← Book details Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 161

Sashe 32

Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Kuɗi ba su ne matsalata ba, indai zan samu biyan buƙata zan iya biyan ko nawa ne. Wannan ne karo na uku da za a min kwatancen waje na je amma ba na samun biyan buƙata"

"Ai ka sha kuruminka kawai Alhaji, aikin ka an riga an gama. Sai dai dole za a yiwa baƙaƙen Aljanu yanka saboda su ne kaɗai za su iya aikin nan. Za a yanka mu su Ɓaunan da be taɓa yiwa mace barbara ba, sannan za yanka Zakaran da yai wa Kaza 'yar kwana bakwai fyaɗe sannan..." yana maganar yana zazzare ido a dole shi malamin tsibbu mai magana da Aljanu.

"Ba sai ka je da nisa ba ka yi lissafi ka faɗi nawa zan baka kawai, ni buƙata na ta biya shine damuwata"

"Dubu talatin"

Muntari ya ciro bandir ɗin kuɗi daga aljihun rigan sa ya ajiye a gaban Malamin tsubbun ya ce " ga dubu hamsin nan. Idan har buƙata ta biya zan dawo na ƙara maka wani alkhairin"

Malamin tsubbun yai saurin ɗauke kuɗin yana faɗin "ai ya saketa ma an gama. Ai yadda za a ɗasa mu su ƙiyayyar junan su ko inuwa ɗaya ba za su iya zama ba"

Da wannan Muntari ya bar rumfar mutumin yai gaba.

Shikuwa Malamin tsibbun dama na bogi ne, yawo ya ke yi ƙauyuka-ƙauyuka ya damfari mutane idan ya samu 'yan kuɗin sa sai ya ƙara gaba ya je wani wajen ya kuma damfarar wasu shashashun.
Bayan tafiyar Muntari ya shiga harhaɗa 'yan komatson sa, zuwa yamma ya bar ƙauyen.

Shi kuwa Muntari ya tafi da zubin nan da kwanaki kaÉ—an Tijjani da Maryam za su rabu. Dan ya É—an yadda da bayanin Malam Nabakin kura da alama shi zai yi gaskiya ba kaman sauran 'yan tsubbun da su ka damfare shi a baya ba.

***
*Anorexia nervosa*

Anorexia: wannan kalma ana alaƙantata ne da wani yanayi da mutane ke tsintar kan su ciki musamman ma su ƙiba. Yanayin shine tsoron ƙiban su, wanda ba su da ƙiba kuma ba tsoron yin ƙiba. Ba anan matsalar ta ke ba, matsalar shine a duk lokacin da ka ke tsoron ƙiban da ka ke da shi ko kuma ka ke tsoron yin ƙiba za ka zama kana aiwatar da wasu daga cikin abubuwan nan ko kuma ka dinga jin wasu daga cikin abubuwan nan:

1-ko yaushe za ka dinga lura da yanayin jikin ka kana duba shin ka ƙara ƙiba ne ko yanene. Ko kuma dai ka rage ƙiba ne
2-za ka damu da ƙiban ka da kuma siffar ko kuma dirin ka musamman ma mata.
3-idan kana da ƙiba za ka dinga ji a ranka cewa sai ka zama siriri ne zaka yi daɗin ganuwa, sai ka zama siriri ne za ka zama accepted a idon mutane. Za ka alaƙanta ƙimar ka da kasancewar ka siriri, wato idan kanada ƙiba za ka dinga gani kamar kimar ka ya ragu.
4-za ka iya yin komai dan kawai ka rage ƙiba. Ko kuma za ka iya yin komai dan kar ka yi ƙiba (saboda kana gani kamar idan ka yi ƙiba shikenan ka kaɗe)
5-za ka dinga hana kan ka cin abinci, ka ɗauki azumin da ba lada sai wahala (wato ka dinga Azumi dan kawai kana so ka rage ƙiba). To the extend koyaushe ka gwammaci ka wuni da yunwa saboda ka sa a ranka idan kana ƙin cin abinci automatically za ka rage ƙiba.
Ko ka ga mutum ya hana kan sa cin daɗi, ya tsiri tsirface tsirfacen cin wasu abincin yana ƙin cin wasu simply because a dole yana son rage ƙiba by fire bu force.
6- idan mutum ma'abocin yin excercise ne (motsa jiki) to za ka ga zai dinga yi babu hutu babu kakkautawa. Za dinga yin excercise da ya fi karfinsa duk dan yana so ya rage ƙiba da wuri
7- idan mutum na fama da Anorexia za ka ga duk yadda ya kai ga rage ƙiba ba zai taɓa haƙura ba shi dai zai dinga ganin kaman baya rage komai. Hakanan za ka ga koyaushe yana cikin gwada nauyin sa.
8-ko ya ci abinci mai yawa sai ya tsiri ƙaƙarin amai akan dole sai ya amayar da abinda ya ci.
9-shine neme-nemen maganin rage ƙiba. Ko me aka ma sa tallah sai ya siya ya gwada ko zai dace ya rage ƙiba
10- kullum cikin jin haushin kan sa ya ke simply because Allah ya halicce shi mai ƙiba. Kullum aka yi comment akan ƙiban sa sai ya ji haushi har ya ji a zuciyar sa inama,inama. Inama inada jikin wane ko inama inada sirantaka irin ta wacce, etc.

*Matsalolin Anorexia:*

-Yana sa mutum ya kasa taɓuka komai sai ya zamana rayuwar sa ta ta'allaƙa ne kawai da son rage ƙiba ko tsoron yin ƙiba.
-Garin hana kan ka cin abinci ka ke ka rasa kuzari ƙarshe ka fara fama da malnutrition idan ya zo da ƙarar kwana mutum ya mutu.
-A neme-nemen maganin rage ƙiba ka je ka sha abunda zai kashe ka ko ka sha abunda zai jawo maka wata cuta ko wata matsala daban.
- Saboda damuwa da ka sa a ranka sai ka iya samun hawan jini.

*Yadda za ka yi yaƙi da Anorexia:*

- ka so kan ka a yadda ka ke. Kafin wani ya so ka sai ka fara son kan ka tukunna. Idan ke macece kamar ni, ki sa a ranki duk ƙibar ki akwai mazan da su haka Allah ya yi su mata ma su ƙiba su ke so ba sirara ba (dama number one problem ɗin shine kina tunanin maza sun fi son sirara shiyasa ƙibar ki zai dinga sa ki damuwa. Hell no baby girl. A yadda ki ke za ki samu masoyin ki na asali wanda shi mace irin ki ma ya fi so). And idan ya complain akan ƙiban ki ki ce ma sa 'go hug transformer'.

- ki dena yin gasa ko kishi da wata 'yar uwar ki ko ƙawar ki da ta ke siririya. Babban abunda ya ke ƙara propagating anorexia shi ne yadda Media ta ke nuna modela sirara, ko jaruma 'yar film za a zaɓa anfi son siririya. Ma su tallen shayin rage ƙiba ko maganin rage ƙiba sai su dinga potraying ma su ƙiba a matsayin ma su matsala amma sirara kuma su ne dai dai (akwai ƙiban cuta ko na rashin lafiya. Ina maganan ƙiba da ya ke naturally haka Allah yayiki ko yayika kuma ba ka da wani unhealthy habit da zai sa ƙiban na ka ya jawo maka wani illah). Ita ƙawarkin da ki ke burin ki zama kamarta may be itama akwai wani abu da ki ke da shi da ta ke bala'in burin ta same shi amma ke ba ki sani ba. The moment kika dena kishi da kuma gasa da sirara za ki ji zuciyar ki wasakai ba wani damuwa. You'll live happily.
-Babu magic powder ko magani da zai sa ki rage ƙiba cikin ƙanƙanin lokaci. Rage ƙiba is a gradual procesa, ba wai dan kin sha wani abu ko kin yi wani abu lokaci guda sai kawai bayan kwana biyu ki ga kin tashi siririya ba. Ba haka abun ya ke ba, rage ƙiba tafiya ce mai ɗaukan lokaci idan kin jure. Matuƙar za ki rage ƙiba ne dan wani ko dan wata kina ruwa. Domin indai dan wasu za ki rage ƙiba to ba ki da kwanciyar hankali, domin abu ɗaya za ki dinga hangowa shine kina son ki zama siririya dan ki burgesu. My Sister and My Brother ba za ka taɓa burge ɗan Adam ba, sai ki sha slimming tea ɗin ki sha haɗe-haɗen ki zama siririyan still a zage ki. A nuna ai yanzu da ki ka zama siriya ba ki yi kyau ba. Wa su su ce ma rashin godiyar Allah ya sa ki ka koma siririya ta ƙarfi.
Chapter 32 · 0% Book details