Sashe 57
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda aka fara shari'a kuwa 'yan uwan T J su ka kasu kashi biyu rabi na wadai da abinda Maryam ta yi sauran kuma na cewa Allah shi kyauta halin Muntari ne ya kaishi haka tunda shi mutun ne mai hassada da riƙo.
Iya har kuka ta yi da jin yadda al'amarin Muntari ta kasance. Gidan na sa ya koma daga Hanne da 'yarta sai Iya da Humairah wanda duk zaman kaɗaici ya ishe su. Hanne kam a ranta kissimawa ta yi akan tana ƙarisa ajin ta na ƙarshe a Jami'a za ta je a raba aurenta da Muntari dan dama ta gaji da auren. Tun ranan da ta gane Maryam ya ke so ɗan sauran mutuncin da ta ke ganin sa da shi ya zube.
Abu da mutum da dukiya da kuma mutane da son zuciya. Ba a jima ba aka fara warwaso akan dukiyar Muntari. GM É—in sa tuni ya wawure abinda ya wawure yai gaba abinsa. A shagunan sa ma abun ba kanta kowa jin an É—aure Muntari sai halin rashin amana ya fara bayyana aka shiga yin satan kaya a hankali a hankali.
Cikin 'yan uwan sa kuwa Rabi'u wanda su ke 'ya'yan Baffanu kuma sa'anni saboda tsakanin su ma sati É—aya ne shi ya zo ya tsaya tsayin daka akan kasuwancin Muntari, dama shi ya ke kula ma sa da shi lokacin da ya ke Lagos to da Muntari ya dawo Zaria shine ya sallameshi bayan ya ba shi enough kuÉ—i da zai fara na shi kasuwanci, shima ya zama ya koma yana zaman kan sa. Ya samu buÉ—i kam da farko amma da ya sa neman mata a gaba sai kasuwancin sa ya zama ba albarka a ciki tunda yadda ya ke kashewa matan banza a waje ko rabin sa ba ya yiwa Iyalin sa biyu da ya ajiye a gida, a haka dai business É—in sa ya ja baya drastically.
Yanzu kuma da ya zama in control na dukiyar Muntari sai liyafa ta ci gaba. Saboda kar a sa ma sa ido sai ya jawo wasu cikin 'yan uwan su ya kawo su kasuwan dan kar ace shikaÉ—ai ya cinye komai. Iya da Hanne kuwa ba abinda su ka rasa tunda duk wata yana ba su kuÉ—i duk da kuwa Hanne ta san abinda ya ke ba su ko kusa bai kai wanda Muntari ke ba su ba amma ta yi shiru dan kar ace itama ta kawo fitina cikin 'yan uwa...
***
*7 years back*
Normal shiga na fita office ta yi na riga da wando na suit sai dai banbancin ta da sauran matan da ke wajen ɗanƙwali da sa ta yane kan ta da shi wanda ke nuna ita ɗin musulma ce. A yau za ta gabatar da wani pitch a gaban manyan kamfanin na su duba da yadda aka promoting ɗin ta wata huɗu kacal da fara aikinta a kamfanin. Bilhaƙƙi ta ke yin aikinta saboda abu ne da ta ke so.
Daga fara bayani ya katse ta tareda faÉ—in ta cire tsumman da ke kan ta dan she looked unprofessional.
Alinah ta yi murmushi ta ce "ba zan iya cirewa ba saboda da ni da abun da ke kaina duk É—aya mu ke"
Kalmar da ya faɗa a gaba ne ya sa ta ajiye highlighter da ke hannun ta ta fice daga hall ɗin. Tunda ta fara aiki yau ne su ka yi gaba da gaba da shi dan a da matsayinta bai ma kai ta yi magana da shi directly ba. Shine mai kamfanin kuma shi ya ce ta fita a hall ɗin dan kawai ta rufe kan ta. Ever since 9/11 da aka kai hari a twin tower na ƙasar musulmai su ke cikin zargi, wannan zargin ne ma ya sa aka dakatar da ita daga aikin da ta ke yi na shekara biyu a kamfanin da ta fara aiki.
Kamfanin Zuhayr ma da ƙyar ta samu aiki saboda ranan da ta je interview ma ta rufe kan ta wanda ya sa aka yi kokonton ba ta aikin, har ta cire rai ma da su aka kirata akan ta zo an ba ta aiki. Watanni huɗu da ta yi da su sun sha samun saɓani da colleages ɗinta simply because ita musulma ce kuma anyiwa Musulmai shaidar su 'yan ta'adda ne. Mutane da dama wannan yanayi ya sa su ka dinga ajiye musuluncin su a gida idan za su fita ba sa yin shiga da zai nuna su ɗin musulmai ne. Wasu da dama a wannan lokaci na takura ne ya sa su ka samu raunin imani har ta kai wasu sun yarda addinin su saboda tsoro da fargaba.
Itakam tarbiyyan da Babanta ya ɗaura ta akai ba zai taɓa bari ta chanja ra'ayinta saboda barazanar wasu ba.
"Alinah Jones" aka kira sunan ta. Ta É—ago tana kallon Aimee wacce ita ce shugabar sashen su a kamfanin.
"Mr Zuhayr wants to see you"
Bayan ta wuce Linda da ke gefen cubicle É—in ta tace " i hope he doesnt get you fired Alinah"
Alinah ta yi murmushi ta ce ma ta ba abinda zai faru.
Bayan ta shiga office ɗin Zuhayr ya ce ma ta zaɓi biyu take da shi a kamfani, ko dai ta dena rufe kan ta ko kuma ta ajiye aiki dan ba zai juri asara a kamfanin sa ba duba da yadda kamfanin ya samu koma baya saboda shi musulmi ne.
Ba ta ma sa magana ba ta koma office É—in su ta typing resignation later ta printing ta kawo ma sa.
Bayan ta ajiye takardar a gaban sa ta ce "Allah ya rabani da ranan da zan jingine addini na saboda son duniya. Ban zo garin nan dan mutane su so ni ba soyayyar Allah na ke nema ba ta wasu tsirarun gafalallun mutane ba. Ka sani Mr Zuhayr, kafin 9/11 akwai ƙasashe da dama da su ke cikin tashin hankali na yau da kullum, kuma a hakan ba su muzgunawa fararen fata mabiya addinin da ba na su ba da ke zaune cikin ta. Ni na san waye ɗan America na ƙwarai tunda na ga halacci a wajen su amma kai da duk wanda ya ke kiran duk wani musulmi da ɗan ta'adda ba ku da banbanci da dabbobi" daga haka ta fice a office ɗin sa.
Maganar ta ya sosa shi sosai amma girman kai ya hana shi ya kirata.
Bayan kwana shabiyu da barinta aiki watarana tana dawowa daga kasuwa da yamma tana riƙe da lema tana tafiya hannun ta riƙe da ledar da ta yi siyayya, ruwa ake yi amma ya tsagaita a lokacin dan ya koma yayyafi.
Da ƙarfi aka bugeta ta baya wanda sai da ta faɗi ƙasa lema da ledar hannun ta su ka yi gefe. Maza biyu ne irin 'yan jagaliya ɗin nan, jikin su duk ya ɓaci da tattoos.
"Kina É—auke da Bomb ne? Ina za ku saka wannan karan"
Ɗayan ya riƙeta da ƙarfi ya fara ƙoƙarin cire ɗankwalinta itama kuma ta riƙe shi gam amma dole sai da ya fincike ɗankwalin da ƙarfi ya haɗa da falla ma ta mari. Kuɗin da ke cikin purse ɗin ta daya faɗi ɗaya mutumin ya ciro ya coge a Aljihu.
"Hey Hey " aka faɗa da ƙarfi wanda ya sa su ka falle da gudu bayan sun ɗaga ido sun hango shi yana tahowa wajen da gudu, baƙaƙen kayan da ke jikin sa ya sa su ka ɗauka cewa ko shi ɗin FBI agent ne.
Wannan cin zarafi da ake yiwa musulmai ya zama ma ta jiki duk da kuwa yau ne aka ma ta wanda ya taɓata sosai tunda har ɗankwalinta aka cire ta ƙarfi a bakin titi.
Bai san wacece ba sai da ya iso ya sa hannu ya tallafa ma ta ta miƙe tsaye. Ya fito daga wani building ne ya hango marin da aka yiwa matar shiyasa ya taho da sauri, yana mugun daraja mata saboda soyayyar da ya ke wa mahaifiyar sa.
Kallon kallo su ka tsayayi na ɗan wasu daƙiƙu kafin daga baya ta je ta ɗauko scarf ɗin ta da ke yashe cikin ruwa a gefe, ta matse ruwan jiki sannan ta yane kan ta da shi. Duk abinda ta ke yi Zuhayr na tsaye yana kallon ta cike da tausayi.
Haka ta bi ta tsince kayanta da suka watse wanda wasu ma ba ta gan su ba. Lemar kam banƙarewa ta yi dan ko za ta yi amfani to sai an gyarata.
"Ki zo na kai ki gida" ya furta da ɗan ƙarfi lokacin da ya ga ta juya za ta tafi.
Ba ta saurareshi ba ta cigaba da tafiya dan haka ya zo ya sha gabanta ya sake maimaita abinda ya faÉ—a. Sai ta yi shiru tana kallon sa.
"Fisabilillah" ya furta a hankali wanda hakan ya sa ta amince ta bishi zuwa wajen da ya parking motar sa.
Kaman jira ake yi ta shiga motar dan tana shiga sai ga ruwa ya ƙara zuwa da ƙarfi shaaaaaaa...
Daga inda ta ke zaune yana ganin yadda ta ke maƙyarƙyatar sanyi dan haka ya cire jacket ɗin sa ya ba ta dan ta bayan ne kawai ya jiƙe kaɗan.
Daga wajen zuwa apartment É—in ta ba nisa dan tafiyar minti uku ta kai su wajen. Ta ma sa godiya ta fita a motar bayan ta tafi ya jima a wajen yana jimamin abinda ya faru tareda tausaya ma ta.