← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 161

Sashe 66

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsugunnawa yai a gabanta ya ce ta hau bayan sa. Zaytoonah ta zaro ido tana ganin kamar ba zai iya É—aukan ta ba duk da kuwa ta san idan ba É—aukan ta aka yi ba a yadda takeji ba yadda za ayi ta iya tafiya mai nisa, tsayuwa ma da ta yi a wajen daurewa kawai ta yi.

"Ki hau dan Allah Zaytoon"

Wata baturiya ta ce wa Zaytoonah kar ta damu ta hau bayan sa.

Tuni an kai mu su jakukkunan su zuwa wajen motar dan haka su kaɗai ake jira. Bantareda ya damu da nauyinta ko kuma shigar da ta yi da ya ƙara ma ta nauyi ba haka ya ke tafiya da ita a hankali har su ka kai wajen motar. Zaytoonah ta lafe a bayan sa tana jin wani daɗi na ratsa ilahirin zuciyarta. Ba ta taɓa zaton Zuhayr na da sauƙin kai haka ba.
A cikin mota ma lafewa ta yi ajikinsa shima ya riƙeta gamgam.

Asibiti su ka fara wucewa, inda yai wa likita bayanin Zaytoonah matar sa ce sun zo yin honeymoon shine ta faɗa cikin ƙanƙara kuma ba a ganta da wuri ba, da aka ganta kuwa sanyi ya kamata sosai har ta suma acikin ruwa, shine ya mata taimakon gaggawa. Ya faɗi hakan ne kar a binciki Zaytoonah ayi zargin raping ɗinta akayi.

Bayan an shiga da Zaytoonah ciki ya zauna akan kujera tareda dafe kan sa yana tunanin abinda ya faru da kuma abinda ka iya biyowa baya idan har ya faÉ—awa Zaytoonah gaskiya. A haka Ben ya kirashi yana tambayar inda ya ke, sai da ya ga sunan Ben ma ya sa shi tunawa ko neman sa bai yi ba lokacin da su ka tafi.
Bayan ya ma sa bayanin abinda ya faru a ɓangaren Ben cillar da wayar yai yana huci. Jiya kasa bacci yai dan haka ya fita daga ɗaki yai ta tafiya sa da yai nisa da su sosai sannan ya tsaya a wajen wani bishiya ya dunƙule hannu yana dukan bishiyar saboda ya ji sauƙin raɗaɗin kishi da baƙin ciki da ya ke ji gameda abinda Zuhayr ke aikatawa da Zaytoonah. Har sai da hannun ya fara jini kafin ya haƙura da bugun bishiyar. Ya zauna ya fara kuka, kuka sosai dan ya jima yana hana mata raɓan Zuhayr tun lokacin Zuhayr bai damu da addini ba ma. Akwai lokacin da su ke makaranta su ka je wani party har Zuhayr ya haɗu da wata yarinya ya ɗauketa da niyyar za su je gidan sa su huta. Ben na biye da su yana kitsa azuciyar sa abinda da zai wa yarinyar idan har Zuhayr ya raɓeta. Suna zuwa gidan su Yarinyar ta ce za ta shiga banɗaki sai da Zuhayr ya manna ma ta kiss kafin ya barta ta fita daga ɗakin, ya kwanta kan gado yana jiran ta dawo.
Har kusan minti shabiyar babu alaman za ta shigo É—akin, hakan ya sa ya fita dan ya dubata amma Ben kawai ya gani a falo yana kallo. Zuhayr ya tambayeshi ina Samantha? Ben ya ce ta tafi wai ba za ta iya haÉ—a jiki da Musulmi ba. Zuhayr yai tsaki ya koma ciki yana jin haushin kan sa ma da ya É—auko Samanthan tun farko.
Ita kuwa Samantha gudun fanfalaƙi ta yi saboda Ben da ya tsoratar da ita da bindiga lokacin da ta fito daga banɗaki za ta koma ɗakin Zuhayr.

Giya Ben ya fito da shi yai ta sha har sai da yai tatil kafin ya ɗauko wani haɗin sa cikin ƙaramar kwalba ya kwankwaɗe duka, hakan ya sa bacci mai nauyi ya ɗaukeshi a wajen duk wani sanyi ya sauka a kan sa amma baya cikin hayyacinsa balle sanyin ya dameshi...

Duk taimakon da ya kamata a yiwa Zaytoonah an mata, sun ce za su riƙeta zuwa washegari kafin a sallameta.
Taimama ta yi a asibitin ta yi sallah a zaune bayan ance ma ta kar ta taɓa ruwa sai gobe.
Lokacin da Zaytoonah ta cewa Zuhayr za ta yi taimama ta yi sallah hankalinsa tashi yai saboda a É—an iya karatun sa ya san idan aka yi irin abinda su ka yi jiya da dare to ana wankan tsarki kafin ayi sallah, shima da ya je hotel É—in su ya yi wankan sannan ya rama sallolin da ya wuce shi. Malam Google ya tambaya amma bai gamsu da bayanan sa ba dan haka ya kira Uncle Aliyu ya tambayeshi. Shima dai bai sani ba amma ya ce ya dakonce shi nan da 'yan mintuna. Kafin ya kira tuni Zuhayr ya kira Shiekh Hassan ya ma sa tambayar inda Sheikh ya ce za a iya yin taimama ayi sallah idan mutum ya warke sai yai wankan, ya kawo hadisi da ya supporting fatawar da ya bayar dan haka hankalin Zuhayr ya kwanta dan tuni Zaytoonah ta yi taimama ta fara sallah. Kafin Uncle Aliyu ya kira sai bayan kusan awa É—aya da rabi inda shima ya ma sa bayanin da Sheikh Hassan ya ma sa.
A asibitin ya kwana tareda matar sa wanda duk wani motsinta yana idon sa. Washegari sai kusan da rana aka sallamesu bayan an sake duba Zaytoonah aka hanata mu'amala da ruwan sanyi sannan aka bata magunguna na sha da na shafawa a jiki.

Bayan sun koma hotel É—in ne ya tara ma ta ruwan zafi ya ce ta yi wanka. Lokacin da za ta shiga banÉ—akin ya kira sunan ta a hankali "Zaytoon" ta juyo tana kallon sa
"Ki yi wankan tsarki kafin ki fito"

"Wankan tsarki?" Ta maimaita da mamaki

Sai da yai gyaran murya kafin ya ce " ba ki ga likita yayita tattaɓa ki ba jiya? kuma nima na kwanta kusa da ke, duk wannan zai iya sawa ki ji wani abu a ranki. So best option shine ki yi wankan tsarki"

Kan Zaytoonah ya kulle, ta dai yi karatu a Islamiyya dai-dai gwargwado amma kuma anya wannan bayanin da Zuhayr yai ya kai ta yi wanka? Ita fa ba ta ji komai ba. Ranan da za ta iya cewa ta ji wani abu da aka taɓata shine ranan da Zuhayr ya kissing ɗin ta a gym room dan da ta koma ɗaki za ta yi wanka sai da ta ga pant ɗinta ya jiƙe.
For the benefit of doubt ta gyaÉ—a ma sa kai alamar za ta yi wankan.

Kwana biyu su ka ƙara a ƙasar su ka tattara su ka koma America saboda makarantar Zaytoonah. Ben kam tuni ya wuce bai bi ta kan su ba dan haushin Zaytoonah da ya ke ji yana gani kamar idan ya ganta kusa da Zuhayr zai iya zuwa ya shaƙeta har sai ta mutu.

Zuhayr kam duk yadda ya so ya faÉ—awa Zaytoonah abinda ya faru tsakanin su ya kasa. Gani ya ke idan ya faÉ—a za ta iya gudun sa.

Duk bayanin da ta ma sa na abinda ya faru har ta fita a daren ranan bai gamsu ba dan ya duba wayar sa babu kira babu text da aka tura, itama na ta wayan babu text ɗin da ta ce an turo. Ya dai lallaɓata akan ta bar zancen tunda an sameta kuma she's alive an healthy.

Sai da su ka koma gidan su da ta ga Ben sai wasu abubuwan su ka fara zuwa ma ta, possibility na yiwuwar Ben ne ya tura ma ta saƙon nan da wayar Zuhayr ya zamo ma ta 90% idan kuma har hakane to kuwa shine ya turata cikin ƙanƙara.
Ta dai yi shiru da bakinta ba ta gayawa Zuhayr komai ba.

Yau tana kitchen tana haɗa banana and avocado smoothie sai ga Ben ya shigo kitchen ɗin. Haka kawai sai ya ɗau wuƙa da Albasa ya zo kusa da Zaytoonah da ke ƙoƙarin zuba ayabar da ta yanka cikin blender, ya ajiye chopping board ya fara yanka Albasa da sauri-sauri irin yadda professional chefs ke yi. Albasar ta yanku ƙanana amma bai tsaya ba ya cigaba da bi yana ƙara yanyankawa.

Tun Zaytoonah ba ta damu da abinda ya ke yi ba har ta juyo ta ce da shi yai a hankali zafin albasan na damun ta.

"Yadda Albasan nan ta koma haka na ke maida duk wanda ya shiga gonata"

"What?" Ta faÉ—a a É—an tsorace amma bai kula ta ba sai ya ma fita daga kitchen É—in gaba É—aya.

Zaytoonah ta ce a ranta dole ta sake magana da Linda dan zuciyarta na riya ma ta akwai possibility ɗin Ben na da hannu a kisan Alinah kamar yadda ta ke iƙirari. Kuma abinda ya faru a ƙasar Finland shi ne sila.

Tana gama shirin fita sai ga kiran Zuhayr. Murmushi ne ya suɓuce ma ta. Ta rasa dalili amma tunda su ka dawo Zuhayr ya koma ba ta kulawa fiye da da. Like a rana idan baya gida zai kirata sau uku ko huɗu yana tambayar lafiyar ta. Idan kuwa yana gida baya bari ta zauna shiru, ko tana ɗaki tana karatu ko kallo haka zai zo ya ce ta sauko falo su yi tare.

"Ina zuwa?"

"Ballet dance"

"Oh! Na manta, ki dawo da wuri"

Ta amsa da to.

Mr Dawson ne sabon Driver É—in ta shine ya wuce da ita wajen da ta ke koyon rawan. Har yanzu dai ba ta wani iya komai ba dan ana kam improving flexibility É—inta ne.

Tana isa wajen Linda ta kirata akan ya kamata su haÉ—u cikin satin, Zaytoonah ta ce ba matsala za su iya haÉ—uwa ranan Asabat.

Awa biyu ta ke zuwa practice a sati sau uku. Abin mamaki lokacin da ta fito tana tunanin za ta ga motar da Mr Dawson ya kawo ta sai ta ga ɗaya daga cikin motocin Zuhayr. Ta ƙarisa wajen tana murmushi dan ba ta ɗauka zai zo ba, sun yi waya lokacin tana ciki kuma bai ce zai zo ba.
Shi da kan sa ya ke tuƙi dan haka gidan gaba ta shiga.

"Ya kuma ka zo da kan ka?"

"Ba kya so na zo É—aukan matata ne?"

Kalmar Matata da ya faÉ—i sai ya sa ta jin kunya.
Chapter 66 · 0% Book details