← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 161

Sashe 92

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon falon na sa ya tsaya yi yana yaba ƙwazon yarinyar dan gaskiya yadda falon ya banbata da tsarin sa na da kuma still yai kyau dole ya jinjina ma ta...

***

"Adaeze" Mommy ta kira sunan ta da sigar jan hankali. Zaytoonah ta tattaro duk wani nitsuwarta ta bawa Mommy tana sauraron ta.

Wani ƙaton brown envelope Mommy ta ɗauka wanda ke saman center table. Jaridar da ke cikin envelope ɗin Mommy ta miƙawa Zaytoonah ta ce "gashi ki karanta headline ɗin"

Zaytoonah ta karɓa ta karanta, sai da ta karanta headline na biyu ne ta ɗago ido ta kalli Mommy da sauri cike da mamaki.
*Udodiri for Senator*

Mommy ta ce "Yes Adaeze. Mutumin da ke jikin jaridar nan Augustus Udodiri Uzodinma shine ƙanin Baba na daya kashe min Iyaye. Na samu jaridar ne shekaru uku da su ka wuce lokacin da ake shirin zaɓe. Daga lokacin na fara bincike na kuma tabbatar shi ɗin ne dai Uncle ɗina. Ya nemi Senator bai samu ba kuma yana so ya sake nema a zaɓe mai zuwa amma kafin nan ina son shigar da shi ƙara. Ina so ya biya dukiyar iyayena daya cinye, ina so a hukuntashi bisa laifin kashe min iyaye da yai"

Fiskarta babu alamun wasa ta ce "Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar ina so ki zamo Lauya ta, ki jagorance ni a wannan ƙara"

"Mommy please, ban shirya ba. Yaushe ma na gama karatu, i will love to be your Lawyer amma ba zan iya ba. Ban taɓa jagorantar kowa ba balle babban case irin wannan"

"Umurni ne ba shawara ba Zaytoonah. Abu ne da na sawa raina tun lokacin da kika furta min cewa Law za ki karanta"

Wannan karan sai ta sassauta murya ta ce "idan kuma ban kai na saki yin abu ba shikenan a rufe zancen"...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 43

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Hajia Ghazala*

Washegari Zaytoonah ta zo da wuri dan ta ma riga Justice zuwa. Duk da ya ganta a office ɗin Secretary bai nemeta ba, sai da ta gaji da jiran kiran sa kafin da ta ga lokaci na ƙurewa ta shige office ɗin sa ko izinin Sakatare ba ta nema ba.

Wannan karan da ta gaishe shi maimakon yai shiru irin na jiya sai ya ce " nan gaba nafi buƙatar Sallama fiye da gaisuwa"

Kallon Sannu ya sheikh ta ma sa tana ayyana abubuwa a ran ta.

Sai da ta tsaya kusan minti biyu kafin ya É—ago a karo na farko ya kalleta. It has been long da ta haÉ—u da idanun da su ka ma ta kwarjini irin wannan kamar yadda na Mr Upright ya ma ta.
Ta yi saurin kauda idon ta daga na shi saboda wani tasirin da kallon ke yi a dukkan gaboɓin jikin ta.

"Ki je wajen Barrister Noah Samson, zai koya miki basics na abubuwan da ya kamata ki sani. Bayan sati biyu ki zo ki bani report na abinda ki ka koya"
Yana maganar ne yana danna Laptop.

Kamar ba za tayi magana ba sai kuma ta yi gyaran murya ta ce "Sir, wajen ka aka..."

"Yes" ya faÉ—a yana zuba ma ta ido.

Ka sa ƙarisa maganar ta yi lokacin da su ka haɗa ido. Ta yi shiru tana kallon ƙasa a hankali kuma ta furta "barin je na same shi"

Ba hakan ta yi niyyan faÉ—i ba. Wajen sa aka turata amma kuma zai turata wajen wani daban. Ita kwata-kwata ba ta son harka da Ustazai balle wannan mai uban girman kan.

Ta dai fita a office ɗin tana ƙunƙuni cikin ran ta.

Barrister Noah ma ba wani sake ma ta fiska yai ba dai shi tana ganin ba zai kai Justice a shekaru ba dan tana tunanin yana late thirties ɗin sa ne. A wajen ya haɗata da Barrister Ahmad wani shima sabon zuwa wanda daga baya ne da yai ta zuba ma ta surutu ta gane ashe Justice Uncle ɗin sa ne, mahaifiyar sa ƙanwar Justice ce. Da shi da itan duk a shekaran aka calling ɗin su to Bar, sai dai maimakon ita da ta yi Law School a Abuja shi Ahmad Law School da ke Lagos ya yi. Da ka ga Ahmad ka san irin Ajebo ɗin nan ne, a yadda ya faɗa ma ta shine ɗan fari a wajen Iyayen sa kuma shi kaɗai ne namiji, yanada ƙanne mata biyu.
Kafin su tashi ranan sai da ta san kusan tarihin Justice kaf a bakin Ahmad. Ashe ma ba tsoho ba ne kamar yadda da take ma sa kallon tsoho. Duk da haushin sa da take ji sai da ta jinjina ƙwazon sa na yadda ya riƙe muƙamai da dama har ya kawo wannan matsayi cikin ƙanƙanin lokaci...

Justice Yunus Muhammad Abbas shine na uku a jerin 'ya'ya Maza na Mai Martaba Sarkin Zazzau. A wajen Mahaifiyar sa su uku ne kacal ta haifa kafin Allah ya ma ta rasuwa. Yana da Yaya Zainab da su ke kira da Hajiya Abu sai É—aya yayar sa Fatima wacce ta rasu da jimawa tun ma Yunus bai wuce shekaru goma a duniya ba.
Gaba da bayan sa sarauta ne, domin Mahaifiyar sa ma 'ya ce ga LamiÉ—on Yola na lokacin, kuma yanzu haka Kawun sa shine Sarkin Yola na Yanzu.

Yayi samu yin karatu da wuri, dan lokacin da ya gama Law school shekarun sa ishirin da biyu. Yayi aiki a Public sector ne har aka ba shi muƙamin Judge of High court na Kaduna lokacin dududu yana 32yrs. Ya zo ya zama Chief Judge na Kaduna gaba ɗaya kafin daga baya aka bashi muƙamin Justice of the courts of Appeal na Sokoto. Yanzu kuma wata biyar da su ka wuce aka bashi matsayin Bench of Justice na Nigerian court of Appeal Abuja.

Matar sa ta rasu shekaru biyu da su ka wuce kuma Allah ya azurta su da 'ya'ya uku duka mata. Fatima wacce su ke kira da Raziya sai mai sunan mahaifiyar sa wato Aisha wacce su ke kira da Falaq sai autar sa Maryam da su ke kira da Suhailah. A rayuwa yanzu ba abunda ya ke so sama da 'ya'yan san nan. Ya ci ace tun rasuwan Maryam ya ƙara aure amma tsoron auro wacce ba za ta riƙe ma sa 'ya'ya tsakani da Allah ba ya ke yi.
An ma sa tayin mata dayawa amma idan ya auna sai ya ga kamar idan yai auren za a samu matsala. Yanzu haka ƙarƙashin takunkunin Hajia Abu ya ke wacce ta rantse idan bai yi aure ba zuwa ƙarshen wannan shekaran za ta yiwa Mai Martaba magana a aura ma sa duk Yarinyar da ta zaɓa. Ta taɓa ma sa maganar Hajia Ghazala tun shekaran farko da matar sa ta rasu amma ya basar da zancen yana ganin kamar ba zai iya auren ƙanwar matar sa ba. Balle kuma Hajia Ghazala da shekaru goma kenan yanzu da rabuwan ta da tsohon mijin ta, ba wannan ba ne matsalar ba, tun da ta fito ba ta sake wani auren ba sai ma ta fanjama harkan kasuwanci kawai, a ganin sa kamar Ghazala ba ta dace da 'ya'yan sa ba.

***

Cikin sati ɗaya da ta yi a wajen Barr. Noah sun je zaman kotu sau biyu ta ga yadda ake gabatar da ƙara da duk wasu procedures da ake bi da ta karanta a littafi ta ganshi ra'ayul ain. Ta san yadda ake yi a chan America tunda ta sha attending court hearing. Yanzu kuma ta ga banbacin chan da nan. Ƙarshen sati ne Barr. Noah ya ba su assignment ita da Ahmad akan ranan Monday za su zo su gabatar mi shi. Wani case ne da aka jima da rufewa ya ɗauko mu su file ɗin yai assigning kowa da abinda zai yi. Ita Zaytoonah za ta zama mai defending wanda ake ƙara kuma a zahiri shine marar gaskiya amma kuma ana so ta yi iya ƙoƙarinta ta kareshi da hujjoji gamsassu. Shi kuma Ahmad shine zai defending wanda ya kai ƙara kuma shine da gaskiya.

Gaba É—aya weekend É—in ta yi shi ne wajen rehearsing presentation da za ta yi ranan Monday. Ta shirya wa abin sosai har tana baiwa kan ta nasara.

Ranan Monday ƙarfe goma su ka fara presentation ɗin a gaban Barr. Noah, Barr. Idris da Barr. AbdulHakeem da wasu ma'aikata guda biyu da ba ta san matsayin su ba.

Barr. Noah ne ya ke zaune a matsayin Alƙali a wajen. Ahmad ne ya fara gabatar da point ɗin sa kafin Zaytoonah ta yi na ta. A hankali abin ke tafiya kafin kusan minti talatin da farawa Ahmad ya faɗi wani point mai zafi yana cillawa Zaytoonan tambayar. Kan Zaytoonah ya kulle. Ahmad ya sake nanata tambayar da ɗan tsawa kamar dai a kotun gaske su ke.

"I dont know, i dont know Ahmad, I dont know" ta faɗa kamar za ta yi kuka. Ɗaga ido da za ta yi sama sai ga idon ta cikin na Justice, ashe tuntuni yana tsaye yana kallon su bai ƙaraso ya zauna ba ne kawai.
Tana saukar da idonta sai ga hawaye ya zubo ma ta, ta yi saurin sa bayan hannu ta goge.

Barr. Noah ya ce ya ba da minti goma su je su huta za a cigaba idan an dawo ya kuma jaddada wa Zaytoonah akan ta controlling emotions É—in ta, ta kuma É—auki presentation É—in kamar da gaske É—in a kotu su ke kuma wani ta ke wakilta.

Bayan sun fita a hall ɗin Ahmad ya matso kusa da ita yana faɗin " are you Ok?" Saboda ya ga sadda ta ke ƙoƙarin goge hawaye.
"Hey Chill, ba fa a gaske mu ke ba"

"Ina zuwa" abinda ta faɗa kenan kafin ta fice daga hall ɗin. Kai tsaye jakar ta taje ta ɗauka ta fita daga building ɗin sai wajen Motar ta. Tuƙi ta ke yi tana hawaye, ikon Allah ne kawai ya kai ta gida.
Tana faɗawa gado ta rushe da kuka tana faɗin "Mommy ba zan iya ba, ki yi haƙuri ba zan iya ba"
Chapter 92 · 0% Book details