← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 161

Sashe 38

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba matan ba har mazan suna kiranta da annoying sunaye. Abinda ba ta sani ba shine ba ƙiban kaɗai ke jawo ma ta wannan izgilanci da 'yan class ɗin su ke yi ba, tun JSS1 har yanzu da su ke JSS 3 ita da Smally su ke ɗaukan na ɗaya da na biyu. Idan ta ɗauka wannan karan zaka ga wani karan Smally ya dage ya ƙarɓa itama wani term ɗin ta ƙwace kayanta haka su ke yi.

Saboda wannan jarraban judging ɗin ta da su ke yi ne ya sa ba ta da ƙawa. Ba ta da wanda ta ke wani mu'amala da ita, Nuratun ma ita ke shishshige ma ta...

***

Shekara biyu kenan da dawowar T J kuma cikin shekaru biyun nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa hadda wani faÉ—a da su ka yi wanda ya sa Maryam É—in ta yi yaji, ba yaji kaÉ—ai ba barin garin Zaria ta yi gaba É—aya kuma ba Ringim ta je ba hakan ya saka T J cikin tashin hankali.

Abunda ya faru shine, kafin T J ya dawo Maryam ta yi sauka amma ba Hadda ba Tartil. Bayan tafiyan T J ƙasar waje ta shiga wani Islamiyya da ake yi da safiyar Asabat da Lahdi, a nan ta cigaba da ɗaukan karatu. To ganin T J ne malamin ta na farko ya sa ta ɗaga Waliman saukar ta zuwa sai ya dawo.
Bayan wata biyar sai gashi ya dawo ya kammala Phd É—in sa ya zama Dr Tijjani Abubakar Modibbo Djibo.
Waliman saukan Maryam da ta kammala Phd É—in sa su ka haÉ—a bayan sati biyu da dawowa aka yi.
To daren ranan saukar su ka fara buɗe kyaututtukan da aka ba ta, kasancewarta revert wato wacce ta musulunta kuma har ta tsaya ta yi karatun Ƙur'ani ta gama, hakan ya sa mutane da dama da su ka halacci waliman su ka ba ta kyaututtuka.
Bayan an gama buɗe kyaututtukan ne T J ya fito da makullin mota ya damƙa ma ta, har ta fara murna sai ya ce kyauta ce daga ƙanin sa Alhaji Muntari. Tana jin sunan Muntari ta yi cilli da key ɗin motar ta ce ya mayar ba ta so.

"Maryam wai mi ya ke faruwa ne? The last time da na ce mu je mu gaishe da matar sa da ba ta da lafiya kin ce Allah ya kiyaye ki taka gidan Muntari. Na tambayeki ba ki bani takamaimai amsar abinda na tambaya ba"

"Ni dai ka mayar ma sa key É—in nan, idan ma akwai wani kyautan da ya fito daga hannunsa a nan ka cire ba na so"

"Maryam miyake faruwa ne? Akwai abinda ya miki da ya kamata na sani ne? Duk abinda yai Maryam bai kai ki dinga nuna ma sa ƙiyayya haka ba. Ba tarbiyyan musulunci ba ne"

A lokacin tana son faɗa ma sa komai gameda Muntari amma abinda ya faɗa ya ɓata ma ta rai shaiɗan ya kuma tunzura ta sai ta hau tabarmar fushi ta tashi ta bar ma sa ɗakin. Ranan a ɗakin Zaytoonah ta kwana.
Washegari dukkan su suka tashi da jin haushin junan su. Ba wanda yai magana da É—an uwansa.
Zuwa yamma Tijjani ya nemi su sasanta tareda ba ta haƙurin tsawa da ya ma ta. Ce ma sa ta yi komai ya wuce ashe ba haka ba ne. Ranan da ya koma gidan Hajjo ta haɗa wa su daga cikin kayan ta ta bar gidan. Takarda ta bawa Zaytoonah akan idan Daddynta ya zo ta ba shi. T J bai samu ya zo duba su ba sai yamma liƙis. Zaytoonah ta ba wa T J envelope ɗin ta ce Mommy tun safe ba ta dawo ba har su ka dawo daga Islamiyya ba ta nan, Auwal ne ya mu su girki.
Hannu na rawa ya buÉ—e envelope É—in ya fara karantawa.

*Ba kai kaÉ—ai ke da 'yan uwa ba da za ka min gori akan Muntari. Na tafi neman 'yan uwana tunda ba daga sama na faÉ—o ba. Kar ka neme ni dan ba zan dawo ba sai na same su. TARBIYYAN MUSULUNCI bai ce na yi watsi da 'yan uwana ba ko da su kafirai ne*

Sun taɓa maganan sake neman 'yan uwan mahaifiyarta a shekarun baya ta hanyar ba da sanarwa a gidan talabijin a Calabar amma kuma T J ya nuna ma ta ba lallai su same su ba haka nan kuma zai iya yiwuwa garin son neman 'yan uwan mahaifiyarta ta ci karo da Uncle ɗin ta wanda ya kashe ma ta iyaye. Haka dai yai ta convincing ɗin ta har ta haƙura da batun neman, musamman ma da ya ke wani hidiman kashe kuɗin za su yi kuma ba su da kuɗin a lokacin.
Sun bar shi akan idan lokaci yayi da kan sa zai rakata su neme su.

Wasa-wasa kwana biyu ba Maryam ba dalilinta, faɗin tashin hankalin da T J ya shiga ma ɓata lokaci ne har Ringim ya je ba ta nan kuma Goggo ma ba ta da masaniyar inda ta tafi.
A kwana na huɗu ne ya shirya tafiya zuwa Calabar zai tafi nemanta duk da bai san ta ina zai fara ba. Idan bai samu labarin ta a nan ba dole ƙauyen su zai je.
Muntari ma jin labarin Maryam ba ta gida hakan ya tayar ma sa da hankali shima ya kawo motar sa da dreba akan su tafi neman tare. Har sun kama hanya
sun fara tafiya sun yi nisa aka kira wayar Muntari saboda lokacin ne aka fara yayin waya kuma Alhaji Muntari ya siya saboda waya a lokacin sai Alhaji wane ko Honorable wane.
Daga gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga ne aka yi kiran aka bawa Auwal yai magana da Muntari ya ce Mommy ta dawo. Jiki na rawa T J ya karɓi wayan ya shiga jerawa Auwal tambayoyi dan ya tabbatar gaskiya ne ba ƙarya ba.

Kusan shaɗayan dare ta gota su ka iso Zaria. Kai tsaye a ƙofar gidan Maryam su ka tsaya T J ya shiga gidan da gudu. Shi ma Muntari ya so shiga amma kuma baya son Maryam ta gan shi ta fara masifa dan haka ya ce Dreba ya juya da shi gida.

"Maryam why? Kasheni za ki yi ne? "Kin san tashin hankalin da na shiga a rashin ki? I love you Maryam, please dont ever leave me again" Ya faɗa kamar zai yi kuka yana rungume da ita ƙyam a jikin sa.

"Gidan Hajiya Fatima na je a Abuja" abunda ta faÉ—a kenan bayan ya saketa.

"Maryam dan Allah kar ki sake irin wasan nan kin ji. Idan na rasa ki mutuwa zan yi"

Ehem kawai ta iya cewa...

Daren ranan T J bai iya baccin kirki ba, motsi kaÉ—an ya tashi ya duba ko Maryam na nan ko kuma ta tafi.

A ɓangaren Maryam ta yi niyyar tafiya neman 'yan uwanta kamar yadda ta rubuta amma bayan ta bar gidan ta rasa ta ina za ta fara. Shekaru sun ja kuma ba ta da wani valueable information akan 'yan uwan mahaifiyarta da ya wuce sunan Kakanta Chief James Asibong, mahaifiyarta na da ƙanne 'yan biyu maza Paul and Peter sai sunan Kakarta mace Elizabeth. Wannan kaɗai bai isa ta same su ba ga uwa uba ba wani kuɗi ta riƙe a hannun ta ba.

Gidan Hajiya Fatima ta wuce a Abuja dan a lokacin tana buƙatar kaɗaici.
Kwana biyun da ta yi ba ta tareda Mijinta da 'ya'yan ta ba, kwata-kwata ba ta da kwanciyar hankali. T J da 'ya'yan su biyu su ne familyn ta yanzu. Ta ya ma za ta yi tunanin tafiya wata duniya ta bar 'ya'yan ta, jinin ta?.
May be she's just exaggerating about Muntari. Yes ya ma ta laifi a baya amma kuma tun bayan da yai aure da watanni kaɗan ya dena aiko ma ta da abubuwan da ya ke aikowa da. Ya dena shiga sabgar ta, iya ka ci yana aikowa 'ya'yan ta kyaututtuka. Bayan ta gama ba wa kanta haƙuri ta koma gidan ta...

T J bai sake ma ta maganar Muntari ba dan Kaffa-Kaffa ya ke da ita. Duk wani abun da zai ɓata ma ta rai har ta kawo tunanin rabuwa da shi baya so.

Shekara ɗaya bayan faruwan haka aka ma ta transfer zuwa Kaduna. T J bai yi wata-wata ba ya amince ma ta ta fara zuwa, duk da kuwa jigilar jeka ka dawo ta ke yi kullum tsakanin Zaria zuwa Kaduna. Bai taɓa complain ba duk da jigilar kuɗin mota da ake yi.

Wata takwas ta yi tana aiki ta ajiye aikin ta cewa T J za ta zama Barrister mai zaman kan ta kawai. Akwai wani private Law firm da wani babban Lawyer ya buÉ—e a Zaria nan ta koma tana zama a chamber É—in su...

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*16-Confession*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Har aka kawota asibiti ba ta farfaÉ—o daga suman da ta yi ba. Kuka kawai Maryam ke yi Salman na tayata. Salman ne ya tashi zai shiga banÉ—aki ya ga Zaytoonah kwance a sume shine ya fara ihu yana kiran Mommy. T J baya gari ya tafi Ringim duba gonar sa dan haka Muntari ne ya kawo su Asibitin tunda yana da mota.

Mommy na zaune tana hawaye shi kuma Muntari na lallashi. Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda Maryam ɗin ta birkice lokaci guda.

"Dan Allah ki dena kuka Maryam addu'a za ki ma ta. Kinga dai Salman ma kukan ya ke"

Ba tareda ta damu da abinda ya faru tsakanin su ba ta ce "Thank you Muntari"

Shi kuwa yai murmushi.
Chapter 38 · 0% Book details