← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 161

Sashe 43

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Good evening Sir" ta gaishe shi tana murmushi.
Ya juyo ya amsa ma ta tareda tambayarta ita ce amaryar Oga? Ta ce ma sa eh. Akwai kitchen dining a wajen mai ɗauke da kujera huɗu dan haka ta zauna Chef Green ya serving ɗin ta ta hau cin abinci. Grilled chicken ne sai spaghetti da kuma salad a gefe, sai orange juice da ya haɗa. Yadda kazar ke tiriri saboda a lokacin aka fito da ita daga oven ya sa yawun Zaytoonah ya tsinke. Chef Green ya yanka ma ta chinya ɗaya da haƙarƙari ya ajiye ma ta a plate. Zaytoonah ta ce ai za ta iya cinye kazar duka. Chef Green ya zaro ido dan kazar Babba ce.
Ta zauna tana ci tana ma sa tambayoyi gameda gidan har ta cinye rabin kaza ta ji ta ƙoshi. Duk da haka sai da Chef Green yai mamakin ta...

Pyjamas ta saka riga da wando ta kwanta bayan ta yi sallar Isha sai bacci.

Hasken rana da ya fara ratsa ɗakin ne ya farkar da ita daga bacci. Ta tashi ta shiga banɗaki ta yi brush sannan ta yi Alwala ta zo ta yi sallar Asuba tana cikin azkar ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa dan haka ta miƙe da sauri dan ta ɗauka Zuhayr ne. Tana buɗe ƙofa ta ga Ben ne.

"Ki shirya ki fito za a kaiki makaranta"

"Ina Zuhayr?"

Yai shiru yana kallonta. Ta sake cewa "ba inda zan je sai na ga Zuhayr. Ni ban yadda da kai ba"

Juyawa yai ya tafi ba tareda ya ce komai ba...

Haka ranan ta wuni ba ta sake ganin kowa ba. Girkin rana da aka yi tana tsaye tana ganin yadda Chef É—in kai komai, yana yi yana ma ta bayanin abubuwan da ya ke amfani da shi.
Abu É—aya ta gane kuma ta tabbatar a wajen Chef Green É—in. Wato kafin zuwanta gidan mutum biyu ke kwana a katafaren gidan nan. Zuhayr da Ben. Shi Chef green ba kwana ya ke yi ba, zuwa ya ke da safe ya tafi da dare. Akwai wata mai aiki Mercy da itama ke zuwa duk safiya tana gyara gidan sai ta tafi.

A inda ta yi sallar Maghrib bacci ya fara ɗaukanta. Sai dai ƙaran saukan Helicopter ya tada ta. Ta yi saurin fitowa daga ɗakin bayan ta leƙa ta window ta ga Zuhayr ya fito daga cikin helicopter ɗin.

Tana tsaye a falon har su ka shigo shi da Ben.
Kallon sa ta ke yi tana jin bugun ƙirjinta na ƙaruwa.
Hannu ya miƙa ma ta yana faɗin "Zaytoon right"
Hannun ta kalla sannan ta kalli fiskar sa ta ce "Yes" ba tareda ta yi musabaha da hannun sa ba.

Maida hannun sa yai cikin Aljihu ya ce "welcome to Las Vegas" yana faÉ—in haka ya haura sama tareda Ben.
Bayan ya tafi tukunna ta yi sauke numfashi tana dafe ƙirjinta. "Ya Allah wannan mutum haka" sai kuma ta ɗan mari fiskarta tace "ji yadda kika basar da shi yana miƙa miki hannu kin ƙi kama hannun. Stupid Zaytoonah"

Komawa ta yi É—akinta tana karanto yanayin fiskarsa da muryarsa a ranta.

Ba su sake haÉ—uwa ba sai washegari da ta fito yin breakfast saboda yunwa ne ya tasheta.

A dinning ta ke ci dan Chef Green ya riga ya jera komai a wajen. Shi da Ben su ka sauko dukkan su sanye da baƙaƙen suit. Ben na riƙe da wani briefcase shi kuma Zuhayr wani ƙaramin paperbag ya riƙe.
Ta cika bakinta da abinci amma ganin sa ya sa ta yi saurin É—aukan coffee ta kai baki dan ya kora abincin.

"Good morning Zaytoon"

Ta amsa ma sa da morning.

Paperbag ɗin ya ajiye a gabanta ya ce waya ne aciki, akwai layi akwai komai za ta iya saka layin ta kira 'yan gidan su. Ya ce akwa numbar sa da ta Ben a ciki idan tana buƙatar wani abu za ta iya kiran ɗaya daga cikin su.

"Ben" ya faɗa yana juyawa gareshi, shi kuma ya miƙa ma sa wani kati kaman na ATM ya amsa ya miƙawa Zaytoonah.

"Ga credit card nan da za ki dinga amfani da shi wajen duk buƙatun ki, ko na makaranta ko na karan kan ki. Kin iya mota?"

Ta girgiza kai

" akwai Driver da zai kai ki makaranta da duk inda ki ke so. Idan kin fita waje ki tambayi Mr Smith shine driver"

Ya ƙara kallon Ben ya ce " what else?"
Ben ya miƙa ma sa wani file ya karɓa shima ya ajiye ma ta ya ce "document ɗin ki ne na makaranta"
Ta ce ta gode.
Har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya ce " fatan ba ki manta da deal É—in mu ba?"

Ta gyaÉ—a ma sa kai ya ce "good, have a nice day Zaytoon"

Bayan ya tafi ne maganganunsa a waya su ka dawo ma ta daren wata Asabat da ya kirata.

*ba ni da ra'ayin aure, ba ni da ra'ayin haɗa rayuwa da mace, amma tunda GrandPa ya riga ya haɗa komai zan baki option biyu. Na farko zan sponsoring karatun ki har ki gama, bayan nan sai na sake ki. Za mu rayu kamar 'yan uwa ba kamar mata da miji ba. Ko kuma another option, zan sake ki yanzu. Ba wanda zai sani sai mu biyu, za ki zo nan Vegas kiyi karatunki hankali kwance, idan kin gama sai ki koma gida. Wanne kika zaɓa?*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*17-Missing*

Bismillahir Rahmanir Rahim

T J bai tashi ba sai chan yammaci. An hana mutane shiga wajen sa saboda ba a son abun da zai tada ma sa hankali. Auwal ne kaÉ—ai ya shiga É—akin ya duba shi.
Yana ganin sa yai murmushi mai ciwo yayinda maganganun Maryam ke sake ma sa yawo a ƙwaƙwalwarsa. Ba abinda ya tsaya ma sa irin furucin da ta yi na danasanin haɗuwa da shi da ta yi har ta fara son shi.

"Daddy ya jikin?" Ya tambaya yana danne hawayen da ke shirin zubowa.

"Mommyn ku tana nan?" Ya faÉ—a a hankali

Auwal ya girgiza kai, sai ga hawaye ya silalo daga idanun TJ.

"Muna tareda ita tuntuni, ta je gida É—auko kaya ne" yai saurin faÉ—a saboda hawayen da ya gani a fiskar TJ. Maryam kam da su ka dame ta da kira ma kashe wayar ta yi.

Ya san ƙarya ya ke yi Maryam ba ta nan, da tana nan ba abinda zai sa ta koma gida ba tareda ya farfaɗo ba.

Kenan da gaske ta tsaneshi, ta tsani zama da shi. Abinda ya faÉ—o ma sa rai kenan.

"Dan Allah ka ce Mommyn ku ta zo ina son ganin ta"

Auwal ya rasa ya zai faÉ—a ma sa abinda ke faruwa yana tsoron kar hankalinsa ya kuma tashi. Anje gida ba ta nan, office É—in ta ma a kulle ya ke ba chan ta je ba.

Ya dai fita dan kaɗan ya rage yai kuka. Yana fitowa Iya ce ta fara tambayar sa ya jikin sa ya ce ma ta da sauƙi. Itama ɗin da ita aka yi zaman jira ta ƙi komawa gida ita yadda aka kawoshi da safe ma ta ɗauka ba zai yi rai ba.

Har dare ba Maryam ba dalilin ta. Auwal kam sai cewa T J yai ciwon Sadiq ne ya tashi Maryam ɗin ke tareda shi a Asibiti saboda ana buƙatar jini. Ya dai ji ne amma ya san ƙarya ne.

"Ta tafi ko?" Auwal yai saurin girgiza kai yana faÉ—in " Allah Daddy tana wajen Sadiq ne, zuwa gobe da safe za ta zo tunda Likita ya ce mutum É—aya ne zai zo wajen ka"...

Maryam hotel ta wuce ta kama ɗaki ta shiga ta durƙusa ƙasa tana kuka. Tun kafin ta iso hotel ɗin ake kiranta lokacin da ta karanta text ɗin da Auwal ya tura har ta karya kwana za ta je Asibitin sai ta fasa.

"Akwai mahaifiyar sa akwai matar sa tareda shi za su ba shi kulawan da ya dace" abinda zuciyarta ya raya ma ta kenan ya sa ta fasa zuwa Asibitin.

Sai da ta sha kukan ta sannan ta je ta yo Alwala ta yi sallah ta zauna tana yiwa T J addu'ar Allah ya bashi lafiya.
Ba za ta taɓa yafewa kan ta ba idan wani abu ya sameshi. So mugun abu ne, duk yadda ta ke kurin rabuwa da T J soyayyar sa na maƙale a ran ta kuma tana jin idan ta rabu da T J tamkar ta rasa farinciki a rayuwar ta ne. Ba ta da identity idan aka cire T J a rayuwar ta.
Tana son zuwa ta duba shi amma ba ta san da wani ido za ta kalle shi ba after abubuwan da ta faÉ—a ma sa. Ga uwa uba ba ta son haÉ—uwa da Iya.

Chan bayan Maghrib da ta ka sa haƙuri ta kunna wayar ta ta kira numban T J ta sani wayar ba zai wuce yana hannun Auwal ba. Shi ɗin ne ya amsa wayan lokacin ma ya fito daga masallaci kenan zai koma cikin Asibiti.

Tambayar sa ta yi jikin T J ya ce ma ta da sauƙi.

"Mommy ina kika shiga? Daddy yana son ganin ki, yana buƙatar ki kusa da shi" Auwal ya faɗa kaman zai yi kuka.

"Ka kula da shi sosai Dan Allah. Idan yana buƙatar matar sa ka kira ma sa Hajjo" daga haka ta katse kiran ta kashe wayan gaba ɗaya.

Ta riga ta yi waya da Maman Fawaz akan su Zaytoonah za su kwana a wajen ta dan ta yi tafiya dan haka ba ta da matsala da yaran.

Ba ta iya bacci ba saboda damuwa da ya isheta, tun 1am ta tashi ta fara sallah tana roƙawa T J lafiya. Zuwa ƙarfe 3 kuma ta ɗauko ƙur'ani ta fara tilawa. Da safe ko abinci ba ta ci ba ta wuce office zuwa lokacin ta fara jin sanyi a zuciyar ta gameda abinda ya faru.
Chapter 43 · 0% Book details