← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 161

Sashe 56

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam sai da ta ga 'ya'yan ta Salman da Junior kafin hankalinta ya kwanta har ta samu damar yin wanka ta ci abinci kafin daga baya su ka wuce police station dan ta je ta ba da statement. Ko kaÉ—an ba ta tunanin za ta ragawa Muntari a wannan karan, sai ta yi duk abinda za ta yi dan ta ga bayan sa once and for all.
Zuwa yamma labari ya karaÉ—e ko'ina na abinda Muntari ya aikata na sace Maryam da yai.
Tuni ya contacting lawyer É—in sa akan a yi bail É—in sa amma hakan bai yiwu ba, strict order aka bayar daga sama akan kar a yadda ayi bailing É—in sa...

Duk abinda Zuhayr yai Auwal bai ɓoye wa Maryam ba, ta jinjina ma sa ta kuma yi farin ciki sosai saboda ko ba komai ya nuna ya damu da damuwar 'yarta Zaytoonah. Ta so kiran sa da dare da ta samu sarari amma ta san a wajen su dare yayi nisa sosai ƙila suna bacci shiyasa ta haƙura zuwa safiya.
Washegari da safe da ta kirashi yana office lokacin, ta ma sa godiya bisa taimakon sa gareta, ya nuna ma ta ai ba komai. Tambayar sa ta yi ko Zaytoonah na ba shi matsala ya ce ma ta a'a sai kuma ya ce eh. Maryam ta É—an ji wani jim a zuciyarta, cike da damuwa ta tambayeshi laifin Zaytoonah.
In a serious tone ya ce "tana cin abinci da tsakar dare, har kwana a kitchen take yi"

Maryam sai ta sa dariya shima ya biye ma ta da dariyan. Chan ta ce "ai Zaytoonah da abinci sai a hankali"

Haka dai su ka É—an yi hira kaÉ—an wanda duk akan Zaytoonah ne kafin ta katse kiran.

A school Mommy ta kira Zaytoonah, ta fito daga class za ta je cafeteria cin abinci wayar ta tayi ringing. Tana É—aukan wayan da ta ji muryan Mommy ta daka tsalle haÉ—eda sa ihu, wanÉ—anda su ke gefenta su ka juyo suna kallon ta. Har ta gama wayan babu nitsuwa a tattare da ita, wani lokaci ta sa ihu,wani lokaci dariya, wani lokaci kuma tsalle.
Da ƙyar ta iya attending class ɗaya da ya rage ma ta a ranan. Mr Smith na zuwa ta ce ya kaita kamfanin su Zuhayr.

Da tambaya aka ma ta kwatancen office ɗin Zuhayr wanda ke hawa na ƙarshe. Elevator ta hau wanda ya kai ta wajen, office ɗin Sakatariyar sa ta fara shiga inda ta nuna buƙatar ta na son ganin Mr Zuhayr.
Sakatariyar ta danna ma sa kira, daga inda ya ke zaune yana duba wasu files ya danna wani baƙin botton a jikin phone ɗin ya ce "yes"

Sakatariyar ta ce "Zoyuna is here" yana jin muryan Zaytoonah lokacin da ta ke gyarawa Matar sunan ta.

"Send her in" ya faɗa a taƙaice

Cike da É—oki ta shiga office É—in tana kallon yadda ya tsaru yai kyau.

"Guess what Zuhayr?"

Ya É—an É—ago ido ya kalleta sannan ya ce "what?"

"An samu Mommy, ashe Uncle Muntari ne ya saceta, shege tsinanne" ta faɗa cike da jin haushin ƙanin Baban na ta wanda tunda ta san shi bai taɓa burgeta ba and he's always causing them trouble.

"Good" ya amsa a taƙaice.

"Good kuma? Kai da za ka tayani murna. We are supposed to celebrate this goodnews"

"After your exams" ya faÉ—a ba tareda ya É—ago ba,
Jikinta ne yai sanyi saboda yadda ta ga fiskan sa ba ta ga alamar yana tayata farin ciki ba amma kuma Mommy ta ce da taimakon sa jami'an tsaro su ka kama Muntari.

Shi kuwa a ɓangaren Zuhayr bayan sun yi waya da Mommy asibiti ya wuce saboda ya karɓi sakamakon series of tests da aka ma sa satin da su ka wuce. Bayanin likitan ya ɗan girgiza shi shiyasa ma ransa ya ke a jagule.

Ganin ya manta da ita a office ɗin ne ya sa ta ce za ta koma gida ya ce ma ta sai anjima. Tana buɗe ƙofa su ka yi kiciɓis da Ben wanda ke shirin shigowa da wani file a hannun sa, ganin Zaytoonah sai da zuciyar sa ta buga da ƙarfi.
Ba ta ma sa magana ba haka ta raɓa ta gefen sa ta wuce tunda shi bai matsa ba sai ma wani mugun kallo da ya ke aika ma ta...

Jiki a sanyaye ta koma gida tana tunanin mi ya ke damun Zuhayr ɗin bayan ta san ba haka su ka rabu da safe ba, infact tarema su ka yi breakfast. Chan ta tuna da maganar da su ka taɓayi da wata baturiya wanda yanzu sunan ta ma ta manta, ta tashi da sauri ta fara neman katin da matar ta bata amma ko sama ko ƙasa ta rasashi, tafi tunanin ranan da ta ke tattare kaya akan za ta koma Nigeria ne ta yar da shi. Ta ji haushin hakan sosai, daga baya kuma ta tuna da Muhsina dan haka ta danna ma ta kira, a kira na biyu ta ɗauka.
Bayan sun gaisa Zaytoonah ta tambayeta waye Alinah?.
Daga ɓangaren Muhsina ta ce "ai na san ba zai gaya mi ki ba, ex fiancee ɗin sa ce da ta kashe kan ta kusan shekaru inaga zai kai ko bakwai ko shida haka"

Zaytoonah ta dafe ƙirji ta ce "kisan kai fa!"

"Iyi, Allah ne masanin komai amma gaskiya ba mu ji daɗin abinda ta aikata ba. Saura ƙiris fah ayi auren, wallahi duk wani shirye-shirye anyi muma muna shirin zuwa Las Vegas ɗin kenan mu ka ji labarin mutuwarta. Abin ba daɗin gani"

"Dan Allah kinada hoton ta?"

"Gaskiya sai dai na duba dan abin ya jima, ko high school ban gama ba lokacin da abin ya faru. Idan na samu zan tura miki"

Zaytoonah ta ma ta godiya ta kashe wayan tana nazarin maganganun Muhsina da kuma maganar da matar nan ta gaya ma ta. To wannene gaskiya?

***

A Nigeria kuwa daga Ringim aka zo bawa Maryam haƙurin abinda ya faru da kuma roƙon ta janye ƙarar Muntari saboda a rufe case ɗin dan kar mutuncin sa ya zube. Maryam kam jin su kawai ta ke yi tana girgiza kai dan ko T J ya zo yau ya ce ta yafewa Muntari ba za ta yafe ba. Idan hauka ya ke yi gara ya je ya ƙarisa a gidan yari ita ba damuwarta ba ne.
Abin mamaki sai ga Iya ta kirata a waya tana ba ta haƙuri. Ba haƙurin abubuwan da ta ma ta a baya ba, ba haƙurin ɓangarenci da ta ke nuna ma ta har yau ba sai dai wai ta yi haƙuri ta yafewa Muntari a kashe maganar ba sai anje kotu ba.

"Iya kin san Allah ko mijina ne ya dawo yau ya ce na janye ƙarar nan ba zan janye ba. Na gaji da yin haƙuri saboda wani mutunci. Mutunci ya ƙare lokacin da Muntari ya sa aka sace ni, mutunci ya ƙare lokacin da ya yi iƙirarin kashe 'ya'yana idan ban bi son zuciyar sa ba. Ko da kotu ba za ta bani nasara ba ba zan janye ba har sai mun kai kotun Allah ya isa kafin na bar shi da Ubangijin da baya zalunci" daga haka ta kashe wayar tana tunanin son zuciya ta mutane. Da Iya da sauran ma su cewa ta yi haƙuri duk munafukai ne abinda ta sawa ranta kenan.
Sun yi waya da Goggo kan maganar saboda ciwon ƙafa da ta ke fama da shi ba ta samu ta zo ma ta ba amma ta ba ta goyon baya ɗari bisa ɗari akan ta cigaba da ƙaran. Idan har Muntari bai yi hankali ba a shekarun sa sama da Arba'in ba ta san ranan da zai yi hankali ba kuma, gara a haɗa shi da hukuma kawai.

A Nigeria inda ake iya kuɗin ka iya shagalin ka. Duk inda lawyer mai kare Muntari ya kai da neman cin nasara hakan bai yiwu ba. Yadda Muntari ke sawa ana ta zuba kuɗi ana bribing mahukunta hakan bai yi tasiri ba domin duk inda ya ke ji da kuɗi wanda ke sponsoring lawyer ɗin Maryam ya taka shi. Zuhayr ya yi alƙawarin indai kuɗi ne ke aiki a Nigeria to dole sai an tura Muntari gidan yari.
Hakan ne kuwa ta faru dan shari'ar da aka fara yi a Kaduna bayan duk wani bincike da aka yi, bayan kuma an yi zaman kotu sau uku ana ɗaukaka ƙara to Alkali ya yankewa Muntari hukuncin zaman gidan Yari na shekaru goma tareda biyan kuɗi naira miliyan biyu.
Ofcourse an ɗaukaka ƙara zuwa court of Appeal wanda a nan ma fa shari'ar ba ta ba wa Muntari gaskiya ba domin kuwa shekaru bakwai a gidan Yari aka yanke ma sa tareda mayarda kuɗin da zai biya na tara zuwa miliyan ɗaya kacal. Haka aka tinƙisa ƙeyar sa zuwa gidan yari. Ko maganar sake ɗaukaka ƙara Lawyer ɗin sa bai yi ba dan evidences da Maryam ta kawo a zaman su na ƙarshe ya ƙara incriminating Muntari ne. Maryam Barrister ce dan haka ta san yadda kotu ke aiki, shiyasa ta tanadi bayanai da shedunta wanda su ke da ƙarfi sosai, ko sun je supreme court ɗin ma dole za a punishing Muntari sai dai kawai za'a dai iya rage ma sa shekarun da zai yi a gidan kaso, kuma ya ga alama ma su goyon bayan Maryam manyan mutane ne da su ka taka Muntari dan haka kuɗi ba zai juya shari'ar ba.
Chapter 56 · 0% Book details