Sashe 131
Zaytoonah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko zama bai iya yi ba yana tsaye kawai ya goya hannunsa a baya.
"Ranka shi daÉ—e na ga ka dawo yanzu, lafiya?"
Juyowa yai a harzuƙe ya ce "Ghazala kan ki ɗaya kuwa?. Tabbas ya tabbata ke ce da ciwon hauka ba Zaytoon ba. Ina mai tabbatar mi ki da cewa idan har ki ka ba da bayani aka ɗaura a gidan jarida, TV ko radio hakan zai tafi da igiyar auren ki ne"
"Abu Razz!" Ta faÉ—a a kiÉ—ime.
"Wannan na ƙarshe kenan da wani abu zai faru a gidan nan da za ki kira wani nawa ki faɗawa ko kuma ki kai waje. Na ƙarshe kenan Ghazala"
Ficewa yai ya barta jikinta na ɓari, ta riga ta yi hira da wani ɗan jarida a waya ɗazu da safe kuma sun ce za su ɗaura labarin a labaran su na rana.
"Na shiga uku" ta furta tareda ficewa da gudu. Wayarta da ta bari a falon ƙasa ta ɗauko ta sake komawa sama, ƙawayenta na tambayarta ko lafiya amma ba ta kula su ba. Bayan ta kirashi Allah Annabi ta fara roƙonsa akan kar a ɗaura hiran ta su a radio. Ƙoƙarin fahimtar da ita ya ke akan ba komai ba ne tunda muryarta ne kuma ma za su iya ɓoye sunan ta.
"Dan Ubanka na ce ban yarda a ɗaura ba" ta faɗa a tsawace ganin zai jawo ma ta matsala ta kashe wayar ta nemi gyalenta da jaka ta fice daga ɗakin da sauri. Office ɗin su na nan Abuja za ta je ta dakatar da wannan katoɓarar da ta aikata. Ta san halin Galadima sarai ba ya empty threat. Duk abinda ta yi ta yi shi ne saboda ta samu gidan ita ɗaya, idan kuma aka ce Galadima ya rabu da ita ai anyi ba ayi ba kenan.
Galadima É—akin Zaytoonah ya shiga inda ya sameta tana bacci. Sajida kuma na kan kujera tana assignment.
"Ta jima da bacci ne?"
"A'a" Sajida ta amsa ma sa.
Ƙarisawa yai bakin gadon ya zauna. Ya ƙura ma ta ido yana kallon ta sai yanzu ya ga ba ƙaramin rama ta yi ba. Ba dole ta rame ba, ina ta ga kwanciyar hankali cikin kwanakin nan.
Addu'arsa ɗaya Allah ya sa shawaran da ya yanke ya ma sa amfani. Gida ya siya ake kan gyarawa yana so ya maidata chan idan an gama. Sajida ya ke so ta bar hostel ta dinga zama da ita yana fatan ya ɗauko wata cikin yaran ƙannen sa su haɗu su zama su biyu da za su dinga ɗebe ma ta kewa idan yana tareda Ghazala a nan. Ƙila idan aka chanja gida maganar Ben ɗin nan zai mutu.
A hankali ya manna ma ta kiss a goshi kafin ya miƙe ya fita.
Bai bi ta kan Ghazala ba ya koma office, da ya sauka bai ganta ba baƙinta ma sun tafi. Motar ta ma babu a waje hakan ya tabbatar ma sa da fita ta yi. Tabbas maganar da ya faɗa ba zai janye ba, matuƙar ta yadda ta sake labarin nan a 'yan Jarida ba abinda zai hanashi datse igiyar auren su. Ta fara fita ma sa a ka, tun asali ya san ita ɗin ba macen da ta dace da shi ba ne to amma duk da shi ba yaro ba ne ba zai yi wasa da maganar manya ba...
Bai dawo ba sai dare bayan sallar Isha, ɗakin Zaytoonah ya fara wucewa ya samu tana zaune a ƙasa kusa da gado 'yan biyunta na gefe suna cin abinci amma Zaytoonah ido kawai ta zubawa abincin ba ta ci.
Sallama ya sake yi a karo na biyu amma babu wanda ya amsa.
"Abincin ne ya hanaku gaishe da Daddy" ya faÉ—a yana shafa kan su.
"Sannu da zuwa Daddy"
" 'yan matana ya gari?" Ya faÉ—a yana sa hannu a goshinta.
"Kina jin zazzaɓi ne? Goshin ki da zafi"
Bakin gado ya zauna ya É—aura hannun sa kan kafaÉ—an ta.
"ÆŠazu da rana na zo kina bacci. Kin samu baccin sosai kuwa?"
"Mommy za ta zo gobe" ta faÉ—a a hankali
"Allah ya kawota lafiya" ya faÉ—a a sanyaye. Ba makawa dai ta ji abinda ya faru ne shiyasa za ta zo. Dan maganar tafiyar su ganin Likita sun barshi sai bayan sallar Azumi, yanzu kuma Azumin ma ana tunanin saura kwana tara ne ko goma.
"GrandMa ta ce tafiya za tayi da mu" Hashir ya katse ma sa tunani
"Gara ma mu tafi ai wannan Raziyan sai ta yi ta ce mana 'ya'yan mahaukaciya. Ni kam ta ƙara faɗa Allah ya isa"
Hadid ne da wannan maganar. Gashi dai yaro ne amma yadda yai maganar ka san ransa a ɓace ya ke sosai.
Sai yanzu Galadima ya gane dalilin da ya sa yaran su ka shareshi lokacin da ya shigo.
"Ai ba ita kaÉ—ai ta ke faÉ—a ba, Hajiyar nan ma haka ta gaya min É—azu da na je kitchen wajen Anty Sajida"
Take jikin Galadima yai sanyi jin maganganun yaran. Ya sani da Zaytoonah na nan da lafiyarta kamar da da za ta kwaɓe su amma yanzu shiru ta yi ba ta ce komai ba da alama ma hankalinta ba ya wajen su.
A ƙoƙarin sa na son janye hankalin su daga wannan maganar ya tambayesu ko Maman su ta ci abinci su ka ce ba ta ci ba, da ta ce za ta ci kaɗan amma da aka kawo ta ce ba za ta iya ci ba.
Ya maida tambayar sa ga Zaytoonah ya tambayeta mi za ta ci idan ba za ta iya cin wannan ba. Da farko shiru ta yi daga baya ta ce ma sa kunu da ƙosai.
"Kunu da ƙosai za ki ci?" Ya sake tambaya
GyaÉ—a ma sa kai ta yi ba tareda ta yi magana ba.
Wayar sa ya ɗauka ya kira numbar Sajida da ta ɗauka ya ce ma ta ta cewa Atika ta haɗawa Zaytoonah kunu da ƙosai yanzun nan.
Bai fi minti biyu ba sai ta kira shi inda ta tambayeshi wai wani irin kunu.
"Adaeze wani irin kunu za ki sha?"
"Kunun gyaÉ—a"...
Bayan ya bar ɗakin Zaytoonah ɗakin sa ya wuce inda yai wanka ya chanja kaya zuwa kayan bacci, yana fitowa Falo ya tadda Ghazala na zaman jiran sa. Ta sha ado sai ƙamshi ta ke.
"Ranka shi daÉ—e na zubo ma ka abinci yanzu ne?"
"Na ƙoshi"
"Abu..."
"Ki kiramin Raziya ku zo tare"
Bayan ta kira Raziya faɗa sosai yai wa Raziyan akan ko da wasa kar ta ƙara kiran Zaytoonah da Mahaukaciya balle har ta zagi 'yan biyu. Bayan ta bar wajen ne ya koma kan Ghazala. Faɗan da bai ma ta ɗazu da rana ba shi yai ma ta yanzu.
Idon Ghazala ya rena fata dan Galadima bai yi da wasa ba. Sharuɗɗan da ya kafa ma ta na zaman gidan sa za su kai goma. Haƙuri ta fara bashi lokacin da ya gama masifar amma bai kulata ba ya tashi ya fita.
Ɗakin Zaytoonah ya shiga ya ga har lokacin ba a kawo mata kunu da ƙosan ba.
Saukowa yai ƙasa ya ce Sajida da ke cin abinci a dinning ta duba ma sa me Atika ke yi ba ta gama abinda aka sata ba.
Bayan ta leƙa kitchen ɗin ne ta fito ta gaya ma sa an gama kunun yanzu za a fara soya ƙosan.
Ya ce ana gamawa ta ɗauka ta kai ɗakin Zaytoonah. Komawa yai sama dan ya je ya lallaɓi 'yan samarin tagwayen na sa...
**
Washegari da Mommy ta zo gidan ta ga Zaytoonah kamar ta yi kuka, ta lalace kamar ba ita ba, compared to ranan da ta zo Zaytoonan ta sake zabgewa.
Ba wannan ne kaɗai damuwarta ba sai yadda jiya aka yi ta damunta da kira ana son ƙarin bayani gameda labarin da ake gani na yawo a media na batun yanka Raziya da Zaytoonah ta yi. Tun a jiyan ta so zuwa sai dai hakan bai yiwu ba. Takanas ta je gidan Hajiya Ni'ima neman ƙarin bayani daga ina ne labarin ya ɓullo. Hajiya Ni'ima ta gaya ma ta Ghazala dai kishiyar Zaytoonah ne ta turo hoton da rubutun zuwa family group ɗin su daga nan kuma aka watsa shi waje.
Mommy ta sake baki tana kallon Hajiya Ni'ima da ke ba ta bayanin abinda ake ta faɗa a cikin Family ɗin su gameda Zaytoonah har da ma su cewa kawai Galadima ya rabu da ita tun kafin ta kashe ma sa 'ya'ya wannan ya tunzura Mommy matuƙa ta ɗau aniyar dole Galadima ya sake ma ta 'ya.
Da ke da safe su ka zo Galadima ya riga ya fita dan haka Mommy ta wuce office É—in sa yayinda ta bawa Humairah umurnin ta taya Zaytoonah tattara kaya.
Ko da ta samu Galadima da maganar saki ko kaÉ—an bai ji daÉ—in maganar ba. Mommy dai ta dage tafiya za ta yi da Zaytoonah. Galadima ya ce ya yarda dai da maganar tafiya ganin likita amma maganar saki ba zai yiwu ba, ba shi da dalilin da zai raba shi da Zaytoonah.
Lokacin da Mommy ta koma gidan ne ta taya Humairah su ka ƙarisa tattara kayan Zaytoonah harda na 'yanbiyu. Suma saboda makaranta za ta bar su a nan Abuja dan cikin Azumi za su yi jarrabawa. Gidan Muhsina ya kamata su zauna amma tunda ba ta nan gidan Yahya za ta kai su, shima wani cousin ɗin Zuhayr ne da ke zaune a nan Abujan, idan ya so sai a dinga kawosu weekend Zaria.
Ghazala ta zo fita shago ta ga dawowar Mommy ranta a ɓace dan haka ta fasa tafiyar ta zauna zaman gulma. Lokacin da ta ga Humairah ta fara saukowa da akwatuna ƙasa sai wani farin ciki ya mamayeta. Kayan da ta ga an sauko da su ba kayan tafiyar kwana ɗaya ko biyu ba ne kaya ne da za ta iya cewa kaman ma duka kayan Zaytoonan aka sauko da shi.
'Yan biyu su ka fita su ka kira Dreba ya zo ya jidi kayan ya kai cikin Mota.