Sashe 156
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba abu ne mai wahala ba idan Hajia Abu ta sa shi ƙara aure nan gaba kaɗan idan har ba ta haifi namiji ba. Though He'll be clocking Fifty soon amma har yanzu mutum ne da idan yana son auren 'yan mata 'yan shashida, shatakwas zai samu. Babu wanda zai ga 49yrs ɗin sa. Abinda za a gani shine gidan da ya fito da kuma ko shi wanene.
"Ya rubuta miki magani ne?" Maganar sa ya katse ma ta tunani.
"Daddyn Raziya ya za ka ji idan nima na dinga haifa maka 'ya'ya Mata"
Shirun da yai ya sa ta yi tunanin ya ji haushin maganarta.
Yatsunta ya riƙe yana murzawa a hankali kafin ya ce " ban aure ki dan ki haifa min ɗa namiji ba Zaytoon. Allah Subhanahu wata'ala shi ke bada haihuwa, kuma ya riga ya faɗa mana cewa wasu zai azurtasu da haihuwan 'ya'ya mata zalla wasu kuma 'ya'ya maza zalla, wasu kuma zai haɗa mu su duka biyu sannan akwai waɗanda zai jarrabesu da rashin haihuwa.
"Ina godiya wa Allah da ya azurtani da 'ya'ya mata har huɗu, kuma ko da wannan da ke hanya ya zama mace ni mai ƙara godiya ne domin 'ya'ya mata ma ni'ima ne. Addu'a na shine Allah ya bani ikon ɗaura su akan tarbiyyan musulunci na kuma samu damar aurar da su cikin kwanciyar hankali.
"Zaytoon i want you to know that i'm proud of my daughters. Yadda ki ke ganin sun nan diamond su ke a wajena"
Kissing goshinta yai ya ce "kar ki sa wannan a ran ki, duk rabon da Allah ya bamu za mu karɓe shi hannu bibbiyu. Infact ko 'ya'ya mata goma ne ki haifo min ina son su"...
"Sayyadi"
"Sayyadi"
Shiru, yayi barci.
Dole yai barci cikin azumin nan duk baya samun yin baccin kirki. Daga ƙarfe biyu da rabi tayi idan ya tashi shi da bacci kuma sai dai da rana idan ya samu sarari musamman idan bai fita office ba ko kuma ya samu dawowa da wuri.
Manna ma sa kiss ta yi a lips É—in sa tareda furta "I love you Zannoon"
Tunda ta ga alama Likita bai gaya ma sa cewa 'yan biyu ta ke É—auke da shi ba itama ta rufe maganar har Allah ya sauke ta lafiya ya gan su da idon sa. A lokacin ta sani he'll be more happier...
***
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka ƙare Azumi lafiya. Wanda kwata-kwata Zaytoonah Azumi shahuɗu kawai ta iya yi.
Kwana biyu kafin sallah su ka koma Zaria.
Suna zuwa kuwa ta kira Humairah akan ta zo ta tayata aikin sallah.
Wannan karan ma hawan da Galadima yai harda 'yan biyu kuma kamar wancan karan wannan karan ma sun burge mutane, dayawa ma na É—aukan su a matsayin 'ya'yan cikin Galadima ne.
Unfortunately rana na ukun Sallah da Zaytoonah ta je gaisuwa Fada su ka yi ido huÉ—u da Ghazala.
Duk da Galadima ya tabbatar ma ta da cewa shi kam ba zai dawo da ita ba hakan bai sa ta cire rai ga komawa gidan ba. Tana ta sintiri tsakanin Zaria da Abuja wajen 'yan uwan sa ko za a samu mai taimaka ma ta amma shiru ka ke ji. Mai Martaba ce ma ta yai ta cigaba da addu'a idan akwai alkhairi a komawarta, ko ba daÉ—e ko ba jimawa Galadima zai maidata gidan sa.
Hajja kuwa ce ma ta tayi ta ɗauki ƙaddara kawai. Hajiya Abu da ta ke da faɗa aji a wajen Galadima ita kuma ta nuna ma ta fir ba za ta koma ba indai ta isa da Galadima.
"Maman 'yan biyu" Ghazala ta faɗa tana ƙarewa Zaytoonah kallo, idan har idon ta ya ba ta dai-dai to wannan hasken da ƙyallin da Zaytoonah ke yi na ciki ne.
"Hajiya anyi sallah lafiya"
"Lafiya, ya yara?"
"Suna lafiya tare ma mu ke da su amma sun tafi gaida Mai Martaba"
"Ayyah!" Ta faɗa yayinda wani abu mai tsini ya soki ƙirjin ta.
Yadda ƙirjinta ke wawal-wawal ba za ta iya zama waje ɗaya da Zaytoonah ba dan haka ta yiwa Hajja sallama ta fita, ko wajen sauran matan ba ta je ba ta wuce gida.
Hajiya Safara'u ta nemi su sake neman wani malamin da zai ma ta aiki mai ƙarfi akan Galadima amma Ghazala ta riga ta tsorata da lamarin Galadiman musamman bayan mummunan jinyar da ta afkawa Hajia Ajwa daga ranan da aka kawo Hajia Fatima gidan.
Ba ta je ta ganta ba amma gulma ya iso ma ta cewa wani irin wari da É—oyi ta ke yi, wanda dole ya sa aka maidata boys quarter ta bar main building É—in.
Daga majiya mai ƙarfi ma ta samu labarin cewa Turaki ya saketa, zaman da ta ke yi albarkacin 'ya'yanta ne maya sa ya amince ta zauna ma sa a gida.
Ba za ta sake komawa maganar boka ko malamin tsubbu ba. So ta ke ta samu Galadima cikin hayyacin sa.
Kwanaki ƙalilan ne ya rage ta gama idda kuma idan wannan damar ya wuceta da wuya Galadima ya sake ba da sadaki ya aureta. Miye zai yi da ita? Bayan idan auren ma zai yi sai dai ya auri budurwa ko matar da ba ta kaita shekaru ba.
***
Lokacin da su Mommy su ka dawo daga Umura ne aka faÉ—awa Humairah maganar aurenta da Auwal. Ga mamakin su sai ta ce ba za ta aure shi ba.
Mommy da ta ma ta maganar sai ta sake baki da mamaki. Humairan dai da ta sani da tuntuni ta jima da sanin cewa tana son auren Auwal. Yarinyar da akan ta ne ma ta zaɓi aurar da Zaytoonah wa Galadima akan Auwal.
"Ban gane ba za ki aure shi ba"
"Mommy ba ya sona, ni ba zan auri mutumin da baya sona ba. Inada mai sona kuma shi zan aura, idan na auri Hamma Auwal kamar dai auren jeka nayika zan yi"
"Ikon Allah! Shi Auwal É—in ne ya ce ba ya son ki?"
"Mommy ki yi haƙuri amma ki gayawa Daddy ba zan aure shi ba" tana faɗin haka ta miƙe ta shige ɗaki zuciyarta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Kamar wasa kuwa da Daddy ya tambayeta sai ta ce ma sa ba za ta auri Auwal ba. Yai-yai da ita ta ƙi, daga ƙarshe ta ce ko za ta aure shi za ta yi ne dan shi amma ba dan ra'ayinta ba.
Da farko Daddy ya shiga ruÉ—u da furucin 'yar ta sa amma daga baya kuma da yai wani tunani sai ya gane halin yaran zamani ne Humairan ke son yi ma sa. Tuni ya dannawa Zaytoonah kira.
Dama a É—oke ta ke dan tun shekaran jiya da su ka sauka a Zaria ta ke son zuwa amma Mai girma Galadima ya ce ta bari sai Jummu'a idan sun je weekend sai ta je ta gaishe su.
"Mutum da iyayen sa ana nuna ma sa iko" ta faÉ—a cikin fushi. Ko da dare da yai niyyar lallashi ba ta bashi dama ba dan har ga Allah ta ji haushin hanata zuwa da yai. Ina Abuja ina Zaria...
"Mi ki ka kitsawa Humairah ta ke yin bore yanzun"
"Daddy ni kuma?"
"Ke dai Adaeze"
Zaytoonah ta ƙyalƙyale da dariya.
Abunda aka rufe mu su ne ya fito fili lokacin da Humairan ta saurari hiran Salman da Auwal inda ya ke tsokalar sa da angon Humairah, a wajen Iya ta samu labarin Daddy da Uncle Muntari sun riga sun tsaida maganar auren su da Auwal. With so much excitement ta kira Zaytoonah ta sanar ma ta. Zaytoonah kuma ta shirya ma ta akan kar ta yadda ta bari Auwal ya sameta a bulus, ta fara ja ma sa aji tukunna har sai ya fitar da abinda ke cikin sa.
"Za ki faɗa ko sai na hau mota na kai ƙaran ki wa Galadima"
"Haba Daddy, nifa kawai dai so na ke Hamma Auwal ya gane cewa ƙanwata na da class"
"Hakan ma yayi kyau Antyn Humairah"
Zaytoonah ta sa dariya.
Bayan ya tambayi lafiyar yara sannan ya tambayeta ko akwai matsala ta ce ma sa babu. Wanda hakan ya sa ke sawa zuciyar sa salama.
Bayan Daddy ya ji komai daga bakin Zaytoonah shima sai ya faÉ—awa Mommy akan ai ba za ayiwa Humairah auren dole ba tunda ba ta son Auwal magana ta wargaje kenan.
"Barkindo you are joking right?"
"I'm serious Nkiru. Dan haka ki gayawa first son É—in ki ya nemi wata matar a gaba"
Maryam ta ƙurawa mijin ta ido tana son tabbatar da gaskiya ko kuma ƙaryan sa.
"Hajiya ya ki ka zuba min ido ne"
Murmushi ta yi ta ce " sai dai ka yiwa na waje amma ni kam na san kaya na. I know when he's lying and when he's saying the truth. Humairah da First son aure ba fashi"
"Wannan wannan Mata" T J ya faÉ—a yana nunata da yatsa.
Maryam ta tura É—ankwalinta gaba ta tsuke baki ta ce "ya akai Mijin Maryama"...
Text É—in da Humairah ta turawa Auwal ne ya sa shi shiga ruÉ—u. Bai sake rikicewa ba sai da ya kira Mommy ya gaya ma ta sai itama ta tabbatar ma sa ai maganar aure ma an janye dan batun da ake ma gobe Muntari zai maida ma sa sadakin sa.
"Mommy Humairan ne ta ce ba ta sona, ita ce ta ce ba za ta aureni ba?"
"Haka dai ta gaya min kuma ko da Daddyn ku ya tambayeta hakan ta faÉ—a ma sa"
Kasa cewa komai yai ya kashe wayar ran sa na ƙuna.
Yarinyar da bakinta ya furta ma sa kalmar so ba sau É—aya ba ba sau biyu ba wai ita ce ke cewa ba za ta aure shi ba yanzu.
Tashin hankali sosai Auwal ya shiga. Kwana ɗaya sai gashi zazzaɓi mai zafi ya kama shi. After loosing Zaytoonah the thought of loosing Humairah again is depressing.
Wasa-wasa sai gashi har da kwanciya a Asibiti a ranan ne kuma su Zaytoonah su ka iso Zaria.
Tareda Galadima su ka zo yai wa su Daddy barka da dawowa kafin ya wuce gida ya bar Zaytoonah da yaran cikin 'yan uwan ta.