa.
"Malam Tijjani" ya juya a hankali jikin sa a sanyaye.
Ganin su a tsatstsaye ya sa shi komawa baya da sauri.
"Inaga Alhaji fa rai yayi halin sa" Malam Muhammadun ya faÉ—a wanda tashin Daddy a wajen ne ya sa shi duba yanayin zaman da Alhaji yai a kan kujera. Ko da shima Daddy ya duba shi sai ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun a fili...
***
Mutuwar Alhaji Iliyasu Mai Auduga ya sa Zaytoonah ta ɗauke hankalinta daga kan maganar auren Galadima. Ya turo ma ta saƙon ta'aziya tunda ba ta ɗaukar wayar sa yanzu.
A ranan Jummu'a da aka yi sadakar uku ne kuma aka É—aura auren Mubaraka da Angonta Yusuf. Wanda Mai Martaba ne ya wakilci Ango shi kuma Galadima ya zama Waliyyin Amarya.
Hajia Ajwa kamar ta yi hauka saboda abubuwanta da su ka fara kwaɓewa. Mijinta Turaki da baya iya yi ma ta mu su shine ya ke iƙirarin sai dai ta mutu amma 'yar sa Mubaraka Yusuf za ta aura. Wai ta godewa Allah ma da Iyayen Yusuf ɗin su ka yafe ma ta abinda ta aikata da yanzun tana jail bisa laifin kidnapping ɗin Yusuf da ta sa aka yi na tsawon shekaru huɗu.
"Ajwa wani irin zuciya gareki. Ki sa a jefa É—an mutane a prison yana shan wahala ba tareda yayi laifin komai ba, har shekaru huÉ—u"
"Sai me idan na sa an rufe shi, ta ya zan bari Mubaraka ta auri É—an Talaka. Ba zai yiwu ba. Dama ban sa an kashe shi ba ko an haukatar da shi ka godewa Allah"
Turaki bai ce da ita komai ba dan maganar ba ta yanzu ba ne, ya wuce ya barta a falo tana banbamin bala'i ita kaÉ—ai.
Lokacin da 'yan É—aurin aure su ka dawo daga Fada ne labari ya riski Hajiya Ajwa akan ba wai auren 'yarta Mubaraka kawai aka É—aura ba harda auren Turaki da tsohuwar matar sa ta farko Hajiya Fatima. Hajiya Ajwa ta daka tsalle haÉ—eda saka ihuu kamar wata zararriya.
Ta shige É—akinta da sauri ta danna key sannan ta É—au waya ta fara kiran Bokanta. Tana fara koro bayani ya katseta da cewa ba shi ya ma ta aiki akan Uwargidan ta bai san komai gameda aikin ba. Ta katse kiran da sauri ta shiga nemo wani number daban, shima still ya ce ba shi ya ma ta aikin ba.
Zama ta yi a bakin gado gumi na tsatstsafo ma ta lokacin da ta tuno wanda ya ma ta aiki akan Hajiya Fatima, wani Bokanta ne a Cameroon shekaru shatakwas da su ka wuce kenan, kuma ya jima da mutuwa.
Aikin da aka yiwa Bilki lokaci guda ya cita Turaki ya saketa, ita kuma Hajiya Fatima na ta bai ci ba sai da aka haɗa ta da wani baƙin mutum sannan aikin da ya ma ta ya ci. An fara tura ma ta ciwo ne lokacin da ciwo ya cita yawan ibadarta ya ragu tukunna aka samu daman shiga tsakanin ta da Turaki.
Kashedin mutumin wanda munin fiskarsa da warin jikin sa ya dawo ma ta yanzu ta fara ji yana yawo a ƙwaƙwalwar ta.
"Idan ta fita daga gidan nan duk ranan da ta sake taka gidan da sunan matar sa komi kika shuka za ki girba. Ciwon da ki ka sa ma ta kema sai kin yi shi, bayan nan duk abinda ya sake biyowa baya kuma ki kuka da kan ki"
"Ai ba za ma ta dawo ba har abada" amsarta kenan a lokacin
Abinda ba ta sani ba shine akwai ƙaddaran da ya fi ƙarfin Boka ko Malami. Allah shi ke sarrafa lamurra, kuma shine Kun Fa Ya Kun.
Wato ɗaya ɓangaren gidan da aka gyara ta ke tunanin ɗan sa na biyu da zai yi aure ya ke gyarawa ashe na Hajiya Fatima ne.
"Ba zai yiwu ba, ba zai yiwu ba" ta faÉ—a a firgice kamar wata zararriya...
***
Da yamma bayan sun dawo daga gidan rasuwa ita da Mommy text É—in Galadima ya shigo.
*ki shirya gobe zan zo na É—auke ki*
Wani text É—in ya sake shigowa *ki duba whatsapp É—in ki za ki ga hoton Amarya tah*
Sai da ta yi kamar ba za ta duba ba amma kuma wani zuciyar ya ingizata. Bari ta ga wannan Amarya da ya ke ta É—oki akan ta.
Lokacin da ta clicking kan hoton da ya turo ƙirjinta sai dukan uku-uku ya ke yi. Sai dai ganin hoton ta ne ya sa ta zaro ido waje. Hoton ta ne ranan da za a kaita gidan Galadima.
"Ya kika gan ta, tana da kyau kuwa?"
Saƙon shi ya shigo bayan ta duba hoton. Sai da ta yi murmushi kafin ta tura ma sa reply.
"Ni bangan ta ba, ina ta ke?"
Yana zaune wajen da ake reception É—in aure amma hankalin sa na kan wayar sa, sai murmushi kawai ya ke yi.
Wani abokin sa da ke gefe ya tsokale shi ko dai nan kusa za su sha biki. Galadima yai murmushi kawai ba tareda ya ɗago ba ya cigaba da typing saƙon da zai turawa Zaytoonah.
Ya sake tura ma ta wani hoton daban, wannan su biyu ne su ka yi hoton. Selfie ne da ta mu su wata safiyar ranan sallah bayan ya gama shiryawa za su fita masallaci.
"Ya ki ka ga, na dace da ita kuwa?"
Zaytoonah ta rungume wayar a ƙirjinta tana dariya. Galadima akwai iya zura mutum a rijiya.
"Kin yi shiru"
"Ko kina kishin ta fi ki kyau ne?"
Ya sake tura ma ta.
"Kai ba!!! Tamm" ta tura reply haÉ—e da emoji na fushi.
"Ni Yunus É—an Muhammad, mi na yi?"
Ya tura da emoji na zare ido.
"Ka sani a layi, ka barni ina ta hauka akan ka ni É—aya ko"
"Ba ke kaÉ—ai ki ke haukan ba, i'm crazy for you too"
Goge ido ta yi da sauri ta sake karanta saƙon da ya turo a karo na biyu.
Did he just say he's crazy for her?
"Yadda ki ka wahalar da ni, haka za ki zo ki karɓi hukunci mai tsauri a wajena. And dont expect mercy Baby"
Saƙon sa na ƙarshe kenan kafin ya sauka.
Zaytoonah ta rufe fiska tana dariya. Gaskiyar Mommy da ta ce ma ta wani lokaci ƙwaƙwalwarta kamar na kifi ne.
Daga jin maganar aure har ta hau dokin kishi. But ya za ta yi, she's just so crazy inlove witn this old man...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 74
Bismillahir Rahmanir Rahim
*a second chance*
Tana tararradin ya za ta yi ta gayawa Mommy akan za ta koma gidan ta gobe, duba da yadda ta ringa cika baki akan ba za ta koma ba kwanan baya. Allah da ya so wanketa sai ya sa Mommyn da kan ta da suna cin abincin dare ta ce ta shirya gobe ko jibi ta kuma gidan ta dan nan da kwana huÉ—u jirgin su zai tashi.
"Ki dena korar min 'ya Dan Allah" Daddy ya faÉ—a yana kallon Mommy
"Da wai nufinka ta cigaba da zama a nan ne?"
"Kwantar da hankalin ki Hajiya, Mijinta zai zo ya É—auketa gobe Insha Allahu"
Zaytoonah ta rufe ido da hannunta.
Salman ya ce "aga aga, aga waye ya ce ba zai koma gidan..."
"Salman"
"Soryy Daddy" ya faɗa yana ƙunshe dariyar sa.
"To ai gaskiya ya faÉ—a. A nan dai wata ta dinga cika mana baki ita ba za ta koma gidan ta ba"
Dariyan da Salman ke ƙunshewa ne ta fito, Mommy ma ta fashe da dariya. Junior da Humairah ma sai kawai su ka fara dariyan. 'Yan biyu ba sa wajen suna gidan rasuwa Muhsina da su ka zo jiya ne ta hana su tafiya shiyasa su ka kwana a wajen ta.
Zaytoonah ta miƙe da sauri ta yi ɗaki da gudu.
Daddy ma sai a sannan ya fara na shi dariyan yana yi yana faÉ—in wai su bar yiwa Princess É—in sa dariya fa.
Zaytoonah kunya ya sa ta ka sa fitowa. Duk da ta ji haushin dariyan da su ka ma ta amma kuma hakan bai hanata jin daɗin kulawar da ta samu daga wajen iyayen ta da 'yan uwanta ba, musamman Salman. Salman ya wuce ƙani a wajenta. He's more of a best friend to her. Har yau idan ka cire Farha da Muhsina to ba ta da wani abokin shawari da ya wuce Mommy da Salman. The kind of childhood ɗin da ta samu ya sa ba ta da tsayayyun ƙawaye. 'Yan Makarantar su na Primary da na Secondary ko na Islamiyya duk zumuncin ya buge a iya chatting a whatsapp ne, shima dalilin buɗe groups na excos ya sa ma ta tuna da wasun. Wasu daga baya sun yi ta ƙoƙarin manne ma ta jin cewa tana auren Galadima. Wasu kuwa hassada ya sa sun ka sa kulata ko da a group ɗin ne.