← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 161

Sashe 36

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganar Daddy da ta yi ya sa Maryam ta tuna lokacin da ya zo ƙarshen shekaran da ya gabata ya zo ya mu su kwana ishirin da huɗu kafin ya koma. Yadda ta yi kewarsa kwanakin nan sun tafi ne da gudu sai da ya tafi taga kamar ma kwana biyu kawai yai. Ba ta dameshi da matsalolin gida ba kar ya tafi da tashin hankali. Sau ɗaya da ya zo da Muntari gidan ne ta taka ma sa birki ta ce indai yana son zaman lafiya kar ya sake shigo ma ta da Muntari gidan. Ya tambayi dalili ta ce ma sa ba ta so ne kawai, ganin da ya matsa ma ta da tambayoyi ya sa ta tashi ta bar ma sa ɗakin hakan ya sa ya bar zancen ya wuce shima baya son abin da zai jawo mu su matsala a iya kwanakin da zai yi da su.

Tun ranan da abun nan ya faru ta ke ganin Muntari a matsayin wanda ya ke da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa. Har yau idan ya bushi iska yana aiko ma ta da flowers office da card mai ɗauke da kalaman soyayya. Ranan da ya fara aikowa sati biyu bayan ɓarin da ta yi har da check ɗin kuɗi tareda makullin mota ya rubuta saƙo kamar haka *My love ki yafe min Dan Allah. Ga wannan kyauta daga gareni kuma kaɗan ne daga irin abubuwan da na tanadar miki idan ki ka amince da soyayyata. I love you Maryam*

Bayan ta gama karantawa ta rasa ma mi za ta ce da Muntari dan gaskiya ya tabbata Mahaukaci ne. Kuɗin da ya rubuta a check ɗin kuwa sun girgizata saboda yawan su. Zuwa ta yi ta photocopy ɗin check ɗin da wasiƙar saboda a matsayinta na Barrister dole ta ajiye shi shaida.
Flower da original check ɗin da key ɗin mota kuwa gidan Hajjo ta je ta watsawa Iya a jiki ta ce idan Mahaukacin ɗan ta ya dawo ta bashi saƙon sa.
Ko Iya ta ma sa magana ne? sai bai ƙara turowa ba sai da ya ja lokaci sannan ya dawo da tsiyar sa amma wannan karan bai haɗo da kuɗi ko key ɗin mota ba zallar card ne da Flower. Haka za ta photocopy card ɗin ta ajiye idan ta koma gida ta sa a leda ta bawa Auwal ta ce ya miƙawa Mai gadin gidan Uncle ɗin shi ya bawa Muntari.

Idan aka yi albashi akwai yadda T J ya tsara yadda za su dinga yi da shi. To tana É—aukan kasonta za ta kaiwa Hajjo na ta. Just of recent ne wani zuwa da ta yi kaiwa Hajjo kuÉ—i, a wajen Hajjon ta ke jin wai su na shirye-shiryen bikin Muntari, Iya ta sama mi shi mata a Ringim...

Washegari Zaytoonah ta ce ba za ta je school ba. Da Maryam ta zare ma ta ido sai ta ce ai 'yan ajin sun tsaneta dariya su ke ma ta su dinga kiranta Fat girl ko Fatty Bombom.
Maryam ta nitsu tana jin maganganun 'yar na ta. Bayan ta gama ƙorafin Maryam ta ba ta haƙuri tareda cewa haushi su ke ji saboda ta fi su ƙoƙari a ajin, tunda Exam ɗin su na first term ita ta yi na ɗaya. Da ƙyar dai ta shawo kan ta har ta yarda ta shirya aka wuce da ita makaranta...

*Hmmmmm. Alhaji Muntari da gaske ba ƙalau ka ke ba*

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*
Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*14-Anger*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Shekara biyu da wata huɗu da dawowan Muntari Zaria wanda yanzu ya ke matsayin Alhaji Muntari Abubakar Modibbo Djibo yai aure. Aure ne da ba wai dan Iya na so ya yi shi ba, Iya ba ta isa ta tursasa shi yin abu ba. Ya yi ne domin ya nunawa Maryam cewa yayi hankali ko na ce ya nitsu, da kan sa ya je office ɗin ta ya kai ma ta invitation ɗin auren tareda sake ba ta haƙuri bisa abinda ya faru tsakanin su. So ya ke ta yarda da shi su koma mutunci kamar da har ya samu ta amince da soyayyar sa cikin sauƙi.

"Sorry Muntari ba zan iya zuwa ko É—aya cikin hidiman bikin ka ba. And kamar yadda na faÉ—a a baya ka fita a harkana, ba zan shiga huruminka ba kai ma kar ka shiga nawa. Idan ka yi haka za a zauna lafiya idan ba haka ba kuwa zan ajiye duk wani kunya a gefe na yi shari'a da kai"

"Maryam kenan. Na ji amma dan Allah ki sassauta min, ki rage takurawan da ki ke yiwa su Zaytoonah. Ko ba komai ni fa Baban su ne"

Wannan karan ido cikin ido ta kalleshi ta ce "Muntari Oh Alhaji Muntari. Bayan Zaytoonah da Salman akwai Humairah da Sadiq. Ba ni da hurumi da sauran amma wanda na haifa da kaina ba zan taɓa bari su yi tarayya da mutum kamar ka ba. Stay away from my kids"

"Ba zan gajiya da baki haƙuri ba Maryam har sai kin haƙura. Ki yi haƙuri dan Allah"

Daga haka ya ajiye ma ta katin bikin ya fita daga office É—in. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya...

Biki aka yi tun daga Ringim aka zo Zaria aka ƙarisa, ba inda Maryam ta je ita da 'ya'yanta. Su Iya da Hajjo su ne ƙirjin biki musamman ma saboda ɗan Yayan Iyan zai aura. Su ka ƙare tsiyar su aka kawo Amarya gidan Muntari.

A ɓangaren Ango kuwa ba wani murna ya ke yi da bikin da zai yi ba. Aure ne da ya ke da ƙaddararren lokaci a wajen sa, da ya samu kan Maryam zai tura ta gaba.

Bayan kowa ya watse aka bar Amarya ita ɗaya. Muntari bai shigo gida ba sai wajen ƙarfe shaɗaya da rabi na dare, kai tsaye ɗakin Amarya ya wuce.

Tana nan dai zaune kan gado ta yi lulluɓi, da Misalin ƙarfen goma 'yan biki su ka watse za su je su kwana a gidan Hajjo.

"Hannatu" Muntari ya kira sunan ta da ƙarfi.

Ba ta amsa ba sai ma mutsu-mutsu da ta fara ta cikin gyalen.

"Ko ki É—aga gyalen nan ko na zo na rufe ki da duka. An gaya mi ki ban san ko ke wacece ba ne, na sani ragowan Salisu aka kawo min"

Nan da nan ta É—age gyalen tana kallonsa jikin ta na rawa saboda ba ta É—auka ya san wannan sirrin ba.

"Ki buɗe kunnen ki da kyau. Na zaɓe ki ne a maimakon Rabi'atu saboda ita nitsatstsiya ce ke kuma watsatstsiya ce"

"Dan Allah ka yi haƙuri Hamma Muntari" ta faɗa tana fashewa da kuka.

Ya daka ma ta tsawa nan da nan ta haÉ—iye kukan.

"Mace ɗaya na ke so kuma ita kaɗai ce zan aura mu yi rayuwar soyayya. Kasancewa kin riga kin sayarda mutunci a wani kinga babu wani mutunci na ki da zan gani. Ki zauna a matsayin Matata ki bi dokoki na, duk lokacin da na buƙaci mace saboda rage zafi zan neme ki, bayan wannan ba na son shishshigi. Kuɗi da mahaifiyar ki ta hango ta zuga Iya akan ta zaɓe ki dai za ki samu amma idan ki ka ce sata za ki yi kamar yadda ma su tarbiyya irin ki ke yi to Wallahi ba za ki ji da daɗi ba a gidan nan" yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin ya bar Hannatu tana rusa kuka. Yau wa gari ya waya ta biyewa daɗin lokaci kaɗan ta ba da mutuncinta tun a waje.

Hannatu dai 'ya ce ga Sama'ila wanda ya kasance Yayan Iya amma uwar su ba ɗaya ba. Lokacin da Iya ta fara nemawa Muntari Mata Rabi'atu ta nema ma sa wanda ita kuma 'yar ƙanin ta ne, tana da hankali ga ilimi dan har tana gab da ƙarisa secondary school ɗin ta kuma a makarantar ana ji da ita sosai saboda ƙwazonta.
Da ta yiwa Muntari magana sai ya ce baya son ta. Shi baya son Ustaziya da za ta zo gidan sa ta rinƙa takura ma sa da Allah Annabi. Hannatu kuwa da ta ma sa tayinta sai ya sa aka ma sa bincikenta. Abu ne na kuɗi shiyasa duk wani dark secret ɗin ta sai da aka faɗa ma sa.
Akwai wani Malamin su Salisu mutumin Jos ne, ya zo bautar ƙasa su ka ƙulla soyayya da Hannatu har ta kai ya rinjayeta, ta kan saci jiki ta je gidan sa su nunawa juna soyayya, a tunanin su fa. Alƙawarin aure ya mata amma daga ƙarisa bautar ƙasa sa da ya tafi bai ƙara waiwayanta ba, ya ci banza.
Bayan ta ƙare secondary school aka saka bikinta da Nura wani ɗan uwanta sai aka fara ƙananun gulmace-gulmace akan ta, hakan ya sa mahaifiyar Nuran ta ce a fasa auren. To da Iya ta zo Ringim ta fara batun haɗa Muntari da Rabi'atu ne shine Umman Hanne ta shiga zancen tana son a haɗa Muntari da 'yar ta. To da ya ce ba zai auri Rabi'atu ba shine aka yi maganar Hanne kuma ya amince da auren ta...
Chapter 36 · 0% Book details