Sashe 118
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna haɗa ido da Zaytoonah ta yi miƙa tareda buɗe baki tana hamma.
"Kai Alhamdulillah! tunda jiki ya kwashi ni'ima daren jiya sai a je a kwanta a huta gajiya" ta yi maganar tana shafa ƙirjinta zuwa tumbinta.
Zaytoonah ba ta ce uffan ba ta dai wuce ta sauka ƙasa. Ruwan zafi ta ke son sha saboda mura da ya kamata ba ta son shan ruwan sanyi.
Sanda ta koma ɗaki zama ta yi akan gado ta buɗe Tab ɗin ta tana kallon instagram page na favourite interior designer ɗinta wato Kelly Wearstler matar ba ƙaramin burgeta ta ke ba kuma gaskiya ayyukan ta na da kyau. Sabbin hotunan da ta ɗaura ta ke dubawa tana ƙara yabon basirar matar.
"Assalamu Alaikum" ya faɗa haɗe da turo ƙofar ɗakin.
Chan ciki ta amsa sallamar tana jin wani haushi-haushin sa musamman da ta tuno kalaman Ghazala wai 'jiki ya kwashi ni'ima'
Yana zama a bakin gado ta gaishe shi ƙasa-ƙasa ba tareda ta ɗago ba.
"Da fatan mun tashi lafiya?"
"Lafiya mana, ko ka É—auka ba zan iya bacci ba ne saboda wata tsohuwar mata da ka ajiye a É—aki"
"Kina kishi na ne?" Ya faÉ—a yana murmushi.
"Allah ya kiyaye"
Ya ɗan jin zafin abinda ta ce amma ya dake ya ce " Tunda kin tashi lafiya Alhamdulillah. Ina dai ba kya buƙatar ƙomai?"
"Babu" ta faɗa da ɗan ƙarfi. Murmushi yai dan response ɗin ta ya nuna kishi ta ke ji. Dama aka ce kishi kumallon Mata.
Yana fita ta ja tsaki ta tashi da sauri ta je ta sawa ƙofarta key.
"Wai mun tashi lafiya? Mtsww a'a da zazzaɓi na tashi. Tsoho kawai"
"Munafuki, dama na san duk wannan shiru-shirun na munafurci ne. Idan ka ga dama ka cikata mata huÉ—u ma ni ba damuwa na bane"
Haka ta dinga ɓaɓatu ita kaɗai tanayi tana jan tsaki.
Ranan da Zaytoonah ta karɓi kwana Justice yai dakon jiranta a ɗakin sa. Ta shigo da yamma ta wanke ma sa banɗaki ta daɗa gyara ma sa ɗaki ta fesa turare wanda hakan ya sa shi jin wani sanyi a ran sa a tunanin sa ta shirya ma sa ne. Sai dai bayan sun gama cin abincin dare da ta wuce ɗakin ta bai sake jin motsinta ba. Kusan ƙarfe goma ya kira wayarta amma ya ji ta a kashe. Goma da rabi ya fito ya nufi ɗakin ta amma yana tura ƙofar ya ji ta a rufe. Bai gwada ƙwanƙwasawa ba juya ya tafi dan ya san da gangan rufe ƙofarta da key.
Ya riga ya sawa ran sa akan ba zai takura ma ta ba zai jira ya ga iya gudun ruwanta. Idan haƙurin sa ya ƙare kuma ƙila lallaɓarta zai koma yi dan ya ga alama matar ta sa 'yar lallama ce, kafin a kai ga haka ma ya san za ta gane kuskurenta.
Baya ɗaya daga cikin mazajen da ke takurawa matan su a ɓangaren kwanciya. Bai yarda da tursasawa ba, indai ba ka so zai ɗaga miki ƙafa, duk abinda ba ka amince ba aka maka ta ƙarfi tauye hakki ne wannan.
***
Ko sati ba a yi ba Ghazala ta fahimce abinda ke faruwa tsakanin Justice da Zaytoonah. Wannan ya sa ta zage damtse wajen tattalin Mijin ta a duk lokacin da ya ke ɗakin ta. Tun lokacin da Justice ya bada sadakin ta zuwa yanzu da ta shigo gidan. Kayan mata na gyara da ta siya aƙalla ba a ƙasaru ba ta kashe ya kai dubu ɗari shida da hamsin. Ta ƙarɓa a hannun mutan Sokoto, Maiduguri da ma wajen mutanen Niger.
Indai kuwa babu wannan kusancin tsakanin su ashe dai yin waje da Zaytoonah ba zai ma ta wahala ba...
Tana cikin jera abinci a dinning Justice ya shigo gidan.
"Ki sameni a É—aki" ya faÉ—a kafin ya haura sama.
Batareda ta É—auko sauran ba ta bi bayan shi da sauri. Da ke Jummu'ah ne manyan kaya ya fita da shi office. Lokacin da ta shigo ya ajiye babban rigan gefe tareda hula.
"Sannu da zuwa" ta faÉ—a lokacin da ta zauna.
"Ya gidan?"
"Lafiya"
Kamar yadda ta lura al'adar sa ce fara yin shiru kafin yai magana mai muhimmanci yanzun ma shirun yai.
Wai dama haka ma su sarauta su ke da jan aji ne ko dai shi É—in ne mai ra'ayi irin wannan?
Ta ɗan gyara zamanta a karo na kusan huɗu ba tareda ya ce komai ba. Chan da ya gama shirun sai ya ce " akwai manyan baƙi da zan yi gobe, daga Sokoto su ke amma yau za su kwana a Kano sai gobe za su iso nan. Su biyar na ke tsammanin za su zo sai dai idan uzuri ya sa sun ƙaru ko sun ragu."
"Allah ya kawo su lafiya"
"Akwai kaya da na sa a shigo da shi ki je ki duba ko akwai abunda babu sai a siyo"
"Ok"
Har ta tashi ta ji ya ce "Adaeze"
Ta juyo ta kalle shi.
"Za su iya isowa Insha Allah tsakanin ƙarfe shabiyu zuwa biyu na rana haka. Dan Allah a tanadi abinci da wuri"
"Insha Allahu" ta faÉ—a tareda barin falon.
Lokacin da ta koma kitchen ɗin ta ga kaya jibge a tsakiyar kitchen da alama Dreba ne ya shigo da shi. Normally dama Atika ko Maman Tope ne za su karɓa su kai store na ajiyewa cikin kitchen ɗin kuma su Ajiye. Sai dai babu Atika a wajen. Da ke ita ke da girki tun huɗu Atika ta gama yiwa ma su aiki abinci ta fita bayan gidan wajen Bahijje.
Ghazala dama tun da safe ta fita, ko ina ta je ma dai ba ta dawo ba har yanzu.
Dama tunda ta lura Atika ta hannun daman Ghazala ce ba ta cika sakata aiki ba sai dai idan ya zama dole, da Maman Tope kawai ta ke shiri.
Ta shiga buÉ—e kayan tana wawware su sai kuwa ta ci karo da buhu yana É—an malala jini. Ta buÉ—e buhun ta ga naman rago ne a ciki an riga an yanyanka. Su hanjin cikin ma an masa wanki mai kyau.
"Ya Ilaahi! Ta ina zan fara aikin naman na? "
Ta jawo kujera ta zauna tukunna tana tunanin ya za ta yi, da kuma ma irin girkin da za ta yi wa baƙin gobe.
Ta sauke ajiyar zuciya bayan ta ga agogo ƙarfe biyar da minti arba'in da shida.
Doguwar riga ne a jikinta dan haka taga gara ta chanja shi dan wannan aikin yana buƙatan shiri mai kyau. Komawa ɗaki ta yi ta cire rigan ta saka baƙar T-shirt da baƙin jeans ta saka hula ta fito.
Naman ta fara kasabtawa, wanda ba za ta yi amfani da shi ba ta saka a deep freezer. Sauran kuma ta shiga gyarawa...
Dai-dai sallan Magariba Ghazala ta shigo gidan. Jin ƙanshin ya gauraya falon ya sa ta wuce direct kitchen dan a tunanin ta Zaytoonah ne ba ta gama girki ba sai kuma ta ga an shirya abinci a dinning table.
"Yau take sallah ne, irin wannan ƙaton tukunya haka"
Zaytoonah ba ta kula ta ba ta cigaba da kwashe naman da ta silala. ÆŠakin Atika ta wuce ta ga ba ta nan dan haka ta kira numbarta.
Jiki na mazari Atika ta shigo É—akin Ghazala.
"Ina kuma ki ka je ana abu agidan nan ba ki sani ba"
"Ran ki shi daɗe wallahi Bahijje ce ta riƙe ni da taɗi"
"TaÉ—i ko dai gulma"
Atika ta yi 'yar dariya.
"Mi za ayi ne na ga Yarinyar nan na sarrafa nama dayawa haka"
"Gaskiya Hajiya ban sani ba, dan tunda na gama girki na fita"
"Ba na son yawon banza baya cikin aikin ki a gidan nan"
"Allah ya huci zuciyar ki tauraruwar Galadima"
"HaÉ—a min ruwan zafi zan yi wanka"
"Angama Hajjaju" Atika ta faÉ—a tareda shigewa banÉ—akin Ghazalar...
"Akwai abinda zan taya ki da shi ne?" Atika ta tambaya tana wani yatsina fiska.
"Ki je kawai na ma kusa gamawa"
"Na ga kamar aikin dayawa"
"Ki je kawai"
Ko kaɗan ba ta yarda da ita ba balle ta sata aiki. Ranan ta ɗaura miya ta fita da ta dawo ta ga Atikar ta buɗe ma ta tukunya, wai sai ta ce tana dubawa ne dan kar ya ƙone. Ta dai yi shiru ne kawai dan kar ace ta fara.
Lokacin da ta zo za ta serving É—in su abinci duk wani motsinta Justice na binta da kallo. T-shirt É—in da ta sa ya kamata sosai, kirjinta ya ciko fam. Ga wandon ma ya fito da shape É—in ta sosai, hips da cinyoyinta sun fito Masha Allah.
Bayan ta gama ta goma kitchen ta cigaba da aiki. (Kai a gaida matan gida fa da ƙoƙari, irin aikin emergency ɗin nan akwai cin rai. Barin ma kai ɗaya ne kuma ba ka da mai aiki da za ta taimaka, ko mai aikin irin Atika ce ka ƙwammaci ka yi aikin ka da kan ka).
Samosa sheet ta yanka kusan wanda zai kai 50 ko ma fiye. Ta riga ta haɗa fillings ɗin ta ajiye a fridge akan gobe kawai sai dai ta dinga naɗewa tana soyawa. Tana gama wannan ta shiga kwaɓa key lime cake irin wanda ta yi ranan ta ga da Justice da yaran duk sun ji daɗin sa. Falaq da ke da ƙaurin baki ma sai da ta ce "i love this cake" Raziya uwar gayyar ba ta yaba ba amma sauran wanda ya rage washegari ita ta bi shi ta cinye.
Lokacin da ta gama komai kanta kamar zai rabe biyu saboda ciwo. Tana shiga ɗaki ta ga ƙarfe shabiyu da minti biyu. Ko kaya ba ta cire ba balle ta yi wanka.
Alarm ɗin ta na ƙarfe huɗu da ya tasheta ta kashe za ta koma bacci sai kawai ta tuno ai ba ta yi sallar Isha ba jiya. Da sauri ta miƙe ta shiga banɗaki...