← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 161

Sashe 6

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ki ji abinda na faɗa ba ne" ta faɗa da ƙarfi wanda yai sanadiyar da kofin hannun Nkiru ya suɓuce ya faɗi ƙasa.

"Please help me, ban san ko'ina ba a garin nan kuma ba ni da kuÉ—i. Ki bari..."

"Will you shut up! Irin ku ne mijina ke so, sweet sixteen. Ba zan yarda ba, ki tashi ki tafi kafin rai na ya ɓaci"

Nkiru ta fashe da kuka saboda ba ta san inda za ta je ba daga nan. Ina ta sani a Nigeria. Gidan su da ke Owerri ko sunan anguwan ba ta sani ba, balle ko ta sani ma ba halin zuwa dan Uncle Udodiri zai iya zuwa ya kamata a wajen.
Yadda matar ta harzuƙa ne ya sa Nkiru ta fice daga gidan da gudu tana gudu tana tunanin ko za ta dace da haɗuwa da Antony. Sai da ta yi nisa sosai da gidan ta haƙura da gudun ta soma tafiya...

Chochi shine mafita gareta za ta samu mutanen ƙwarai da za su taimaka ma ta a wajen. Tana tafiya tana baza ido ko za ta ga alaman church. Ba a jimaba kuwa ta hango wani madaidaicin church sai dai a kulle ya ke ta yi tsaki ta cigaba da tafiya. Sanyin December na shigarta amma ba ta damu da sanyin ba ta cigaba da tafiya a hankali tanayi tana zubda hawaye. Mafiya yawancin ma su wucewa kallon mahaukaciya su ke ma ta, pink pyjamas ne ajikinta mai gajeran hannu gashi ƙafarta ba takalmi. Slippers ɗin da Elizabeth ta ba ta ya tsinke lokacin da su ke tahowa garin Obowo a ƙafa, yanayin tafiyarta kaɗai ya isa ya gamsar da mutum cewa ba ƙalau ta ke ba.

Yadda ta hango wasu treloli da bus bus a ɗan nesa da ita ya sa ta ɗan tsaya. A ranta ta ke tunanin ƙila za ta iya samun motan Calabar a nan, sai dai matsalar ba ta da kuɗin mota amma ba ri ta gwada roƙon su ko za su taimaka ma ta. Ta shafa cikinta da ke ta ƙugi yana neman abinci, rabon da ta ci abinci tun shayin da ta sha daren da aka kashe iyayenta. Sakwara da miyar egusi aka kawo mu su daren ranan wanda ya ji naman Akuya nasha-nasha sai dai ita ba ta cin naman Akuya kuma ba ta son cin abinci mai nauyi da dare, shiyasa kawai ta haɗawa kan ta tea ta sha yayinda iyayen ta su ka ci sakwaran, ashe da rabon za ta rayu ne shiyasa ba ta ci ba...

"Kai É—an Fillo akwai ka da abin dariya"
Ɗaya daga cikin ma su lodin jarkunan manja cikin trailer ya faɗa yana kallon T J da ke cigaba da ba su labarin yadda aka kusa kasheshi a wani ƙauye.

"Ka san na sadaƙar da rai na, ina ta tunanin ina ma albarkacin sunan Shehu Tijjani da na ci nima Allah zai ba ni karama kawai na ɓace na ganni a gaban Baffa na. Amma inaaa, ita mutumin sai wuwulwuwul ta ke da wuƙa tana faɗin Osibatata osibututu osiburebure..."

Gaba ɗaya 'yan wajen su ka fara dariya, wani da ya ɗau jarka sai ga shi da jarkan a ƙasa ya riƙe ciki yana dariya.
T J ya dage yana maimaita mu su siddabarun da mutumin ke faɗi yana cikin haka ya ji an dafa ƙafaɗar sa.
Ya juyo a hankali yana dariya, buÉ—e baki yai yana kallon wacce ta dafa shi, ya É—an rufe ido ya buÉ—e ko dai yarinyar ce ta ke ma sa gizo.

"Please help me, i'm going to Calabar but i dont have money". Nkiru ta faɗa kamar za ta yi kuka. Tunda ta shigo wajen ta ke rarraba ido tana neman wanda za ta yiwa magana, yadda ake kallonta ya sa jikinta yai sanyi tana tunanin anya akwai wanda zai taimaka ma ta, ganin wani saurayi sanye da kayan NYSC ya sa ta tunkare shi, ko a Owerri ta ga ma su irin kayan watarana da su ka fita shaƙatawa inda Baban ta ya ma ta bayanin ko su waye ma su saka irin kayan.

"Please" ta sake maimaitawa ganin ya ƙi yin magana.
DaÉ—in muryanta tareda British accent É—in ta ya dawo da shi daga duniyar tunani da ya tafi na 'yan sakanni.

"Sorry, you said Kalaba?"

Ta gyaÉ—a ma sa kai

Ya kalli É—aya daga cikin ma su lodin manja ya tambayeshi ko ana samun motar Calabar a wajen, mutumin ya ce ma sa sai dai ta je General Park.
T J ya juyo ya gaya ma ta da turanci.
Yadda ta sauke ajiyar zuciya ya sa T J ya san ba lafiya ba. ÆŠago idon da za ta yi sai ya ga hawaye a idonta mamaki ya kamashi.
So ta ke ta gaya ma sa ba ta da kuÉ—i kuma ba ta san inda General Park É—in ya ke ba amma ya ma ta kwarjini ba ta sani ba ko kallon mahaukaciya zai ma ta. Ta juya a hankali ba tare da ta ce ma sa komai ba ta fara tafiya, wannan karan church za ta je ko da a rufe ya ke za ta zauna a bakin church É—in, ba ta da mafaka da ya wuce House of the Lord, ko da mutuwa za ta yi gara ta mutu a church.

"Hey wait" muryan T J ya tsaidata. Ta dai tsaya amma ba ta juyo ba.

Tambayarta yai ko ita ce ta yi rawa a wani festival da aka yi a ƙauye kwana uku da su ka wuce. Ta gyaɗa ma sa kai.

"What happened to you?"

Hajijiya ta fara ji dan haka ta tsugunna tana dafa kanta.

"Are you Ok?" Ya tambaya cike da damuwa. Kallon ƙafarta yai ya ga ashe ko takalmi babu ga ƙafar har ya faffashe.

"This is serious. Where are your parents? Why are you like this?"

Ba ta iya ba shi amsa ba sai hawaye.

"ÆŠan Fillo yarinyar nan fa yunwa ta ke ji, tana cin abinci za ta warware" wani a wajen ya faÉ—i.

Wani kuma ya ce " Ku ga idon É—an Fillo dan Allah, ya ga yarinya 'yar dumaduma ya ruÉ—e"
Aka kwashe da dariya
Wani kuma ya ce "ÆŠan Fillo da rabon dai yau za a yanke ma ka wuya"

Nan su ka hau maimaita Osibatata Osibututu su na dariya.

Taimaka ma ta yai ta miƙe tsaye sannan ya ce ta biyo shi. Wajen mai shayin da ke tashar su ka je, duk garin shi kaɗai ke sana'ar shayi, da farko Hausawa 'yan uwan sa kaɗai ke siya daga baya kuma ya fara samun ɗaiɗaikun mutane da ba hausawa ba wanda su ke aiki a tashar su ma suna siya.

"Malam Idi zubo min shayi dan Allah"
Malam Idi ya ce "to Shehi" Da ke ya saba da 'yan tashar , su na haɗuwa wajen Sallah, sannan duk wata ya kan zo tashan ya ba da saƙo a kai ma sa Kano daga nan har garin su.

Yadda ya ke haɗa ma sa shayi ya ji sugar sosai haka ya haɗo ya miƙa ma sa. T J ya karɓa ya miƙawa Nkiru da ke zaune a kan benchi. Ta amshi kofin shayin ta kai baki, yadda hannunta ke rawa ya sa T J ya ƙara jin tausayinta tabbas akwai yunwa a tattare da ita.
Ko zaƙin tea ɗin ba ta damu da shi ba haka ta fara kurɓan tea ɗin nan ba kakkautawa, kafin ka ce me ta shanye shi tas. Ta miƙa wa T J kofin tana faɗin "Thank you"

Ya miƙawa Malam Idi kofin ya karɓi wani shayin tareda bredi ya miƙa ma ta. Ta wafce bredin da sauri ta fara ci da sauri-sauri. Saboda yadda ta cika bakinta da bredi da ƙyar ta ke taunawa. Ganin haka ya sa T J da ke kallon ikon Allah ya miƙa ma ta kofin shayi ta kuwa amsa ta kurɓa, hakan ya sa bredin da ke bakinta yai laushi har ta samu ta haɗiyeshi haka ta cigaba da ci har ta cinye.

Shi ma mai shayin ya lura da yadda Nkiru ke cin bredin ya san ba ƙaramin yunwa ta ke ji ba.

"Shehi ko za ka ƙarɓo ma ta shinkafa a wajen Maman Chukwudi"

T J ya amsa da to. Ya kalli Nkiru ya ce "wait here, i'm coming"

Da sauri sauri T J ya wuce shagon Mama Chukwudi da ke sai da abinci a tashar ya karɓo shinkafa da wake da miya har tiriri ta ke saboda ba a jima ma da sauke ta ba, haka ya karɓo yana sauri kamar zai tashi sama. Har a lokacin zuciyarsa na son sanin mi ya samu yarinyar nan cikin 'yan kwanaki uku kacal ta lalace haka.

Wannan karan rabin shinkafar Nkiru ta ci ta tura gefe ta ce ta ƙoshi.

Ganin ta fara dawowa hayyacinta ya sa T J ya tambayeta sunan ta.

"Nkiruka-Mary"

"Kiruka?"

Nkiru ta girgiza kai ta sake maimaitawa, wannan karan tana stressing N É—in
"NNNkiruka or Nkiru"

T J ya ce "Inkiru"
Still ba dai dai ba ne amma ta bar shi haka.

Ganin ta na kallon sa ya sa shi cewa " My name is Tijjani but people call me T J"

Itama ta maimaita T J É—in da ba za ta iya kiran Tijjani ba.

Tambaya na gaba shine miya kawota nan sannan miyasa ta ke son zuwa Calabar.
Ba ta san miyasa ta ke jin za ta iya yarda da shi ba, its like there's something in his eyes that is telling her he's honest trust him. A taƙaice ta bashi labarin yadda aka kashe ma ta iyayenta da kuma yadda wata ƙanwar mahaifin ta ta taimaka ma ta ta gudu.
Ya tambayeta ko ta taɓa zuwa Calabar ta ce ma sa a'a. A zuciyar sa yana faɗin lallai akwai matsala.
"Kin san gidan ku na Owerri?" Nan ma ta amsa da a'a, kusan komai ya tambaya sai ta ce a'a.
Ya ce "tirƙashi ashe kai kifin rijiya ne"

" what?"

"I mean what are you going to do?"

"I dont know, i want to look for my maternal grandparents but i dont know how"

Kafin yai magana ya ji ana ƙwalla ma sa kira.
Chapter 6 · 0% Book details