Sashe 102
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Azumi ne ke cinta saboda aikin wahala da su ka yi kwana biyun nan. Su Chief Asibong ne su ka kawo mu su Ziyara dan su kai godiya wa mutanen da su ka taimakawa 'yar su. A Zaria su ka fara sauka inda su ka yi kwana biyu. Mommy ta mu su jagora wajen Iya, ko ba komai ita ce uwa ga mutumin da ya chanja ma ta rayuwa.
Kunya taf a idon Iya lokacin da Auwal ke fassara ma ta maganganun Chief Asibong wanda godiya ne na irin tarba da su ka yiwa Mommy. A zahiri Goggo ce ta cancanci wannan godiya dan ita ce uwar Mommy. Ita ce ta riƙe ta tamkar 'yar da ta haifa, sai gashi yau babu Goggo a tareda su ita Maryam ke karramawa haka. Duk da kasancewar su Christians hakan bai hanata ganin girma da darajar su ba. Da ganin ido ta san 'yan uwan Maryam manyan mutane ne. Da za su tafi Uncle ɗin Maryam ya ajiyewa Iya wani envelope akan centre table suna faɗin 'yar ƙaramar kyauta ce ta nuna godiya. Bayan tafiyar su Humairah ta ɗau envelop ɗin ta buɗe shi sai ga check ɗin kuɗi million ɗaya. Humairah ta challa ihu tana tsalle.
"Humairah minene? Takardar miye su ka bamu?"
"Iya check É—in kuÉ—i ne, check É—in million É—aya. One million naira Iya" ta faÉ—a tana nuna ma ta check É—in kamar Iyan ta za ta gane abinda aka rubuta.
Gidan surukan Zaytoonah su ka wuce inda nan ma Alhaji Iliyasu ya tarbe su da kyau. Da taɗi yai taɗi ne ma Chief Asibong ya tuna cewa sun taɓa haɗuwa da Alhaji Iliyasu a Newyork kan wani taron kasuwanci na ƙasa da ƙasa da su ka halarta kusan shekaru hamsin da uku da su ka wuce.
Cikin ƙanƙanin lokaci Chief Asibong da Alhaji Iliyasu su ka samu wani bond na musamman, aka zauna ana tuna baya. Rayuwar ƙuruciya da su ka yi da kuma yadda zamani ke tafiya yanzu.
Chief Asibong bai bar wajen Alhaji ba sai wajen ƙarfe takwas na dare inda driver ya maida shi hotel ɗin da su ka sauka.
Washegari kuma su ka wuce Ringim. Nan ma 'yan uwan T J sun sha kyaututtuka daga wajen Kakan Mommy wanda ya ke ƙara godiya da irin mutanen da Allah ya haɗa jikar sa da su.
Yadda ake ta maganar kyawawan halayen T J ya sa Mommy ta fara hawaye.
Ina ma ace T J yana nan tare da su ya ga wannan rana. All this credit da ake ta bawa 'yan uwansa shine ya fi chanchanta da hakan. T J silar zuwanta Ringim. T J shine silar duk wani abinda ta zama yau.
Ganin kuka na shirin kubce ma ta ga sa Mommy ta tashi daga falon da ake taron. Ba ta tsaya ko ina ba sai ɗakin Goggo wanda ya zama ɗakin da ake saukan baƙi. Ta zauna a ƙuryan ɗakin tana tuna shekarun baya da ta ke rayuwa a wannan ɗakin. Kyawawan halayen Goggo, company da ta ke samu a wajen Pendo ga uwa uba soyayya da kulawar T J.
Kamar yau ne T J ya damƙa ta a hannun Goggo, kamar yau ne ta fara sallah a ɗakin nan bayan ta karɓi kalmar shahada. Kamar yau ne ta yi wankan jego a wajen Goggo.
"Rayuwa kenan" ta furta a fili tana kallon screen É—in wayarta wanda hoton T J ne akai yana murmushi kamar yadda koyaushe fiskar sa ke cike da fara'a.
Looking back to all those years she badly wish T J na tare da ita. Ya ga 'yan uwan mahaifiyar ta da su ka zo ya kuma ga yadda 'yar su ta defeating Chief Udodiri a kotu.
Ta sunbaci hoton sannan ta rungume wayan jikinta tana hawaye...
Wannan ziyaran har Fadar Ringim sai da su ka je domin ba da labarin Mommy da 'yarta ba tareda an sako Sarkin Ringim ba to kamar an manta wani babban shashe ne mai mahimmanci na labarin.
Kowa sai mamaki ya ke ashe dai 'yan uwan Maryam ma su Arziƙi ne da gaske. Hajjo da ta zo gaisuwa Mommy ta nuna ta a matsayin 'yar uwarta wanda su ka zauna tare ƙarƙashin miji ɗaya sai da ta yi kuka. Tun rabuwan su har yau Mommy ba ta fasa yiwa Hajjo alkhairi ba duk lokacin da ta zo Ringim.
Cash É—in dubu É—ari aka ba ta a envelop da za ta tafi. Mommy har mamakin yawan kyaututtukan da Kakan na ta ke ta bayarwa ta ke, dan ba ta tsammanci zai martaba 'yan uwan mijinta haka ba.
Ba su kwana a Ringim ba a ranan su ka wuce Zaria inda su ka ƙara kwana biyu kafin su ka wuce Abuja inda daga nan su ka shiga jirgi su ka koma Owerri akan su da zuwa kuma sai bayan sallah lokacin bikin Zaytoonah.
"Zaytoonah kashe waya ki ka yi ne? Ummin ki ta ce ta kira numbar ki bai shiga ba"
"Ina ga network ne amma wayar a kunne ta ke"
"To ki kirata"
Mommy ta yi maganar tana shigewa ciki dan daga makaranta ta ke.
Wayar ma wahala zai ma ta shiyasa ta gyara kwanciyarta akan kujera. Kwanciyar ɗaki ne ya isheta ya sa ta fito. Duk yadda ta ke jin jiki ma wai ashe sai yanzu ƙarfe uku ta yi.
Ta É—auke idon ta daga kan agogon ta koma kallon ceiling.
Har ta É—an fara bacci kiran Ummi (Pendo) ya tashe ta.
Tana ɗaukan wayar Ummi ta fara yi ma ta faɗa kan ƙin zuwa da ta yi ta ma ta gyara.
"Anya Zaytoonah kina amfani da abinda na aiko miki da shi kuwa?"
"Ina yi" ta faÉ—a dan kawai ta rufe maganar.
"Kin san Allah idan na zo na samu ba ki yi amfani da shi ba zan saɓa miki"
"Ummi ina yi fa"
"Wannan na ganyen dalbejiya É—in shima kina yi"
Zaytoonah ta yi shiru. Ita fa tunda Salman ya karɓo ma ta saƙon Pendon daga park da ta buɗe taga haɗe-haɗen gyara ne da bayanan su da aka rubuta a littafi ta tattara su ta ajiye gefe, ba abinda ta yi amfani da shi.
"Zan saɓa miki Zaytoonah. Ke ba yarinya ba ce, auren ki ya zo a ƙurarren lokaci amma ba kya so ki gyara jikin ki"
"Ummi da Azumi zan ji ko da gyaran jiki..."
"Za ki sha mamaki idan na shigo Zaria"...
Wasa-wasa sai ga shi har ana gobe ko jibi sallah. A ɓangaren Mommy a karo na biyu tana shirye shiryen bikin 'yar tata amma ita Amarya Zaytoonah ba abinda ta ke yi. Ita ba wanda ta faɗawa ma za ta yi aure balle wani shirye- shirye.
A Ringim za a É—aura auren inda daga nan za a kawo ta Fadar Zazzau kafin ta wuce gidan mijin ta da ke Abuja.
Auren na matsowa tana ƙara jin fargaba gameda auren.
Ranan da dare sai ga Justice a gidan su. Shima ya shigo Zaria. A madaidaicin falon su aka sauke shi inda yaran su ka yanyameshi suna murna da ganin sa. Tunda Zaytoonah ta ajiye ma sa ruwa ta shiga É—aki ta yi kwanciyar ta. Ganin sa da ta yi ya sa ta ji jikin ta yayi sanyi.
Shima Justice bai neme ta ba dan dama yaran ya zo dubawa tareda kawo mu su kayan sallah da ya mu su, sannan ya nemi alfarmar zai tafi da su Idi kuma idan ba matsala zai fita da su hawan da za ayi.
Zaytoonah na kwance yaran su ka shigo da gudu suna ihu wai Daddy ya ce za su hau doki. Kora su ta yi dan ihun na su ya isheta.
Bayan fitan su ne ta ga saƙon Justice a wayar ta inda ya tambayeta ko tana buƙatar wani abu. Ta tura ma sa reply da cewa a'a...
***
Kusan wannan sallar ta zo wa 'yan biyu a yanayi na farinciki fiye da kowacce Sallah. Tun da sassafe driver ya zo ya ɗauke su bayan sun sha kayan da Justice ya kawo mu su. Tun a jiyan su ka dinga waƙar cewa kayan da Daddy ya kawo za su sa ba kayan da Mom ta mu su ba.
Dukkan su uku irin kayan Justice ne a jikin su bayan an kai su gidan sa su ka ga shima irin sa ne a jikin sa. Maimakon da da su ke bin Alhaji Tsoho zuwa masallacin idi wannan karan Daddyn su za su bi.
Tuni an reserving mu su doki da kuma wanda zai riƙe mu su dokin saboda suna cikin tawagar Galadima idan za ayi hawan sallah.
Zaytoonah tun tana sa idon za a dawo da 'yan biyu da Junior har ta haƙura ta zuba ido kawai. Daga baya Justice ya tura ma ta saƙo akan za su kwana a gidan sa.
Ta taɓe baki tana mamakin wannan fin ƙarfi. Tun kafin ma ya aureta ya fara nuna iko akan yaran ta...
Tun bayan sallah Mommy ta sa wa Zaytoonah ido gameda gyaran jiki da ta ƙi yi. Dole da ta yarda ta fara amfani da wasu abubuwan da Ummi ta aiko ma ta da shi. Ana saura kwana biyar ɗaurin auren Ummi ta zo Zaria. Inda ta cigaba da gyara Zaytoonah da kayan gargajiya ma su inganci musamman wankan Lalle.
Zaytoonah dai na ta ido, dan da ta yi magana ma Ummi za ta fara masifa ganin yadda Zaytoonan ta yi sakachi da amfani da abubuwan da ta aiko ma ta tun farko.
Magana kaÉ—an sai ta fara " ke fa Matar É—an Sarki be, gidan sarauta za ki shiga dan haka dole ki je ki kece reni"
Ranan Asabat da misalin ƙarfe shaɗaya da minti huɗu aka ɗaura auren Justice Yunus Muhammad Abbas da kuma Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar.
Auren da ya samu halartar ɗaruruwan mutane daga wajaje daban-daban. Galadima mutum ne mai Jama'a shiyasa kowa ya ke farinciki da wannan aure. Ana gama ɗaurin aure aka wuce Zaria inda aka gabatar da reception a wani babban hotel. Da ƙarfe huɗu na yamma kuma aka fara yin hawa don taya mai girma Galadiman gari murna.
Gaba É—aya gari ya cika da jama'a kamar wani hawan Sallah ake yi...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 49
Bismillahir Rahmanir Rahim
*The winning*