← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 161

Sashe 22

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bikin na matsowa T J na ƙara nunawa Maryam kulawa duk dan ta kwantar da hankalinta. Daurewa kawai ta ke yi tana nuna ma sa ba komai but deep down she's hurting. Wani lokaci idan baya nan haka za ta zauna ta sha kuka ta ƙoshi, daga baya ta sanyawa kanta salama. Yanzu ita musulmace dole ta karɓi hukuncin Allah daya halatta auren mata huɗu.

Haka ranakun su ka yi ta wucewa har aka ɗaura auren Tijjani da Hajara. Kusan shiyayi komai saboda Hajara da mahaifiyarta sun bari acewa ita ƙanwar sa ce dan haka ko ba aure haƙƙin sa ne ya siya ma ta kayan ɗaki. Bayan wannan sai da ya biya Alhaji Rabe kuɗin daya kashe wa Hajjon tunda ta ci kuɗinsa kuma ta ƙi auren sa.
Su gani su ke aikin koyarwa da ya ke yi wani kuɗi ya ke samu na azo a gani. Ba dan Noma da kiwo da ya riƙe ba da ba ƙaramin jin jiki zai yi ba. Shi duk kuɗin abinda aka ce ya kawo kawowa ya ke yi saboda a zauna lafiya. Shi lokacin auren Maryam ba abunda yai tunda komai su Baffah ne su ka ma sa.

Cikin É—akuna uku da su ke gidan shi ya bawa Hajjo É—aki É—aya aka zo aka mata jere.
Cikin kashi sittin na 'yan uwan sa sun yi na'am da auren da yai, hujjar su kuwa shine ita Maryam ƙabila ce gara ya haɗa da 'yar gida.
Sauran kuwa sun nuna ba a yiwa Maryam adalci ba tunda auren su kwata-kwata shekara uku ne kuma kowa ga shaida halin Maryam na da kyau...

Faɗin ƙazantar Hajjo ma ɓata lokaci ne. Abun daya fara sa ta fitawa T J a ka kenan. Ƙazantar jiki da muhalli duk ta haɗa shi, shi idan na muhalli ne ma da sauƙi amma jikinta ta kasa gyarawa. Daya dinga takura ma ta akan wanka kuwa sai ranan girkinta idan ta ji sallamar sa ya dawo daga office zakaga ta shige banɗaki da gudu ta yi wanka fuyaaa ta fito ba tareda ta cuɗa jikinta da kyau ba.
Kasancewar Hajjo ita ɗaya ce 'ya mace a wajen mahaifiyarta ya sa Inna Saratu ta sakaltata, kwata-kwata ba ta kwaɓarta, a haka sai ta sangarce. Ba ta iya girki ba balle gyara gida. Ba abinda ta sani a ƙauyen su sai dai ta yi kwaskwarima ta banka foda a fiska ta cikawa bakin nan janbaki ta fita gari tana yawon ƙawance.

Ranan da ta fara girki cikin su ba wanda ya iya cin abincin, wannan ya sa Maryam ta ce ma ta duk ranan girkinta kar ta yi girki da ita. Ta kuwa gayawa T J ba za ta iya cin abincin Hajjo ba tunda 'yar wannan shinkafa ta kasa dafata da kyau. Duk rashin wayewar su Goggo Maryam ba za ta taɓa cewa ba su iya girki ba, tun lokacin da ta soma cin abincin gidan ba ta taɓa ganin aibun sa ba iyaka dai ba su yin varieties na vegetables kamar yadda Mommynta ke yi. Yadda su ke dafa Alayyaho ma ya banbanta da wanda ta sani. Ba ta cin miyan kuka amma idan Goggo ta yi miyan kuɓewa har suɗe hannu ta ke yi, dan za ta ji miyar ta ji citta, daddawa, masoro da sauran natural ingriedients ma su inganta abinci.

Shima dai T J ganin da gaske fa ba ta iya girki ba ne ya shi cewa ta tsaya Maryam ta koya ma ta girki . Ita kuwa ta kama ƙugu ta ce Allah ya sawwaƙa ta je ta koyi girki a wajen kishiyarta, kishiyar ma Inyamura. Ya kuwa daka ma ta tsawa ya ce lallai duk inda za ta je ta je ta koyi girki amma duk ranan da ta kuma kawo ma sa jagwalgwalon abinci sai ya zuba ma ta a ka sannan zai maida ta gidan su. Hakan ya sa ta ɗan tsorata da shi.
Wata maƙociyarsu ta samu ta nuna ma ta yadda ake girki na ɗan kwana biyu. Itama dai sammakal ne dan girki ne da aka yi amanna da kafi zabuwa.
Maganar saka Kafi zabuwa ko Ajinomoto a abinci kuwa tun yana maganar har ya dena dan Hajjo ta kasa denawa ta dai rage gambaÉ—awa, ita kamar yadda Maman Bilkisu ta koya mata haka ta É—auka, wai girki a Ajino baya daÉ—i.
Shikam duk ranan girkin Hajjo baya ƙoshi dan baya cin abinci sosai saboda ba jin daɗin abincin ya ke ba yana dai haƙuri ne. Yana gama ci yake brush saboda zaƙi-zaƙin Ajinon da ke tsaya ma sa a harshe. Wani lokaci ko yayi brush ɗin sai ya haɗa da asuwaki.

Gyaran gida kam Maryam ke yi ko ba ranan girkinta ba ne dan idan ta ce ba za ta gyara falo da kitchen da sauran wajajen ba sai dai cikin kwana biyun da T J zai yi a wajenta idan sun yi baƙi su ji kunya saboda Hajjo ba sharewa za ta yi ba. Ɗakinta ma sai ta yi sati bai ga tsintsiya ba, idan ka ga ta yi shara T J ne ya tsaya akanta ya ce dole sai ta share ɗakin. Ba abunda ta sani sai dai ta kunna T V da ke falo tayita kallon Films ɗin Indiya, tana yawon neman sabon casette daya fito.

A ƙoƙarin sa na son ganin Hajjo ta gyaru yai tunanin sa ta makaranta. Kasancewar ko Primary ba ta ƙarisa ba ta bar zuwa ya sa ya sama ma ta primary school aji huɗu. Ko yanene ta yi shekara biyu ta ƙare primary sai ta fara JSS one. Sai daya gama shirin sa har Uniform ya ɗinka ma ta Hajjo ta ce ba za ta yi makaranta ba. Ƙarshe ta ce irin makarantar da Maryam ke zuwa zai sa ta idan yana so ta yi karatu. Makarantar manya ba ta yara irin su Bilkisun maƙotan su ba.
Duk wani bayani yayi ma ta ta ƙi ji, ƙarshe ta ce wai ai ba dole ba ne tayi karatu. Da ya ma ta jan ido sai ta nitsu.
Kullum za ta shirya ta sa uniform ta wuce gidan Maman Bilkisu ta zauna su yi ta kallo sai da rana idan anfara dawowa daga makaranta sai ta koma gida.
Kusan sati uku ana haka T J bai taɓa ganewa ba, sai da watarana headmaster ɗin makarantar ya samu T J akan matarsa da ya ce za ta fara zuwa har yanzu form master ɗin ajin su ya ce bai ganta ba. Kunya ta sa T J ya rasa mi zai ce.
Da ya je gida ya tsare Hajjo kuwa sai ta sa kuka wai ita ba za ta yi makarantar yara ba. Haushi ya kamashi ya ce ta cigaba da zama a jahilci tunda Ilimin ne ba ta so, watarana za ta yi kuka da kan ta.
Daga ranan batun makarantar ta ya bi ruwa. Ba abinda ta ke yi sai kallo da yawon gulmace-gulmace. Da farkon kawo ta Amarya wasu cikin maƙotan su Maryam Hausa/Fulani su ka fara ja baya da Maryam suna cusuwa jikin Hajjo tunda acewar su 'yar uwa ce ba kamar Maryam da ta ke ƙabila ba.
(Kamar Hausa/Fulanin ba Ƙabila ba ne)

Dama Maryam ta fi harka da Madam Mitchele wata baturiyar ƙasar Poland wacce itama lecturer ce sai kuma Mama Lucas wata Igala sai wata Bayarabiya Iya Korede. Ita Iya Korede gidan su baya layi ɗaya amma duk da haka su na zumunci dan itama mijinta ya barta ta fara karatu, duk da ba Course ɗaya su ke da Maryam ɗin ba amma su kan haɗu wani lokaci a cikin School.

Daga baya da Hajjo ta nuna halinta na haÉ—a guri sai su ka fara ja baya da ita. Yanzu Maman Bilkisu ce kaÉ—ai su ke É—asawa da ita itama halinsu ne ya zo É—aya.

Maryam kam duk wani shirmen Hajjo ba ta biye ma ta, ba ma ta da lokacinta karatun ta kaɗai ya isheta ga wanda su ke a gida da T J. Ganin ba ta samu fiska a wajen Maryam ba ne ya sa ta dena taƙalarta da tsokana.

Watarana T J na Office aka zo aka kirashi wai matar shi na Asibiti. Gaba ɗaya ya tsorata dan bai san wacce ba ce cikin matan na sa. Sai da ya je ya ga Hajjo. Faɗa su ka yi da Maman Bilkisu, garin faɗan ne Maman Bilkisu ta tureta cikinta ya bugu da centre table shine ta yi ɓari.
Haushi takaici duk ya cika T J wai matar sa ta rasa cikinsa garin kokawa. Bayan an sallamesu ya ɗauketa su ka dawo gida tsabar ɓacin rai bai san mi zai gaya ma ta ba. Ya hanata yawo amma ba ta ji. Daya fara magana sai ta fara kuka wai bai tausaya ma ta bayan ta rasa gudan jinin su, hakan ya sa shi yin shiru.
Bayan kwana biyu ya ce ta je gida ta huta, shi da kan sa ya kaita gidan su ya kuwa yiwa Goggo maganan duk halin Hajjon ya kuma ce dan Allah ta ma ta faɗa. Bayan tafiyar sa da Goggo ta kira Hajjo tana ma ta faɗa sai ta fashe da kuka wai sharri T J ya ma ta dan ya fi son Maryam a kanta. Wai Maryam ce ta tureta har ta bugu ta yi ɓari. Takaici ya kama Goggo dan ta yarda da maganan T J. Duk faɗan da ta ma ta yana shiga ta kunnen dama ne yana fita ta hagu.

Bayan sati ɗaya da T J ya zo ɗaukanta Iya ta sa shi a gaba da faɗa wai ya jawa Maryam kunne, dan ita ba ta haihuwa ba zai sa ta dinga kashewa Hajjo 'ya'ya ba. Ga ainihin abinda ya faru amma Hajjo ta juya zancen akan Maryam ce ta tureta ita kuma Iya ta yarda da hakan. Ba ta ma bashi dama ba balle yai ma ta bayanin gaskiya, haka dai ya ɗau Hajjo su ka tafi ran sa a ɓace.
Chapter 22 · 0% Book details