Sashe 150
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Galadima na fita bai zame ko ina ba sai gidan sa, wanka yai ya chanja kaya kafin ya fito ya ce Dreba ya kai shi gidan su Zaytoonah. Duk da dai gaisuwar ta sirikin sa ne amma yana fata ya sa matar sa a idon sa. Ba ƙaramin kewarta yai ba.
A ɓangaren Zaytoonah kuwa da su ka kai breakfast gida suna zazzaune a falo suna jiran Daddy ya fito aci abinci, kamar yadda aka ci tare jiya sai gashi ta buge da amai. Sabon turaren wuta da Mommy ta kunna ne ya sa ta wannan aman. Tun dawowanta gidan ma Mommy ta dena amfani da room freshner saboda damun Zaytoonah da ya ke yi.
Bayan aman da ta yi kuwa sai abincin da su ka yi ya fita ma ta a rai ta kasa cin komai sai zallar tea marar sugar da ta sha.
ÆŠakin Salman ta shiga ta kwanta dan wani sanyi ma ta ke ji. Daga inda ta ke tana jin hayaniyar su a falo har kusan minti talatin kafin bacci ya tafi da ita.
Bayan Auwal ya wuce office, Salman ya tura yaran waje. Humairah kuma ta shiga kitchen ta fara wanke-wanke.
Salman ya É—aga ido ya ce " Daddy, ya ce anjima kaÉ—an zai zo ya gaisheka"
"Allah ya kawoshi lafiya"
Mommy ta amsa da Amin jiki a sanyaye. Labarin da Salman ɗin ya ba su ne ya taɓa ta. Wani irin ƙaddara ke bibiyan Zaytoonah? Allah ya sa dai ƙarshen wahalarta kenan yanzu. Ba abinda za ta iya ma ta sai dai addu'a kawai. Allah ya cigaba da kareta daga sharrin Ghazala da sauran maƙiya.
Lokacin da Galadima ya fara juyawa Zaytoonah baya sai da ya kira Salman ya ma sa bayani a tsanake akan abinda ke faruwa. Sannan ya ce ma sa ya dinga kiranta kullum yana kwantar ma ta da hankali. Bai involving Mommy a maganar ba ne saboda ya san mata are too emotional, balle kuma UWA.
Kusan Azahar Galadima ya kira Salman ya faɗa ma sa cewa ya iso. Salman ya fita ya shigo da shi. Ba kowa a falo lokacin sai ƙaran TV da ke ta aiki.
Salman ya ƙarisa ɗakin Mommy ya mu su sallama.
"Daddy ya iso" ya furta sannan ya koma falon bayan Daddyn ya ce ma sa gashinan zuwa.
Yunwa ne ya tada Zaytoonah daga bacci dan haka da hamma ta fito falon tana faÉ—in "Mommy yunwa na..."
Ta yi saurin riƙe baki ganin Galadima a falon tareda Salman. Farar shadda ya saka tareda baƙar hular Zanna.
Sai da su ka haɗa ido kafin ta yi saurin yin baya da gudu. Tana shiga ɗaki ta dafe ƙirjinta saboda zuciyarta da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Da gaske dai sai da ya zo ɗin. But why will he come now? After all ya rabu da ni ai. Ta faɗa a ƙasan ran ta.
Da sauri ta shiga duba madubi. Ganin ba ta samu ba ya sa ta ɗau waya ta shiga camera ta fara kallon fiskarta. Fiskar ya kumbura, gefen idonta ya fitar da shatin bacci. Ɗanƙwalin da ta ɗaura yayi wani gefe da shi gashinta ya fito ta gefe-gefe yayi buzu-buzu. Rabon da gashin ma ya ga gyara tun tana Abuja.
"Innalillahi! Yanzu a haka ya ganni"...
Bayan minti biyar Daddy ya fito falon da sallama. Tunda ya fito da Galadima ya É—aga ido ya kalleshi ya kasa sauke idon sa. Tambayoyi da dama ne su ka bayyana a fiskarsa.
Daddy ya ƙarisa ya miƙa ma sa hannu tareda faɗin "Allah ya taimaki Alƙali" haka ya ke faɗa ma sa a mafi yawan lokuta idan ya buɗewa Galadima gate zai fita lokacin yana gadi a gidan sa.
Har Daddy ya zauna opposite da shi bai iya cewa komai ba.
Salman da ya lura da shock É—in da ke fiskar sa ya ce "Ranka shi daÉ—e ga Daddyn mu nan. Allah ya dawo mana da shi lafiya"
Innalillahi ya furta a ƙasan ran sa. Sai yanzu sunan da abokinsa Alhaji Ishaq ya kira Malam Shehu ya dawo ma sa.
DR TIJJANI ABUBAKAR MODIBBO and he's beloved wife's name is ZAYTOONAH TIJJANI ABUBAKAR.
Ya Allah! Sai yanzu da ya ga Salman kusa da Daddy ya gano kamannin su. Lokacin da ya fara ganin Salman sai da ya yi tunani a ransa akan yana kama da wani da ya sani amma bai iya tunowa ko waye ba ne.
"Alhamdulillah! Gaskiya ba abunda za mu ce sai dai mu godewa Allah. Allah mai hikima. Barka da zuwa Doctor" ya faÉ—a lokacin da ya É—an nitsu.
Daddy yai murmushi ya ce "Alhamdulillah ala kulli halin"
Ba a jima ba Salman ya ba su waje, bayan ya kawo wa Galadiman ruwan sha.
Yana shiga ɗaki ya ga Zaytoonah kwance ta ƙudundunu da bargo.
"Big Sis ya jiki?"
"Munafuki, kwana É—aya Daddy yai amma har ka kira shi. Shima da ke ba shi da kunya ya wani É—auko jiki ya zo. Ko mi zai gayawa Daddy oho?"
"I'll pretend i didnt hear anything. Ina Alinah dan Baban ta na tambayarta?"
"Zai tambaya ai, tunda shi ya haifa min ita"
Salman ya riƙe baƙi yana faɗin "barin bar ɗakin nan kafin kunnena ya toshe"
Ƙugin yunwa da cikinta ya cigaba da yi ne ya sa ta kira Humairah akan ta kawo ma ta abinci.
"Ina gidan Iya fa, akwai abinci a kitchen ki shiga ki É—auka"
"Ki zo ki kawo min, ba zan iya zuwa kitchen ba"
"Why?"
"Daddyn Raziya na falo"
"Kayya Anty"
"Dan Allah ki yi sauri Airah"...
Kusan awa biyu Daddy da Galadima su ka yi zaune suna hira kafin daga baya su ka wuce masallaci dan gabatar da sallar Azahar, daga nan kuma ya wuce fada saboda Mai Martaba da ke neman sa.
Lokacin da Zaytoonah ta idar da sallah ta duba wayarta saboda tuntuni ya ke ta ringing. Ga mamakin ta sai ga missed calls É—in Galadima guda biyu da kuma text É—aya.
*sleeping beauty, when i saw you, all i ...*
"Anty Zaytoonah wai ki zo inji Daddy"
Muryan Humairah ya katseta.
Maida hankalinta ta yi kan wayar bayan ta cewa Humairah tana zuwa yanzu.
*sleeping beauty, when i saw you, all i wanted to do was to KISS those sexy lips of yours. Wishing you safe trip Qurratul Ayn*
Mi ya ke É—aukan kan sa ne wai. Zai faÉ—i abinda ya ke so a lokacin da ya ke so. Yanzu ai ba matar sa ba ne. But wait... ba dai Daddy ne ya ce ya maida ni gidan sa ba?. Gaskiya ba zan koma ba.
Ko 2 seconds bai kai ba sai ga shi ta sake maida kai tana karanta text ɗin. And as she reads it, tana jin taste ɗin bakin sa a na ta harda lashe bakin, jikin ta ya fara tsirfa saƙon sinadarin dophamine da ke triggaring pleasure a jikin Ɗan Adam.
A falo ta samu Daddy da Mommy da Humairah sai Alinah da aka kwantar akan kujera. Gefen Daddyn ta zauna ta ce gani.
" kin samu kin ci abinci kuwa?"
"Yes Daddy"
"Mijin ki ya faÉ—i impressive things a kan ki Adaeze. I'm proud of you"
"Daddy may be Mommy ba ta gaya ma ba" ta É—an yi shiru kafin ta ce " ni da Daddyn Raziya mun rabu, he divorced me"
" 'yar ta ka wani lokacin kan ta kaman na kifi ya ke, Allah "
"Mommy ni É—in?"
"Kar ki kulata, she's jealous of you ne Princess"
"Ka ji da shi dai"
"Kar ki damu, ni da kai na zan hukunta mi ki shi. For neglecting you, dole ya karɓi hukunci mai tsanani"
Mommy ta ce "ka cigaba da biyewa ƙarya gindi. Nan gaba kaɗan za ta baka mamaki idan ta tattara ta koma wajen sa"
"I'm not going back to him" Zaytoonah ta faɗa da ɗan ƙarfi.
Mommy da Humairah su ka sa dariya saboda yadda Zaytoonan ta yi da baki.
"Daddy ka ga Dariya su ke min"
"Ki bar su Princess, duk kishi su ke da ke sun ga Daddyn ki ya dawo"
Bayan ya gama rarrashinta tukunna ya gaya ma ta dalilin kiranta, dama gobe ya ke son zuwa Ringim kuma jikinta da ba daɗi ya ke tunanin ko za ta iya bin su ko za ta zauna a nan. Ai ko ƙarasa maganar bai yi ba ta ce ma sa za ta je.
Da yamma da Salman ya dawo ta matse shi sai da ya gaya ma ta duk abinda ke faruwa. Daddy da Mommyn duk ba wanda ya gaya ma ta komai, sun barta a baibai ta sake shiga ruÉ—u.
Jikinta yayi sanyi bayan Salman ya gaya ma ta abinda ya sani gameda Galadima na dalilin da ya sa ya dinga shareta.
Ta san Ghazala ba ta da mutunci but ba ta taɓa tunanin za ta iya neman yi ma ta asiri ba. For what? Akan namiji.
"Madam Galadima kin ji dai abinda ya faru, sauran bayanan kuma za ki ji a wajen mijin ki"
"Salman wai mi na tarewa mutane ne? Can't i be safe in my husband's house, can't i be happy in my husband's house?"
"Sis ki godewa Allah da asirin matar nan ya tonu. Lets say Allah ya ba ta nasara akan abinda ta shirya da shikenan yanzu sai dai a dinga wani maganan ba wannan ba. Ki ƙara godewa Allah gaskiya"
Bayan tafiyar Salman sai ta ka sa samun sukuni. Baƙi da su ka zo yiwa Mommy Barka ya sa ba ta je ta samu Mommyn a falo ba. She needs motherly care now, dan har yanzu ba ta girmi hakan ba.
Rayuwar aure akwai shi da ƙalubale da jarrabawa kala-kala daga Ubangiji. Ta gani a lokacin aurenta da Zuhayr gashi nan tana gani a gidan Galadima.
Gara ta rayu ba aure, da ta auri mutum ta muzguna ma sa da shi da iyalinsa.
Babu namijin da ya chanchanci ta saɓawa Allah saboda shi, babu abin duniyan da zai kaita gaban Boka ko Malamin tsubbu. Ba ta fata Allah ya jarrabeta da son zuciya da kwaɗayi, dan suna ɗaya daga cikin dalilan da ke sa mutane dayawa ke faɗawa halaka.